Sashe 8
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hijabin sallarta ta ɗauka ta saka ta ɗauki ƴar purse ɗinta da take ajiyar kuɗi ta fice, kamar tayi wucewarta ba tare da ta sanarwa Mallam ɗin ba ganin irin tijarar da yayi mata a tsakar gida kamar Baqeer ɗin ne ya ɗorawa kanshi larurar sai dai kuma ba zata iya yin hakan ba don ba sabonta bane fita bada izininshi ba bare ma da yake cikin gidan a zaune ba wai baya nan ba. Daga bakin ƙofa taja ta tsaya ta ɗaga labulen ƙofar ɗakin tace mishi "zan tafi asibitin na zauna dashi tunda kai ka dawo". Da yake shima a ƙullace yake da ita ko musu bai yi mata ba sai ma ɗaga kanshi da yayi alamun amsawa, ganin hakan itama tasa kai tayi ficewarta zuciyarta cike da tausayin yaronta da mummunar ƙaddara irin wannan ta afko mishi da kuruciyarshi, tana tafe tana ɗauke hawaye da bakin hijabinta har ta samu adaidata sahu ta tara ta shige ba tare data tsaya sun yi dogon ciniki ba.
Lokacin data isa asibitin ta samu babu kowa a wajen shi sai shi kaɗai yana kwance yayi lamo abin duniya ya taru yayi mishi yawa, ya kasa gaskata wai shine ake cewa ba zai sake iya taka ƙafarshi ba, shikenan ana nufin ya zama nakasashe ya tashi daga mai lafiya ya zama gurgu. Yana kawowa nan a tunanin wasu hawaye masu tsananin zafi suka sulmiyo daga idanunshi, hannu tasa tana share mishi hawayen sai dai ita kuma ta kasa tsayar da zubar nata hawayen ganin tun ba ayi wata tafiya mai nisa ba mahaifin Baqeer ɗin daya kamata ace shine na farko wajen ƙarfafa mishi ya ƙarbi ƙaddarar data sameshi ya juya mishi baya. Abun nan yayi mata ciwo ba ɗan kaɗan ba. Sai da suka yi kukansu ya ishesu sannan ta tambayeshi ina Bashir yaje tunda tazo bata ganshi ba bayan kuma shi ne yake zaune a wurin shi yana jinyar shi.
"Tun bayan tafiyar Baba shima ya fita bai ce mini ga inda zai je ba" ya amsa mata da shaƙaƙƙiyar muryar data sha kuka ta ƙoshi. Zama tayi akan kujera daga gaban gadon ta riƙo hannunshi mai lafiyar tace "kayi haƙuri Baqeer, kowanne bawa da kake gani yana tafiya ne akan ɓigire na zanen ƙaddararshi, muhimmin abu a wajen mumini shine karɓar ƙaddarar a duk yanda tazo mishi, tunda kaga hakan ta faru da kai to haka nan Allah yake so ya ganka don haka nake horarka da yin haƙuri ka ƙarɓi ƙaddararka a yadda tazo maka In Sha Allah ba zaka taɓe ba. Allah yayi maka albarka ya tashi kafaɗunka.” Baqeer ji yayi ya kasa cewa Ameen a fili, jugum-jugum suka yi a ɗakin gaba ɗaya kowa da abinda yake sakawa a ranshi, wayar tace tayi kara da kamar ba zata duba ba sai kuma ta ɗauko taga ƙanwar Baqeer ce mai bi mishi ke kiran, tayi aure tun shekaru biyar da suka wuce, tana ganin itace ta kalli Baqeer wanda ya ɗan kalli wayar shima, nan da nan wani abu ya sake taso mishi, kanshi kawai ya sake kwantarwa, cike da tausayi ta kashe wayar tace “Ka tashi kaci abinci, na siyoma alale mutumin ka.” Kai ya girgiza a hankali alamar a’a kawai dan baya ji bakinshi ma zai iya tauna abinci.
Ta sani sarai ba zai iya cin abincin ba amma dole ne ta karfafa mishi gwiwa, wannan wacce irin muguwar kaddara ce ta samesu?
****
Duk yadda Habi take yiwa Asiya magana ta kasa tankata, cike da takaicin abinda take aikatawa Habi ta fizgota tace “Asiya menene hakan? Ya zamu zo asibiti dubiya amma ki gudu? Bayan kin san yana bukatar wanda zai lallasheshi a wannan lokacin?”
Fizge jikinta Asiya tayi tace “kinga Malama karki kuma tado mini maganar dubiya, hauka nake kina tunanin zan cigaba da soyayya da Baqeer? Ko baki ji me likita yace bane? Akan ba zai warke ba? Aure zanyi ko kula da gurgu?”
Baki Habi ta saki mamaki ya sake rufeta tace “Asiya kina nufin yanzu daga yin wannan abin shine har kwakwalwarki ta tafi lissafin haka? Kin manta wanene Baqeer a gareki? Ko kin manta karatunki ma ba dan shi ba da baki karasa ba? Sannan shekara nawa yayi yana kula dake da duk wasu bukatunki?”
“To saka shi nayi? Ko tilasta mishi nayi?” Ta faɗa tana cigaba da tafiyarta, gaba ɗaya Habi kasa motsawa tayi saboda mamaki, tana nan tsaye har Asiya ta shiga adaidaita ta ɗan ɗaga murya tace “Zaki zo mu tafi ko na tafi na barki?” Kasancewar tasan za’a mata faɗa a gida yasa ta ƙaraso ta shiga adaidaitar suka fara tafiya, sam Asiya bata ba ta fuskar magana ba hakan yasa ta yin shiru kawai suka cigaba da tafiya, suna sauƙa Habi tace “Lallai na yarda ɗan adam butulu ne, yanzu duk soyayyar da kike magana iya kacinta kenan?”
Tsaki tayi tace “Da nace miki bana son shi ne? Ko kinji na faɗi haka da bakina? Sai dai ni ba auren jinya zanyi ba, kinfi kowa sanin kaf gidan mu babu wanda ya kai ni kyau da diri mai tsari ga karatu na nayi daidai gwargwado, ta ya ina planning na future ɗina magana ta sauya zuwa raino? Bana ɗaukan lokaci akan ajiye duk wani abu da zai kawo mini cikas a rayuwata, ba zanyi aure irin na gidan mu ba da za’ace babu dan haka karki sake yi mini maganar Baqeer.” Tana kaiwa nan bata jira amsar Habi ba ta shiga ciki ranta a matukar ɓace.
Gaba ɗaya Habi mamaki ne ke sake rufeta yarinyar da a saninta ko wayar Baqeer ne bata ji ba hankalinta tashi yake yi?
Haka ta shiga gida jikinta duk a sanyaye, Inna ta gani zaune tana ɗaura tandar waina, da sauri ta ƙarasa ta gaisheta sannan ta cire mayafinta tana neman amsar aikin.
“Waya taɓa Yayarki naga ta shigo rai a ɓace."
“Shareta Inna kin san halinta ai ita wannan.” Habi ta faɗa tana neman zama.
“A wanke hannu kafin a fara.” Dariya tayi ta miƙe tsaye tana nufar wajen famfo don ta wanke hannun.
*******
Umma ce ta kalli agoggo ganin har azahar ta wuce ba Bashir gashi tun ɗazu Baqeer ke nemanshi ya taimaka mishi yaje banɗaki, ita dai wannan abu ya zasu yi da wannan sauyin? Baqeer ne ya kalleta muryarshi a karye yace “Umma dan Allah nemo wani ya taimakeni….” Ya kasa karasawa saboda yanayin da yake ji a ƙasan ranshi, tana buɗe ƙofa tayi kicibis da Salim, wata muguwar ajiyar zuciya ta sauke tace “Salim mun gode, dan Allah taimaki abokinka ka shigar dashi banɗaki.”
Gaisheta yayi sannan ya shiga ciki hankali a tashe, ganin Baqeer yayi ya dafa saman goshinshi da hannu, cike da tsokana yace “Wato an farka shine ka dawo da mulkin naka ko?”
Kallonshi kawai Baqeer yayi yama rasa abinda zaice gashi a ɗan matse yake, jiki a sanyaye yace “Please Salim ga wheelchair can taimakeni naje toilet.”
Bai kawo komai ba ya ƙarasa da wheelchair ɗin yaja ya tsaya yana jiran Baqeer ya hau, sai dai ina duk yanda ya motsa ya kasa, mamaki ne ya kama Salim yace “Wai buguwar haka ta wahalar da kai?” Kai ya girgiza kawai yana ji yana magana to tabbas kuka zai yi, wai yau shine ya koma haka?
Jikin Salim rawa ya fara ganin duk yanda yaso daga Baqeer ya kasa ɗaga ƙafar shi, Umma ta shigo ta taimaka da kyar suka sakashi akan kujera, babu abinda kowa ke yi sai hawaye sun kasa ko magana, haka Salim yaja shi banɗaki zuciyarshi na zafi sosai. Suna shigewa Umma ta sake fashewa da kuka a hankali ta ɗauki waya ta ƙira Baba, kamar ba zai ɗauka ba sai kuma taji ya ɗauka, bayan sun gaisa tace “Mallam dan Allah ko zaka kira Bashir yazo babu kowa a gun Baqeer sai yanzu da Salim yazo kasan yana bukatar namiji kusa dashi.”
“Wannan kuma ya dame ni ne? Ko kina son ce mini Bashir mai jinya zai koma? To ni bazan tilastawa yarona ba in yaso yaje ya zauna in bai so ba ra’ayinshi ne, ke a matsayinki na mahaifiyarshi kisan yadda zaki yi.”
Jin kalamanshi tayi kamar an watsa mata ruwan zafi tace “Mallam ka manta wanene? Baqeer ne fa?”
Tsaki yayi yace “Da can bai san shi wanene a gareni ba sai yanzu? Sanda nake mishi faɗa kina ina? Sannan ki gagauta sanar dashi ya tabbatar ya fara rike pencil dan akan shi bazan sadaukar da burina ba, in bashi da ƙafa ai yana da hannun da zai yi zane, lokacin ni da kaina zan kai shi Abuja a keken guragun muje muyi komai tare, wannan shi kaɗai ne uzurin da zan sake yi mishi, kina zaune kin bar yaron nan ya lahanta kanshi kun cuceni daga ke har shi wallahi, sai dai bazan bari ku salwantar da abinda na dade ina fata nake addu’a akai ba shekara da shekaru.” Yana kaiwa nan taji ya kashe wayarshi, daga banɗaki taji ihun Salim, da gudu ta tashi ta ƙarasa tace “Salim lafiya?”
A tsorace ya buɗe ƙofar yace “Umma.”
Idanu ta zaro ganin Baqeer a yashe a ƙasan banɗaki…..
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SHIDA*