Sashe 32
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zainab da tun fara faɗan Mallam Badaru ta kasa zaune ta kasa tsaye mamakin jin tijarar da yake yiwa Umma da Baqeer a tsakar gida cikin mutane kawai take yi kamar ba shine wannan mai ji da Baqeer ɗin ba da baya iya ɓoye soyayyar da yake yi mishi a gaban kowa ma nuna mishi so yake yana alfahari dashi, wai shine yanzu don wani iftila'in rayuwa ya saukar mishi yake neman ya juya mishi baya, ji take yi kamar ta fito ta faffaɗa mishi baƙaƙen maganganu ko ranta yayi sanyi ita dai tasan ko me zai sameta a rayuwa Daddynta ba zai taɓa barinta ba amma shi wannan sai gashi shine ma kan gaba wajen nunawa ɗan nashi ƙiyayya. Kasa haƙurin jure jin waɗannan maganganun tayi ta fito ta fice fuu a fusace ta bar gidan, da kallo ya bita yana tunanin ita kuma wannan wacece, idanunta kan Baqeer suka sauka wanda daidai nan shima ya ɗago ya kalleta, yanayin kallo tayi mishi wanda ya sakashi sake kallonta sai da ta ƙurewa ganinshi sannan kalaman Baba suka dawo dashi daga kallon wurin, me idanunta ke son ce mishi? Meya kawota gidansu yau ma?
Baba yaji ya cigaba da zazzagawa Umma tijara tana tsaye tana zubar da hawaye, shi kuwa Baqeer baƙin cikin yadda Baban yake nuna mishi ne ya cika fal cikin zuciyarshi sai wani irin kallo da yake bin Baban dashi yana tunanin wai dama can haka yake ko kuwa yanzu ne dai ya canja halinshi ganin babu wani amfani da zai iya yi mishi.
Ajiyar zuciya yayi wanda Baban yace “Kai Baqeer ina fada kana sauke mini ajiyar zuciya?”
Kai ya kauda kafin ya samu kanshi da cewa “In ka gaji dani ka sallamani mana, wannan wace irin rayuwa ce?”
Baki buɗe Baba ya kalleshi a fusace yayi kanshi yana neman ya dakeshi cike da hargagi yake cewa “Ni kakewa magana haka?”
Umma ce tayi saurin shan gabanshi tace “Mallam na rokeka da Allah ka bari, wannan wace irin rayuwa ce? Dame ake so yaron nan yaji?”
Kallon Baqeer yayi yanda ko kallonshi baya yi, nan ya sake fusata yace “Ni Baqeer zai yiwa haka? Duk yadda na kula dashi a rayuwa? Sannan ina faɗa ki dinga cemin wace irin rayuwa ce wannan to wallahi yattara kayanshi ya bar min gidana, kuje can kusan abun yi.”
Abu ce tace “Mallam ayi haka? Ba dai almajiranta kake so su fara janshi ba ko? Gurgu ina zai je in ya rasa wurin zama?”
Jamila ce tayi saurin cafewa tace “To ai yanzu barar ma sana’a ce kawai dai yaron Mallam ya girmi sana’ar barar ne.”
Ai kamar sun sake ingizoshi sai cewa yayi “Yaje yayi abinda yafi bara ma ya dameni ne? Na dai faɗa muku wallahi kafin nan zuwa magriba kusan inda kuka kai shi, har ni zai faɗawa magana? Duk ya gama tallata kanshi a titi wato azo aga Baqeer babu ƙafa ko? To kai ma ka ɗana kaji ya zaka yi rayuwa in ba gida.” Yana kaiwa nan ya juya cikin ƙunar rai yayi waje. Umma ce ta kalli Baqeer wanda take tunanin zata ga yana hawaye da mamaki ganinshi tayi garau, kallonta yayi sannan ya ɗan murmusa gefen leɓenshi kaɗan yasa hannu yana tura keken zuwa ɗakin shi. Jikin window yaje ya zubawa waje ido abubuwa da yawa na sake yawo a cikin ranshi, rayuwa kenan, ada ko a mafarki aka ce Babanshi zai yi mishi haka ba zai yarda ba, mutumin da ko dukanshi aka yi a islamiyya da kanshi yake zuwa yaci ma malaman mutunci, wai yau shine ke faɗar ya bar mishi gida.
A hankali ya runtse idanunshi idanuwan yarinyar ne suka sake giftawa ta idanunshi, wai wacece dake neman shigowa rayuwarshi ƙarfi da yaji? Wayarshi ce tayi kara a hankali yasa hannu ya ɗauka sai yaga Salim ne, hakan yasa bai ɗauka ba, ba wai don yayi fushi ba sai dai ba zai bari Baba ya dinga cin zarafin shi ba daga taimako, ya sani abinda Baba yayi mishi tabbas ya taɓa ranshi sosai tunda yasan yadda yake ji in wani yayi mishi gori, kuma shi yanzu dake gaf da tafiya lahira baya ji zai bar Salim ya shiga wani halin saboda shi, saƙo Salim yayi mishi ‘Baqeer ya jikin? Kayi hakuri tun daga ranar nan ban sake zuwa wurinka ba.’
Kamar kada ya mayar mishi saƙon sai kuma dai ya rubuta mishi ‘Salim ina godiya har abada bazan manta da hallacinka gareni ba, haƙiƙa kai aboki na gari ne.’ Yana kaiwa nan ya tura tare da kashe wayar gaba ɗaya.
Sake maida idanunshi yayi ya rufe yana son sanin wani irin kallo yarinyar nan tayi mishi, na tausayi ne ko na jin ƙai? Me take son cewa wanda idanunta suka nuna mishi? Kanshi kawai ya kwantar yana sake yawo da abun a ranshi.
****
Abu ce tace “Tab din jam! Fatima yanzu ya zaku yi? Ba dai da gaske barar zaku fara ba?”
“In ma barar zamu fara ina dai ba Kamalu bane ɗan jagora?” Umma ta faɗa tana komawa ciki ranta a matukar ɓace, Jamila ce ta sheke da dariya tace “Abu kema dai da neman magana kike.”
Wani mugun kallo Abu ta watsa mata ta koma ciki, Jamila ta taɓe baki ta koma nata ɗakin ita ma, haɗin da Abu ta bata rannan ta ɗauko tabbas wannan haɗin ba abin arziki aka bata ba dan gashi sai cusawa take yi bata ga wani canji daga Mallam ba iya kace ma kwanciyar da ƙyar take samu suke gamawa.
Ƙwafa tayi tace “Muguwa wato ni zaki cuta ko? To nima zaki ga wulakanci, ai ina da mutane a Sokoto, mu saka ƙafar wando ni dake.
Umma kuwa tana shiga ɗaki ta ɗauki waya ta kira Maryam da Hadiza ta sanar dasu suzo gida akwai gagarumar matsala.
*****
Da ƙarfi ta daki steering wheel na motar tana sauke wani huci tare da furzar da iskar dake bakinta, ji take yu zuciyarta na wani irin azalzala, da ƙyar ta kai kanta gida tana shiga ta maida ƙofar motar cikin ƙarfi ta nufi ciki da sauri, Mummy na kitchen ana ta shiryawa Daddy abinci don yau akwai baƙin daya gayyata zasu zo. Zeey na shiga ta ƙarasa wurinta da gudu ta rungumeta.
Bayanta ta shiga shafawa tana cewa “Ya isa haka nan, ni kam meke damunki ne gaba ɗaya kin canza? Kin san maganarki nawa kuwa daga jiya zuwa yau?”
Zeey ta ɗago ga mamakin Mummy hawaye ta gani a fuskarta, hankalinta ne yayi mugun tashi ta kamata suka yi ɗaki a bakin gado ta zaunar da ita ta kwantar da kanta saman cinyarta tana shafa saman kanta tana cewa “Zainab menene? Menene yake damar mini ke haka?”
Kallon Mummy tayi ta share hawayenta tace “Mummy nima ban san meke damuna ba, takaici ne kawai yake damuna na rasa yadda zanyi nayi magana.”
“Kamar ya kenan?”
Yawun bakinta ta haɗiya tace “Mummy ashe iyaye ba zasu iya yarda da ƙaddara ba in Allah ya jarabci ɗan su? Ashe iyaye zasu iya manta soyayyar da suke yiwa ɗa saboda ya samu wani giɓi a rayuwar shi? Mummy ta yaya hakan zata kasance?”
Murmushi ta ɗan yi kaɗan tace “Ba lallai sun manta da soyayyar bane watakila dai abinda ya samu ɗan nasu ne ke damunsu sosai wanda yasa suke huce takaici a baibai.”
Kai ta girgiza tace “A’a wannan ba haka bane.”
Ta sake shafar kanta tace “Kin san Allah yayi mu daban-daban dole wasu halayensu zai banbanta, amma ke menene naki na damuwa? Ko wanda aka yiwa hakan kin sanshi ne?”
Kallon Mummy tayi da sauri, Mummyn tace “Namiji ne?”
A zabure Zeey ta miƙe tace “A’a mace ce sannan ba wai saninta nayi ba Mummy a hanya na gani shine abun ya dameni.”
Kai ta jinjina cike da gamsuwa don tasan Zeey da tausayi, shi yasa abin bai wani bata mamaki ba.
******
Maryam da Hadiza sun sha kuka jin abinda ke faruwa, jiki a sanyaye Maryam tace “Ni matsalata uban miji, da zai bari da sai na kaishi BQ na gidana ya zauna, amma kun san halinshi dai yana gani na tafi dashi gidan sai hakan ya zama abun magana har ma ya nemi haɗa fitina a tsakanina da Baban Aareef.”
Umma ta girgiza kai tace “Kema kin san ba bari zai yi ba don haka kar ma ki fara.”
Hadiza tace “wurin Dada ne kawai ya rage mana amma ta tsufa Umma ita kanta tana buƙatar mai kula da ita.”
Maryam tace “Ya zamu yi? Haka nan zamu kaishi sai mu nemi mai aiki ko a layin ne ta dinga zuwa tana gyara gidan da safe.”
Shiru suka yi don tabbas sunsan basu da wata mafita data wuce wannan.
Cikin takaici Maryam tace “Gwara ma ya bar gidan don zamanshi anan ba abinda zai jawo mishi sai depression, ace gidan iyayenka sam baka da kwanciyar hankali?”
Hadiza ta girgiza kai tace “Wallahi abin nan na cimin rai dole mu tashi mu nemi kuɗi mu taimakawa Ya Baqeer wahalar da yayi damu shekara da shekaru muma mu nuna mishi yana da ƴan uwa masu ƙaunarshi.”
Umma ta share kwalla tabbas itama tana ganin gwara ya bar gidan don ko kalmar bara dasu Abu ke ambata inta tuna ranta ɓaci yake yi.
Haka su Maryam suka kwashe kayanshi aka saka a motarta, nan suka jawo kekenshi, wani babban almajiri ya taimaka aka sakashi a mota ko sallama basu yiwa su Abu ba suka yi gaba.
Abu na ciki ta fito da sauri jin ƴar hayaniya kaɗan, Jamila ma ta fito da sauri suka kalli Umma dake tattare kaya a tsakar gida suka kalli juna, Abu tace “Na ɗauka ma baƙi aka yi?”
Umma ko tankasu bata yi ba ta cigaba da aikinta, tunanin saida injin taliyarta ne ya faɗo mata akan ta sayar ta aikawa Dada da kuɗin su fara amfani dashi kafin ta samu abun yi.