← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 168

Sashe 57

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da mamaki Zeey ke kallon motar da aka yi parking a harabar gidan, in har ba wai tayi kuskure ba motar Mummy ce, to yaushe tazo? Tambayar data faɗo mata cikin rai kenan, da sauri ta ƙarasa ciki fuskarta ɗauke da fara'a don tasan Mummy missing ɗinta ne yayi mata yawa,  harta shiga falon bata ga kowa ba, hakan yasa ta nufi ɗakin Inna kai tsaye don daga cikin falon tana iya jiyo magana na fitowa daga sama-sama don dama ta gaji da takurar Inna gwara ta bita su koma gida gashi kuma ta samu Junaid  zai dinga taimakawa Baqeer.
Hannu tasa zata ƙwanƙwasa taji muryar Inna na cewa "Ke sam kamar ba uwa ba baki san me ya kamata ba? Wannan wace irin rayuwa kika ɗaukar wa kanki? Kenan ke baki san abinda ya kamata ba? Ko ce miki aka yi ita ba....." Ƙofar ta buɗe wanda hakan yasa su kallonta da sauri, ajiyar zuciya tayi zuciyarta na tafasa idanunta a kansu tace "Ni kam don Allah sai yaushe zaku daina faɗa a kaina? Wannan wace irin rayuwa ce?"
Mummy ce ta taho tana neman riƙeta ta ɗaga mata hannu tace "Mummy please ki bari, ni yarinya ce? Ko kuwa shi kenan ni ban isa nace zanyi abu ba? Gidanku ne fa ba wai wani wurin naje ba amma sai kin nuna kamar ana wahalar dani?"
Inna ce tayi tsaki tace "Ba sai tai tayi ba ni dai na faɗa ban gayyaceki ba don haka babu wanda zai zo ya ɓata mini rai a cikin gida don haka ki tattara ki bita."
Takaici ne ya rufe Zeey kawai ta wuce ɗakin su da gudu, kan gado ta faɗa tana kallon Nabeela dake zaune tana karatu cike da shagwaɓa kamar mai shirin yin kuka tace "Aunty Nabs wai haka zamu zubawa Mummy da Inna ido? Shi kenan su daga sun haɗu sai faɗa, ba zaka taɓa ganinsu suna hirar arziƙi ba? Wannan wace irin rayuwa suka ɗaukarwa kansu? Ƴa da uwa kamar wasu maƙiyan juna? Kuma babban takaicina duk a kaina suke wannan abun?"
Jiki a sanyaye Nabeela ke kallonta tace "To ya zamu yi dasu? Ni shi yasa muna gaisawa na bar musu falon don nasan dama raina ne kawai zai zo ɓaci."
Kanta tasa a saman pillow cikin takaici tace "Ni wallahi na gaji da wannan abin nasu haba! Da zan bi Mummy mu koma gida amma yanzu Allah babu inda zani." Ta faɗa tana juya baya zuwa saitin Nabeela tana tunanin wannan rashin jituwa ta Mummy da Inna.
Ita dai Nabeela kai kawai ta girgiza ta cigaba da karatunta don bata shiga wannan case ɗin.
Mummy ce ta shigo ɗakin tana yiwa Nabeela alama da tayi shiru har ta ƙaraso ta zauna kusa da Zeey, hannu tasa ta ɗan mintsineta kaɗan, Zeey ta juyo da sauri rungumeta tayi tace “Mummy please!”
Nabeela ce ta tashi ta bar musu ɗakin hakan yasa Mummy shafar bayan Zee tace “Naji ya isa am sorry shikenan?”
Kallonta tayi tace “Bana son ku dinga faɗan nan, especially a kaina don Allah!”
Jinjina kai tayi cike da fahimta tace “Naji to tashi mu wuce.”
Ajiyar zuciya ta saki tace “Please Mummy ki bar ni zuwa jibi, abubuwa ne a kaina wallahi gaba ɗaya ni kaina ban san meke damuna ba, watakila faɗan Inna zai sa na dawo hayyacina.”
Cike da mamaki take kallonta tace “Har akwai wani abu da zai hanaki sukuni a duniyar nan Zeey? Dad ɗinki yafi sonki a gida kema kin sani kaf duniya yafi ji dake sama da komai.”
Fuska ta tsuke sosai tace “Kema kin san zolaya kike Mummy ni gaba ɗaya…….”
Ta maida kanta kan cinyar Mummy cike da damuwa tace “Ban san ya zanyi ba sam haushin kaina da damuwar halin da nake ciki ya isheni.”
Shafar kanta tayi tace “Koma menene kar ya dameki, a duniya mahaifinki ko me kike so zai tsaya miki ki samu, haka duk wani abu da bai fi ƙarfina ba kema kin san zan tabbatar kin samu abun nan, don haka ki sanar dani koma menene, na gaji da ganinki cikin wannan halin.”
Tace me to? Bayan ita kanta bata san mazaunin da take ba?
Mikewa tayi ta zauna a gaban Mummy ta lanƙwashe ƙafa a kan gado tace “Mummy mutum ne ya shiga raina, komai nake yi da tunaninshi nake yi bayan na kuma san bani da haɗi dashi to cut it short ma ni dashi enemies ne wanda am sure ko sunana yaji ya ganeni kallona ba zai sake yi ba, sai dai ban san meke damuna ba.”
Da mamaki take kallonta tace “Son shi kike yi?”
Kai ta girgiza da sauri tace “No of course not! Sannan ba ma lafiya gareshi ba kina ganin tausayi ne yasa nake jin hakan?”
Shiru tayi tana nazari na wajen minti uku kafin tace “Ban san meke ranki ba Zeey sai dai nasan koma menene na baki damar kiyi abinda hankalinki ya kwanta dashi, a koda yaushe ina bayanki.”
Rungumeta tayi tace “Mummy I love you so much, zan yi ƙoƙari nayi sorting tunanina kafin jibi in na dawo zan sanar dake komai.”
Kai ta jinjina cike da gamsuwa sannan tace “Kuɗi fa kina bukata?”
Kai ta girgiza tace “Har yanzu wanda Dad ya bani ban ma ci ko rabi ba.”
“Bari na wuce.” Saukowa tayi daga kan gadon suka fito falo, har yanzu Inna bata fito ba da alama Nabeela na wurinta don suna iya jiyo dariyarsu ita da Nabeela daga falon, Zeey na mamakin wannan abu a koda yaushe Inna bata fushi da Nabeela amma baka taɓa ganin fara’arta da Mummy.
Haka Mummy ta wuce ita kuma ta koma ɗaki, zuciyarta na tunanin ko Baqeer yana can yana exercise ɗin kuwa? Haka kawai sai taji murmushi ya kamata.

******
Washegari…….

Umma tana gugar kayan Baqeer ragowar da aka bari a gidan tana so ta tattara ta samu taje ta ganshi, ita dai fatanta Allah yasa ya barta taje, tana mamakin yadda duk kwanakin da Baqeer yayi a gidan Dada har yau Badaru bai tambayi ina aka kai shi ba bai kuma tambayi lafiyarsh ba, ita sam dama bata damu da sai dole yazo ɗakinta ba amma a ƙalla soyayyar da yake nuna wa Baqeer bai ci ace ta gushe lokaci guda ba.
Kamar daga sama taji ance “Hadiza? Uban me kike mini a gida har da ƴaƴanki da ƙatuwar jaka?”
Garin razana da Umma tayi bata san sanda dutsen gugar ya ɗan shafeta ba, da sauri ta ajiye a gefe tunda na gawayi ne ta fito cikin sauri tana addu’ar Allah yasa ba Hadizanta bace yake magana akai.
A tsugune taga Hadiza tana share ƙwalla tana gaida mahaifin nasu.
A fusace ya nuna mata hanyar waje yace “Wallahi tun kan ranki ya ɓaci ki tashi ki bar mini gida, bana son haukar banza da wofi, bazan aurar da ƴara ba sannan su dawo mun gida da jaka don wannan jakar ko ban tambaya ba nasan ta yaji ce, ko ƙarya nayi?”
Hawaye ta share tace “Baba don Allah ka tsaya ka saurareni wallahi auren nan sam……”
“Kina sake magana zan sallami uwarki kuje can ku ƙarata, yau naga shirmen banza da wofi ni dama yanzu na cire rai da yaran Fatima amma babu ƙatuwar macen da zata dawo mini gida bayan ta cinye kayan gara da kayan ɗakin da na kashe kuɗi nayi mata.”
“Ai dai gidan mahaifinta ne ko? To in ma komawar ne ba dai yau ba, don kuwa babu inda zata". Cike da dakiya Umma ctayi maganar duk kuwa da irin faɗuwar da gabanta yake yi.
Salati Abu ta saka tana tafa hanu tace “Fatima? Wai Mallam kike yiwa magana haka gatsal? Ba tarbiyya babu biyayya? Tab lallai kin riƙa, wannan ai tarbiyar da take amfani da ita kenan shi yasa aka korota.”
Nan da nan kuwa Badaru ya sake tunzura yace “Ki kwashi shirginki kibar mini gida kema, sai kuje can kuyi yawin tare tunda iskancin naku ya isa.”
Umma bata tanka mishi ba tasa hannu taja Hadiza da ƴaƴanta suka shiga ɗaki tasa makulli ta rufe, suna jiyoshi yana zazzaga masifa amma babu wanda ya tanka a cikinsu sai Abu dake ta sake tunzurashi, Jamila mamaki duk ya rufeta wai yaushe Abu ta kile har haka? Bayan aurenta ne ta koya mata maida martani?
Umma suna shiga ta kalli Hadiza dake ta kuka ga Aydah a bayanta itama kamar tasan me ake yi kawai kalle kake take yi ga ƴan biyu da alama bacvi ma suke ji, kuka sosai take yi Umma tayi shiru ita ma tana matsar ƙwalla a fakaice, wannan wani irin bala’i ne.
Chapter 57 · 0% Book details