← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 168

Sashe 80

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

****
Zainab ce ta kalli Nabeela tace “Haka Mummy tace?” Nabeela dake share ƙwalla ta ɗaga kai alamar to, da sauri ta fita daga ɗakin ta nufi falo. Mummy na zaune suna hira da Daddy ta zauna a gefen ta tace “Mummy don Allah ki yiwa Aunty Nabs magana tace ke kika ce ta tafi?”
Fuska sosai ta tamke tace “Auta ƙyaleta gwara taje ta zauna kusa da Inna tana buƙatar taimako.”
Daddy ne ya kalleta yace “In ba don Nabeela ba a gidan nan kina tunanin komai zai tafi daidai? Kika jure wannan sai Nabeela ce kullum ke laifi?”
Zeey ce ta turo baki tace “Ni dai kullum nice mai hali mara kyau.”
“Yanzu amsa min ɗin da kika yi a haka shima daidai ne kenan? Nabeela kuwa ko da wasa baza tayi magana haka ba ko da bare ne ya mata magana kuwa bare.” Mummy ce tayi saurin cewa “Don Allah ka bari Senate, ita dai bata isa tayi magana ba sai an ce maganar ma bata yi daidai ba?” Kai ya kawar ya ɗauki jarida bai tanka musu ba, yana murmushi don shi kam yasan lamarinsu sai a hankali sam Mummy bata taɓa ganin laifin Zeey, kafaɗarshi ta dafa tace “Ranka ya daɗe ba dai fushi kayi ba? Kai ya girgiza yana kallon Zeey yace “Sai kuyi tayi, sannan a halayen ta kuma bata tunanin bin umarnina ta auri namijin da nasan zai jure halayyarta.” Tana jin haka tayi maza ta tashi tace “Daddy na manta ina da abun yi a ɗaki.” Ta fara tafiya da sauri sai data kai ƙofar fita daga falon ta waigo tace “Mummy sorry amma bazan barta ta koma ba gaskiya, Daddy sai da safe.” Ta waiga da sauri, Kabir ta gani a tsaye da alama ma tsayawa yayi don yaji me suke cewa, wani banzan kallo yayi mata yace “Akan me bazata koma ba? Ko ke ce kika haifeta?”
“Kaga don Allah ka bari, kai wai a duniya ba zamu zauna lafiya ba? Neman faɗa har da wanda bai shafeka ba?” Ranshi ne ya ɓaci ganin shi Nabeela ke takurawa a gidan nan don yanzu saboda ita zaman gidan ma ba sosai yake san yin shi ba yayi ƙwafa sannan ya juya, kallonshi tayi ta harari bayanshi sannan ta bishi a baya tana cewa “Yaya K please kasan masu ɗinki irin professionals ɗin nan na mata?”
Cak ya tsaya sannan ya kalleta yace “Ɗinki ina wanda yake yi miki na wurin Mummy?” Ta ɗan yi kif da ido sannan tace “Ba ni zanyi ba sannan bata son na Mummy wani take son gwadawa.”
Jim ya ɗanyi sannan yace “Akwai amma sai na yiwa Najib……..” ai kafin ma ya ƙarasa tace “No, kada ka damu nama tuna.” Ta shiga ɗaki tana cewa “Rabani da abokinka yanzu in Baqeer ya sani am sure..” sai kuma tayi shiru kafin tayi ajiyar zuciya a fili tace “Always getting ahead of yourself, a wani waje Baqeer ya ajiyeki?” Kan gado ta faɗa ta ɗauko wayarta, nan da nan ta zaro ido tana ganin tambayar da yayi mata, bata san sanda ta saki wani irin ƙara ba tana bubbuga ƙafa kai kace wani kyauta aka bata. Ta fito daga ɗakin da gudu ta nufi ɗakin Nabeela wacce ke zaune ta saka akwati a gaba, janye akwatin tayi ta riƙo hannunta tace “Aunty Nabs yau shi ya fara nemana.” Da mamaki take kallonta tace “Wa?” Kai ta girgiza tana daidaita nutsuwarta tace “Mu bar wannan maganar, don Allah me yake nufi idan namiji ya miki text yace All good?”
Ɗan yatsuna fuska Nabeela tayi tace “All good? Har wani kalma ne mai ma’ana daban?”
Saketa tayi tace “Share baza ki gane ba,” tayi maganar tana fita, kan gado ta faɗa tayi rub da ciki sannan ta kira Baqeer, a lokacin shi kam har ya gaji da jin haushin kanshi da saƙon daya tura yana ganin gashi nan ya janyowa kanshi rashin reply ai, wanda a ganinshi bada kanshi ya gama yi. Ɗauka yayi ba tare da yace komai ba, ita ma bata ce komai ba har kusan sakan bakwai sannan yayi ɗan gyaran murya ita ma gyaran muryar tayi suka sake ɗan shiru kafin ta sake gyaran murya, “Mura kike yi?” Ya tambaya ganin abun nata ba irin nashi bane.”
“Matsalar a zauna kusa da masu mura kenan sai su sa maka before you know it.”
“Wa ke mura?” Ta dan rage murya tace “Kai mana Ya Baqeer ka manta kai ka fara gyaran murya?”
“Don nayi gyaran murya sai akace kuma mura nake yi?” Ta ɗan kwantar da kanta akan pillow tace “Kuma fa haka ne to ba mura nake yi ba ciwon GM nake.”
Yanayinshi ne ya canza zuwa na damuwa yace “GM? Me kenan?” Ta dan yi jim sannan tace “G for gyara, M for murya?” Duk yadda Baqeer yaso ya daure kasawa yayi kawai yaji dariya tazo mishi, wani irin shauƙi ne ya dinga ratsa sassan jikinta babu shakka ƙaunar da take yiwa Baqeer ta riga ta gama bin jini da jijiyarta. Yatsa yasa ya sosa kunnenshi ya daidaita kanshi sannan yace “Umma tazo yau.” Tace “Haba? Kai masha Allah kace yau cikin farin ciki kake.” Yace “Uhmm!” Ta dan ja bargo wani tunani na shiga ranta tace “In tambayeka?” Yace “Eh!” Ta ɗan sake yin shiru kafin tace “Ka yarda dani?” Da mamakin kalamanta yace “Kamar ya?” Kai ta girgiza tace “Kawai tambaya ce.” Shiru yayi bai amsa ba, jin haka yasa tace “Ina Dada ta?”
“Ta kwanta,” ya faɗa yana kallon wayarshi, so yake ya sanar da ita zancen contracts amma yana tunani gwara ya bari yayi signing tukunna don ya kula tafi kowa farin ciki in taga abun alkairi ya sameshi to gwara ya jinkirta sanar da ita har sai ya tabbatar da contracts ɗin .
Sun ɗan yi shiru kafin yace “Yace sai da safe.” Har zai kashe tayi saurin cewa “Ya Baqeer?” Tsayawa yayi sai dai yanda ta kira shi yasa yaji dim ta ɗan rage murya sosai, cikin wani yanayi tace “Baka ji amsar tambayar da kayi mini ba.” Kasa amsata yayi saboda yanayin daya shiga jin yadda tayi maganar, nan ta cigaba “All good, sannan thank you for asking.” Wani abu ne ya ɗan tokareshi da sauri ya kashe wayar yana mamakin abinda ke faruwa dashi, Zeey kuwa iska ta furzar da karfi tana shafa sumar kanta.
****
Umma tana dawowa ta tarar da Jamila da Abu a zaune yau yan haɗin kan nasu ya tashi dan suna zaune tare suna hira, tasa key zata buɗe ƙofar ɗakinta sai taji ƙofar a buɗe, da mamaki ta kallesu gani tayi sun kawar da kai, ta ciki aka buɗe ƙofar da ƙarfi wanda ya sata tsorata kaɗan ta ɗan yi baya.
Badaru ne ya banƙare kofar ya fito yana kallonta sheƙeƙe yace “Eh dama ni nasan ba mutunci ne dake ba kwanan nan, yanzu ko kunya da imani baki ji ba kika yi miya kika juye tas kika kaiwa tsohuwa ni da yake baki ɗauke ni da daraja ba baki ajiye mini ba? Bayan ke kin san Jamila ba lafiya ne da ita ba bazata iya girki yau ba?”
Mamakin kalamanshi ne suka rufeta, ba yau ta saba yin miyar nan ba menene suke neman maida abun wani zance daban? Sannan yaushe Jamila ta fara ciwo? Kafin ta gama tunani sai ji tayi Abu na cewa “Sannu Jamila, Allah dai ya baki lafiya.” Mallam kayi hakuri ni wallahi naso yin girki  kuɗi ne sam babu a hannuna.”
Kallonta ya sake yi yace “Allah wadan naka ya lalace wannan mugun halin naki shi yaranki suke kwaikwaya shi yasa rayuwar auransu ba daɗi kuma wallahi ni da siyan kujeru ke da saidawa sannan ke da cinye kuɗin.” Rai a ɓace ya wuceta ya shiga ɓangaren Jamila, Fatima ciki kawai tayi don ita ta ɗauka ma zancen fili zai yi to in dai wannan ne ita kam ko a jikinta yaje can su ƙarata, da can da take miyar ai bai taɓa sa ido ba sai yanzu, ita fa duk wani abinshi yanzu ya daina hata haushi.
Chapter 80 · 0% Book details