← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 168

Sashe 74

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******
Zeey da tsantsar farin ciki ta shigo gida, parking tayi mai gadi ya taho da sauri ya miƙa mata leda yace “Hajiya gashi wai inji Sadaath wai ku hadu ko a menene din soyayya?”
Wani banzan kallo ta yiwa ledar tace “Waye hakan?”
Yace “Wannan dai yaron da yake zuwa nemanki.”
“Ban san shi ba ban kuma san daga ina yake ba, ka ajiye in ya dawo ka maida mishi bana son hauka please.”
Tana kaiwa nan tayi ciki, ɗakin Mummy tayi tana ganinta ta rungumeta ƙam tana cewa “Mummy na kalli.”
Amsa tayi ta buɗe jakar, nan ta zaro ido tace “Inji wa?”
Shigewa jikinta tayi tace “Wanda ya sakani jin duniyar babu daɗi kwana biyu.”
Dariya tayi tace “Wai harda rose? ashe kun fara dating?”
Kai ta girgiza tare da sauke ajiyar zuciya tace “Wannan clueless man ɗin kawai siya yayi ba da wata manufa ba, Mummy kina ganin so ne ke damuna ko?”
Kuncinta ta ɗan jaa tace “ɗari bisa ɗari kawai dai tsorona mahaifinki, kinga Junaid yake son baki bana son ku samu matsala.”
Baki ta taɓe tace “Nifa kin san babu mai takura mini nayi abinda bana so, sannan Daddy fa don siyasarshi yake son aurar dani ga Junaid kema kin sani.”
Riƙo hanunta tayi tace “Kada ki damu kisa a ranki ni ina bayanki a koda yaushe.”
Kai ta ɗaga cikin jin daɗi tace “Shi yasa nake sonki Mummy na.”
“An dai girma ba’a san an girma ba.” Nabeela ta faɗa tana daga tsaye jikin ƙofar, Zeey ta ƙara ƙanƙameta tace “Ke dai Aunty Nabs ko kishi kike? Ko muje ki rungumi Inna hankalinki ya kwanta.”
Maimakon ta bata amsa kawai juyawa tayi, abincin Kabir ta ɗauka tayi ɗakin shi, bata ko ƙwanƙwasa ba ta shiga, ya fito daga wanka kenan da towel a ƙasan shi sai kuma ƙarami yana goge kanshi, a zabure ya kalleta yasa hannu ya rufe ƙirjinshi yace “Meye hakan?”
Juya baya tayi da sauri tace “Sorry KB ban kula ba.”
Riga yayi sauri ya zura yace “To ba sai ki fita ba me kike yi anan?”
Waigowa tayi ta tako har inda yake tana murmushi tace “Plz Kabir ka canza tunaninka, wallahi it's not a big deal.”
Matsawa yayi ya juya mata baya, da sauri ta saƙalo hannunta ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi, gabanshi ne ya shiga faduwa don duk rigimar Kabiru baya harkar mata ba kuma ya shaye-shaye tace “Baka so na kasance kusa dakai?”
Waigowa yayi yace “Nabeela please!” Yayi maganar yana janye jikinshi, idanunta ne ya cicciko tace “Allah ne ya ƙaddara mini nima ba ni nasa wa kaina ba.”
“Please enough don Allah! Ke wai me yasa kike yin abu babu tunani? Don Allah kada ki sake yi mini haka, ya isheni haka nan bana son shirme please.”
Yana kaiwa nan ya fita ma ya bar mata ɗakin, hawayenta ta share ta fito, Mummy ce ta ganta tana shiga ɗakinta ita ma ta shiga tace “Me nace miki? Wai uban me kike zuwa yi ɗakin Kabir?”
Kai ta kawar tana ƙoƙarin zama tace “Abinci na kai mishi.”
“Yaushe kika zama mai kai mishi abinci? Ha’a wallahi zaki tattara ki koma gida wannan shine last warning da zan miki tana kaiwa nan ta fito.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
        *Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
       *DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA SHIDA*

{46}

Tun da suka rabu da Zainab yake tunanin ta yadda zai yi ya faɗaɗa sana'arshi, ba zai yiwu ace yana daga zaune komai sai tayi mishi ba. Ta dai yi mishi hanyar yadda zai kafa tubalin business ɗin shi amma dole yayi komai da hannunshi, dole yasan yadda zai yi ya nemi customers da kanshi kafin ya nemi tailoring school ya shiga don a yanzu yaji babu abinda yake da bukatar yi irin sana'ar ɗinki, dama can yana da passion for ɗinkin harkar zanen nan ce ta ɗauke mishi hankali da kuma Baba da ya hana mishi damar da zai koyi ɗinkin don a cewarshi babu abinda zai yi dashi bayan yana da sana'ar da tafi ɗinkin da yake so daraja da kawo kudi. Wayarshi ya ɗauka ya kira Salim yace idan ya samu dama yazo yana nemanshi, dole yana da buƙatar mataimaki a yanzu kuma da Salim kaɗai ya yarda shi yasa ma zai janyo shi suyi harkar tare. Kafin gari ya waye yayi duk wasu tsare-tsare na yadda zai faɗaɗa kasuwancin nashi akan takarda, zuwan Salim kawai yake jira ya nuna mishi abinda ya tsara zasu yi.
Da wuri kuwa Salim yazo don tun da yaga kiran wayar Baqeer jiya bayan har ya kwanta yasan cewa abu mai muhimmanci yasa yake neman shi. Tare suka karya sai da suka gama sannan Baqeer ya ɗauko takardar nan ya nuna mishi. "Yanzu dai dole mu nemi masu sayen sketches ɗin idan anyi don ba zai yiwu muce yarinyar can ce zata samo mana masu saya ba, ta dai kafa mini tubalin kasuwancin and I really appreciate her for that amma ya kamata ace na karɓi komai ya dawo hannuna ba wai ina daga zaune komai sai anyi mini ba, tana da rayuwarta kaga bai kamata mu dogara da ita ba, sannan tana mace bai ma kamata ta dinga bin mutane saboda mu ba.”
Salim ya jinjina kai yace "Wannan shawara ce mai kyau Baqeer its high time dama ka tashi ka gyara rayuwarka ka sani cewa babu mai taimakonka sai har idan kai ka taimaki kanka, babu wani dalili da don Allah ya jarabce ka da disability shikenan kace rayuwarka ta kare bayan yayi hakan ne don ya jarrabi imaninka. wannan tsarin da ka kawo mai kyau ne kuma In Sha Allah zan tuntubi wasu tailors dana sani akan sayen sketches din namu duk da dai ba directly zamu nemesu da su sayi kayanmu bane zamu ɓullo musu ta yadda Zainab ta yiwa wancan telan sai mu haɗa dasu Maryam idan zasu yi dinki a basu sketch din su kai daga haka idan har suna buqata su zasu kawo kansu da kansu ba sai mun bisu ba, sai kuma sabon page da zamu bude a ig da zamu dinga ɗora hotunan sketches din idan anyi sai kuma mu ƙirƙiri sunan da za'a sakawa business ɗin sai kuma muyi logo da zamu dinga ɗorawa a jikin sketches ɗin saboda masu satar fasaha". Haka dai suka zauna suka yi ta tsare-tsare har wani lokaci, basu tashi ba sai da Dada ta gabatar musu da abincin rana sannan suka yi akwala suka fita masallaci suka yi sallah sai da suka dawo ne suka ci abincin. Da Salim zai tafi ya karbi wasu daga cikin sketches ɗin akan zai kaiwa Maryam ta kaiwa telanta ya ɗinka yasan zai yi wuya shima bai biyosu ba kamar dai yadda wancan telan yayi. Akan haka suka rabu Baqeer ya koma ya kwanta yana jin wata irin nutsuwa na sauka a cikin zuciyarshi, dama can har da  rashin abun yi yasa damuwarshi ta yawaita amma yanzu ya samu nutsuwa tunda ya samu wani abun yin da ko bai sayarwa da wani ba zai iya yi da kanshi don a yanzu nema yake ƙara jin son koyon ɗinki fiye da shekarun baya da sha'awa kawai yake bashi.

*****

Lokaci zuwa lokaci Zeey ke sakin murmuahi idan ta tuno da kyautar da Baqeer yayi mata, duk da turaren bai kai tsadar wanda take amfani dashi ba amma sosai taji daɗin kyautar kuma take jin son turaren cikin ranta bare idan ta tuna da rose flower ɗin daya haɗa mata dashi sai tace anya kuwa shima baya jin irin yadda take ji a kanshi a kanta? Idan ta tuna da cewar da yayi kuma wai taje wajen saurayinta yayi mata allura sai taji wata dariya ta kamata. "Is he jealous?" ta samu kanta da yiwa kanta wannan tambayar sai kuma tace kai a'a zai yi wuya ace kishi yake yi bayan ko damuwa bai yi da ita ba idan har ba ita ta nemeshi ba shi sam baya nemanta, gaskiya bata zaton yana jin irin abinda take ji a kanshi tunda gashi ita bata iya yin dogon fushi dashi ko tayi ma da kanta take bawa kanta haƙuri ta huce amma shi yana iya shareta idan har bata nemeshi ba baya iya nemanta. Bedside drawer dake gefenta ta janyo ta fito da rose flower ɗin ta shinshina tana lumshe ido tana jin wani shauƙi da farin ciki na kamata duk ta tuna wannan kyautar daga hannun Baqeer ta fito, wani ƙwayar mutum guda ɗaya da a yanzu take jin dukkanin wani farin cikinta ya ta'allaƙa ne da kasancewarshi cikin farin ciki da walwala, har mamakin yadda ta damu dashi da yawa har haka take yi bayan tasan a daa can babu wani shiri a tsakaninsu, koda yake tafi danganta rashin jituwar tasu ta wancan lokacin da yarinta.
Chapter 74 · 0% Book details