Sashe 149
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA BIYU*
{92}
Kallon cikin motar Umma take yi tana ƙara godewa Allah da irin baiwar da yayi wa ɗanta, da Badaru ya koreshi saboda yana ganin babu wani sauran amfani da zai yi mishi sai korar ta zame mishi alheri gashi yanzu sanadin hakan Allah yayi mishi arziƙin da ba lallai yayi ba idan a gaban Badaru yake. Shiru tayi a cikin motar ta kasa cewa komai sai Hadiza da Tanimu ne suke ta hirarsu sai jefi-jefi Baqeer ke saka musu baki har suka ƙarasa gidan Dada. Yanzu ya zama dole yayi ƙoƙari ya cikawa masu gidan can kuɗaɗen su don ya samu a shirya gidan cikin lokaci tunda gashi ya ɗauko Umma a lokacin da bai gama shiryawa ba, da farko da ya bari ne sai ya gama cika musu kuɗin gidan an zuba furniture kafin yaje ya ɗauko Umman to kuma sai wannan al'amarin ya faru da yasa dole ya rabota da gidan.
Gaba ɗaya suka shiga gidan Dada da Baqeer yasa aka gyara aka mayar dashi na zamani sosai kamar ba gidan tsohuwa ba. Ganin suna shigowa da kayan Umma yasa tace "Ke kuma lafiya? Ina Badarun kika tattaro kika dawo gida?" Zama tayi akan tabarmar da Dadan ke zaune kafin tace wani abu Baqeer yace "Na rabota da wancan gidan ne Dada ba zata sake komawa ba."
Kallon mamaki Dada tayi mishi duk da tasha jin shi yana zancen zai ɗauke Fatima ya rabata da zaman gidansu ba sau ɗaya ba sau biyu ba amma bata taɓa tunanin zai aiwatar ba, duk tunaninta yana dai faɗa ne saboda takaicin halin uban su ashe shi da gaske yake yi, murmushi tayi ta girgiza kai tace "In banda abinka Baqeeru ta yaya zaka rabo mace daga gidan aurenta mijinta bai saketa ba, a ina ake yin haka saboda Allah?"
Yana tafiya ɗakin shi ya bata amsa da "Za’a fara akaina, ni dai na ɗauko ta kuma baza ta koma ba," yayi shigewarshi ɗakin shi. Hadiza ce tace "Allah Dada Baban ne baya da kirki, yanzu haka idan kin ji abinda yayi ba zaki sake ganin laifin Ya Baqeer ba."
Harararta Dada tayi tace "Kome yayi ai dai uban ku ne har kike cewa baya da kirki." Ƴar dariya Hadiza tayi tace "Hhamm Dada kenan, wai fa zuwa nayi gidan na tarar an ɗebo musu ƴan sanda Kamalu yayi sata shine Baba yake bayar da shaida akan Umma wai ta sace mishi takardun filinshi a haɗa har da ita a tafi bayan takardun filin da yake magana akai na Ya Baqeer ne ba nashi bane."
"Allah ya kyauta," kawai Dada tace ta juya tana amsa gaisuwar da Umma take yi mata. Tashi Hadiza tayi ta kwashe kayan Umma ta kai ɗakun Dada, sai da ta shirya kayan tsaf sannan ta fito tayi musu sallama zata tafi gida saboda yamma tayi ta baro yara a gida.
Hadiza na fita Umma ta tashi ta shiga ɗaki, ta rasa tunani guda ɗaya da zata kama sai take ganin al'amarin kamar a mafarki sai dai idan ta ɗaga ido ta kalli Baqeer yau bayan wani tsawon lokaci Allah ya ƙara haɗa su zama a muhalli guda sai tasan cewa ba mafarki take yi ba.
*****
Zaɓe yana ta matsowa saboda haka hankalin kowanne ɗan takara ya tashi, kowa burin shi ace yau shi yayi nasarar lashe kujerar daya fito nema. Primary Elections za'a yi a jam'iyyar su Daddy don haka hankalin shi ya kasa kwanciya domin abokin takarar shi na neman saye ƴan jam'iyyar da kuɗi duk da shima ba baya ba wajen yi musu ɓarin kuɗin duk don ya samu su zaɓe shi a matsayin ɗan takarar jam'iyyar tasu. Yau sun fita yawon campaign a wani ƙauye basu baro garin ba sai dare. Suna tafe a hanya motocin campaign ɗin sai zura uban gudu suke yi a titi suka yi wani mummunan accident. Haka mutane suka yi dafifi akan su ana ta fitar da mutane daga cikin motocin da hatsarin ya rutsa dasu, wasu sun rasu wasu sun ji munanan ciwo, a cikin waɗanda suka ji ciwo har da Daddy don wani ƙarfe ne ya coke shi a cinya ya ɓullo ta ɗaya ɓarin cinyar abun babu kyaun gani.
Sai da ƴan road safety suka zo sannan aka fara zuba su a mota za'a bar wutin dasu don wurin da suka yi accident ɗin daji ne. Haka aka kwashe su aka yi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dasu a ɓangaren accident and emergency.
Kabir na kwance har ya fara bacci yaji wayarshi na ringing, haka ya tashi yana tsaki ya ɗauki wayar sai yaga ashe Daddy ne ke ƙiran shi. Cikin muryar bacci yace "Hello Daddy," sai yaji wata murya da ba ta Daddyn ba ta amsa. Ai tuni yaji ya wartsake jin wayar ba'a hannun Daddy ba, da ƙyar ya nutsu suka gaisa da mutumin sannan mutumin ya faɗa mishi maƙasudin kiranshi da yayi. Tuni hankalinshi ya tashi yana tambayar mutumin "Yanzu ina Daddyn? Da fatan dai bai ji ciwo ba?"
"Eh to, yana nan accident and emergency na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano idan kun zo zaku ganshi."
Hankali a tashe ya zari makullin motarshi ya fita, har ya isa harabar gidan ya tuna bai sanar da Mummy ba don haka ya koma yayi knocking a ƙofar ɗakinta. Cikin bacci taji ana ƙwanƙwasa mata ƙofa, sai da ta ɗauki wayarta ta duba lokaci sannan tace "kai waye anan?" Saboda har lokacin ba'a daina buga ƙofar ba.
"Mummy nine," jin muryar Kabir yasa ta duro daga gadon ta ɗauki hijabin sallarta ta saka sannan ta buɗe ƙofar tana cewa "Kabir lafiya kuwa yanzu da dare?" Idanunshi sun yi jawur saboda tashin hankalin yace "Yanzu aka kirani a waya wai an kai Daddy asibitin Aminu Kano sun yi accident a hanyarsu ta dawowa daga campaign, har na fita zan tafi na tuna ban faɗa miki ba shine na dawo."
Tuni itama ta rikice tace "Subhanallahi nima gani nan zuwa bari na shirya." Juyawa yayi ya tafi da kamar ya tsaya jiranta ta shirya ɗin kamar yadda tace sai kuma yaji ba zai iya ba gaba ɗaya hankalin shi yayi gaba gara yaje yaga a wane hali Daddyn yake ciki idan yaso ta iske shi a asibitin. Gudu kawai yake yi akan titi bare da titin ya kasance babu kowa saboda dare da ya fara yi babu yawaitar motoci a titun. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarasa asibitin, yana shiga cikin accident and emergency ɗin ya kira number Daddyn, mutumin na ɗauka yace mishi gashi yazo sai yana ɗan ɗaga hannu, daga nesa mutumin ya ganoshi yayi waving ɗin shi back. Da sauri Kabir ya ƙarasa wurinshi yana zuwa yace "Ya jikin Daddyn? Ina fata babu wata babbar matsala."
Hannunshi mutumin ya kamo yaja shi wajen kujera suka zauna yace "Mu ɗan jira su anan likitocin na dubashi har yanzu," hannu Kabir yasa ya riƙe kanshi yana jin tashin hankalin shi na ƙaruwa, a yanzu burinshi kawai yayi ido biyu da Daddy watakila idan ya ga a halin da yake ciki ya samu ƴar nutsuwar zuciya. Dafa shi mutumin nan yayi yace "Ka kwantar da hankalin ka In Sha Allah zai samu lafiya, kai dai kayi tayi mishi addu'a Allah ya sauƙaƙa mishi ya tashi kafaɗunshi."
Kasa ki amsawa Kabir yayi, suna zaune a wurin babu wanda ya fito wurin su har lokacin sallar asuba yayi suka tashi suka fita amsallacin cikin asibitin suka yi sallah suka dawo. Har wannan lokacin likitocin basu nemesu ba, gaba ɗaya Kabir ya ɗaga hankalinshi gani yake yi Daddyn ya mutu kawai faɗa mishi ne basa so suyi. Sai can wajen ƙarfe shida na safe sannan ɗaya daga cikin likitocin ya fito, mutumin na ganinshi ya gane shi don haka yayi wa Kabir magana suka tashi suka ƙarasa wurinshi. Yana ganin wannan mutumin daya kasance ɗaya daga cikin yaran Daddy na amana ya yafito su, kallon Kabir yayi yace "And who are you?"
Mutumin ne ya amsa mishi da "Mahaifin shi ne mara lafiyan ai."
"Oh okay, to ku biyo ni," yaja su zuwa wani office. Bayan sun zauna ya kalli Kabir "muna buƙatar kuyi signing akan wannan form ɗin don zamu shiga dashi surgery," ya miƙa mishi consent form. Karɓar takardar Kabir yayi yace "Ya jikin Daddyn? Meya sameshi da har sai anyi mishi aiki?" Ya tambayi likitan ba tare daya duba takardar ba.
Ɗan kallonshi Doctor ɗin yayi yace "Mahaifinka is diabetic gashi kuma ƙarfe ya shige cinyarshi ya ratattaka ƙashin wurin da ba zai gyaru ba don haka dole zamu yi amputating ƙafar don idan aka barta ruɓewa zata don ƙashin wurin ya tashi a aiki babu ta yadda za'a iya gyarawa."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun," kawai Kabir ke ambata, dafe kanshi da yake jin yana wani irin sara mishi yayi. Ya ɗauki wasu ƴan mintuna yana cikin halin ruɗani kafin da ƙyar ya iya buɗe baki yace "Yanzu ina Daddyn yake? Zan iya ganinshi?"
Cike da tausaywa suke kallonshi Doctor yace "Me zai hana, idan kun shirya muje ku ganshi sai kuyi ƙoƙarin biyan kuɗin aikin dan a samu a shiga dashi akan lokaci."