← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 168

Sashe 106

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*****
Har motar ta ɓacewa ganinshi bai daina bin hanyar da tayi da kallo ba. Wacece ita a wurin shi take tambayar shi, to wacce amsa zai bata? Zai fito ne ya faɗa mata gaskiyar matsayin da ya bata a cikin zuciyarshi ko kuwa zai ƙyaleta ne suci gaba da tafiya a yadda suke yi? Idan ya fallasa mata asirin zuciyarshi ba lallai ne ta amshi soyayyarshi ba don ido ba mudu ba yasan ƙima, ko ba'a faɗa mishi ba yasan daga babban gida ta fito, ko babu nakasa ita ɗin ba ajin shi ba ce to bare ga larurar dake tare dashi bayan haka bai manta da Junaid ba duk da taƙi amsa mishi shi yasan saurayinta, to ya isa yayi takara dashi a yadda yake ɗinnan? Yasan idan aka bata zaɓi tsakanin shi da Junaid dole shi zata zaɓa ta barshi saboda shine tsaran rayuwarta shine sa'an aurenta ba shi ɗan gidan Mallam Badaru da Umma Fatima ba. Kasa komawa cikin gidan yayi sai ya tafi can wajen da su Tanimu suke zama inda yake zuwa daa, bai samu Tanimu ba saboda yanzu akwai shagon da yake zuwa yana taya su ɗinki yace so yake yi hannunshi ya faɗa sosai kafin lokacin da Baqeer zai buɗe nashi shagon. Zama yayi cikin yaran da ya samu a wurin yana kallon duk abinda suke yi, tausayi yaran suke bashi don wasu a cikinsu basu fi shekaru biyar ba, yaran da basu wuce raino ba shine iyayensu suka tsige su daga jikinsu suka kawo su almajiranta babu ci babu sha kuma a haka suke iya bacci hankalinsu a kwance alhalin basu san a wane hali ƴaƴansu suke ciki ba, cikin ranshi yana ji inama shi wani mai faɗa aji ne da babu abinda zai hana bai daƙile kai yara garuruwa yawon almajiranta ba tunda in dai don karatu kowanne gari akwai makarantun allo me ya hana su barin yaran a kusa dasu idan har da gaske saboda karatun ake kai su ba don su yakice nauyin da Allah ya ɗora musu ba.
Bai bar wurin ba sai da aka yi kiran sallar magriba, daga nan wurin masallaci ya wuce bai koma gida ba sai da ya sallaci sallar isha'i sannan ya koma. Yana shiga gida Dada ta tare shi da tambayar inda ya shiga tun ɗazu bai dawo ba. Ɗan murmushi yayi yace "Dada ni yaro ne da don na fita na daɗe ban dawo ba duk zaki bi ki damu, ina can wajen dasu Tanimu suke zama daga nan kuma na wuce masallaci kin san kuma ina tsayawa ɗaukar karatu duk bayan sallar magriba zuwa isha'i, abinda ya hanani dawowa da wuri kenan."
Kwanukan abincin shi ta ajiye a gabanshi tace "Ni dai bana son daɗewar nan da kake yi a waje yadda rayuwar nan ta lalace babba ma ba tsira yayi ba bare yaro bare kai da ba lafiyar ƙafafu gareka ba." Jinjina kai yayi yace "To Dada In Sha Allah xan kiyaye," don yasan fa gaskiya ta faɗa mishi, yadda rayuwar nan ta lalace mutane ba abun yarda bane.

*****
Sai da tayi nisa sosai da barin unguwar sannan ta samu wuri tayi parking ta ɗora hannunta akan ƙirjinta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi kamar wacce zata fasa ƙirjinta ta fito. Ita kuwa yau me ya shiga kanta ne? Me ya kaita furtawa Baqeer waɗannan kalmomin? Yanzu da wane ido zata ƙara kallonshi saboda Allah bayan wannan abun kunyar data tafka, wai wacece ita a wurin shi, inndai ba abinda take fatan ji daga gareshi zata ji ba me ya kaita yi mishi wannan tambayar. Idanunta ne suka kai kan gift bag ɗin daya bata ta janyo ta buɗe ta fito da kayan ciki, turaren Arden beauty (Elizabeth Arden) daya sabar mata da fesawa don tun daga ranar farko da yayi mata kyauta dashi ta bar turaren da take amfani dashi ta komawa wannan, ajiye shi tayi a gefe ta fito da abayar ai bata san lokacin da ta furta kalmar "wow" ba don sosai abayar nan ta tafi da ita, tayi mata kyau sosai kuma daga texture na fabric ɗin tasan ba ƙananun kuɗi ta kwasa ba. Irin waɗannan gestures ɗin na Baqeer ke sawa take ganin shima yana sonta kamar yadda zuciyarta ta afu a soyayyar shi, to amma idan da gaske yana sonta me ya hana shi furta mata duk tsawon lokacin nan da suka ɗauka tare, bai taɓa tambayar wani abu a kanta ba, bai taɓa nuna son yasan wacece ita ba duk da tana tsoron ranar da zai gano ita wacece amma tana ganin idan har akwai wannan son a tsakaninsu sanin asalin wacece ita ba zai zamo matsala ga tarayyarsu ba. Haɗa kayan tayi ta mayar cikin gift bag ɗin sannan ta ɗauki wayarta ta tura mishi saƙon sms. "I wanted to let you know how much I love the gift you gave me. Your thoughtfulness truly touched my heart. Thank you." Ajiye wayar tayi bayan ta tabbatar message ɗin yayi delivering sannan ta tashi motarta ta bar wurin, wani irin mixed feelings take ji a tattare da ita, ɓangare ɗaya tana jin takaicin kanta na yadda take kasa iya controlling emotions ɗinta akan Baqeer har sai tayi wani abu da daga baya zata zo tana dana sani a ɗaya ɓangaren kuma tana jin shauƙi da ƙaunarshi na daɗa ratsa dukkanin wasu sassa na jikinta, ta rasa me zata yi da Baqeer zai fahimci halin da take ciki, tana so duk ranar da Daddy ya ƙara yi mata maganar Junaid ace tana da makamar dafawa amma idan bata san a wane matsayi ya ajiyeta ba bata isa ta tunkari Daddy da zancen shi ba. Har ta ƙarasa gida bata da cikakkiyar nutsuwar zuciya, gabanta ne ya faɗi da taga motar Daddy fake a harabar gidan, yaushe ya dawo? Tayi wa kanta tambayar da bata da amsarta. Jiki a sanyaye ta fito daga cikin motar har ta ɗauki gift bag ɗin zata shiga da ita gida sai tayi wani tunani don haka ta mayar da ita mota ta ajiye, tasan yanzu tana shiga ciki za'a fara yi mata tambayar daga ina take tunda ba wai ta faɗawa Mummy zata fita bane, to a yadda ta fita ta bar gidan ma ai bata jin akwai wanda zai lura da rashinta a gidan yadda duka mutanen gidan basa cikin walwala.
Har tayi hanyar ɗakinta don bata so kowa ya ganta bare asan dawowarta gidan sai ta fasa jin kamar hayaniya na tashi daga parlourn Daddy. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," tace haɗe da ɗora hannu aka ganin yadda Daddy yake dukan Kabir da wata sharɓeɓiyar dorina, a gefe ga Nabila a tsugune tana kuka sai Mummy dake tsaye hankalinta a tashe idanunta na tsiyayar da hawaye, tama kasa ƙarasawa kusa da Daddyn bare ta hanashi dukan da yake yiwa Kabir ɗin. A rikice Zainab tace "Daddy......"

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
        *DA
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BIYAR*

{65}
Chapter 106 · 0% Book details