← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 168

Sashe 82

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*****
A hankali Nabeela ta tura ƙofar ɗakin ta shiga cikin sanɗa kamar mai gudun kada wani ya ganta. Bata ganshi akan gado ba don haka ta hau jujjuyawa tana ƙarewa ɗakin kallo, motsin da taji daga banɗaki ne ya bata tabbacin yana ciki sai ta shige can cikin ƙuryar ɗakin inda kayan gadonshi suke ta kishingiɗe akan gadon tana danne-danne a wayarta. Bata daɗe da kwanciya ba sai gashi ya fito da towel ɗaure a ƙugunshi sai wani ɗan ƙarami a hannunshi da yake goge ruwan jikinshi dashi. Tana kallon duk abinda yake yi daga nan inda take sai dai ko motsi bata yi ba bare yasan da wanzuwarta a cikin ɗakin har ya gama shiryawa cikin wandon faded jeans baƙi da polo shirt kalar maroon. Sai sannan ta taso cikin rangwaɗa ta nufi gaban madubi inda yake duba tarin turarukanshi yana zaɓar wanda zai fesa. Yana ganinta ya haɗe rai tamkar bai taɓa dariya ba sai dai ko a jikinta ɓacin ranshi bai hanata nufarshi ba kamar yadda tayi niyya sai ma ɗaukar ɗaya daga cikin turarukan tayi ba tare data duba ko wanne bane ta rangwaɗar da kai gefe guda cikin wani irin salo na jan hankali tace "May I?" Bata jira jin ta bakinshi ba kawai sai ta hau fesa mishi turaren a dukkanin jikinshi, takaici ne ma yasa ya tsaya ƙiƙam kawai yana kallonta yana mamakin ƙarfin hali irin nata da bata jin duk jan kunnen da yake yi mata akan shigo mishi ɗaki. Kwalabar ta ajiye ta ɗora hannunta akan kirjinta tana yi mishi wata irin shafa da tasa ya kusa rasa nutsuwarshi, bai yi aune ba kawai sai jin saukar leɓunanta yayi akan nashi cikin wani tattausan kiss, duk rashin jin Kabir baya kule-kulen mata, barshi dai da son harkar chilling da clubbing amma sam babu ruwanshi da shiga sabgar mata shi yasa abun yazo mishi a bazata. Bai san lokacin da ya fara mayar mata da martanin kiss ɗin ba sai can kamar wanda aka yiwa raɗa cikin kanshi ya tuna wacece ita da matsayinta a wurinshi, da sauri ya hankaɗeta yayi baya ya bayar da tazara mai yawa a tsakaninsu ranshi a matuƙar ɓace da wannan rashin hankalin da tayi mishi. A fusace yana nunata da yatsa yace "Bana son iskanci fa Nabila wallahi idan baki fita sabgata ba zan yi miki rashin mutunci irin wanda baki taɓa tsammani ba, haba wannan wacce irin jaraba ce? Ana so dole ne ko an gaya miki kowa ma jaki ne dabba wanda baya aiki da tunani da zaki yi tunanin wani abu makamancin wannan zai taɓa shiga tsakaninmu, ko kin manta ke wacece a wurina da zaki dinga damuna da abin da kika san ba zai taɓa yiwuwa ba, to wallahi ki fita a hanyata kada ki ƙara shigo mini ɗaki idan ba haka ba duk wulaƙancin da nayi miki ke kika saya da kuɗin ki." Yayi tsaki kawai ya fice ya bar mata ɗakin don bama zai iya tsayawa ya jirata ta fita ba. Haka kawai shi da ɗakinshi da gidansu amma tana nema ta takura mishi, yanzu gaba ɗaya baya iya sakewa a cikin gidan don yana tsoron yadda take yawan shigar mishi ɗaki ba tare daya sani ba.

*****
Tana komawa gida ɗakinta ta wuce tayi sauri ta shiga wanka ta shirya a gurguje don sai bayan dawowarta sannan ta tuna ashe fa akwai inda zasu je ita da Mummy shaf ta manta saboda hankalinta daya bar jikinta tunda ta amsa ƙiran Baqeer tunaninta gaba ɗaya ya koma wajenshi, bata tashi tunawa ba sai data ɗaga wayarta don ta duba lokaci taci karo da tarin missed calls ɗin Mummy. Sassauƙar shiga tayi cikin pencil trouser da kaftan top data kai mata har wajen gwiwa, medium veil tayi rolling  a kanta ta ɗauki turaren wurin Baqeer tayi amfani dashi da tunda ya bata ta daina amfani da kowane turare idan bashi ba har gashi ma ya kusa ƙarewa. Sai data gama shirinta tsaf sannan ta fita zuwa ɗakin Mummy. Tana shiga Mummy tace mata "Ina kika shiga yau tun safe bayan kin san zamu fita kuma shine nayi ta kiranki a waya baki ɗauka ba?" Langaɓar da kanta tayi gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace "Ayya, i’m sorry Mum wallahi wani ɗan uzuri ne ya fitar dani kuma wayar tawa a silent take ban tashi ganin missed calls ɗinki ba sai da na kusa ƙarasowa gida, i'm sorry please bazan ƙara ba," ta ƙarashe maganar tana kama kunnuwanta duk cikin ban haƙurin.
Girgiza kai kawai Mummyn tayi tace "Idan ban haƙura ba ya zanyi dake Zeey, most a times nafi ganin laifin kaina don ni na sakar miki da yawa har haka shi yasa kike abubuwan ki babu shakkar abinda zai je yazo amma in banda haka bayan kin san Daddynku yana gari shine kika saka ƙafa kika fita tun safe ba tare da sanin kowa ba salon idan ya tambayi ina kike na rasa amsar bashi ko."

"Please mana Mum tunda nace kiyi haƙuri ba sai ki haƙura ba abar maganar, yanzu dai gani na shirya ko mun fasa fitar ne na tafi naje na kwanta?" Ta ƙarashe da tambayarta. "Hmm" kawai Mummy tace tana jin rashin daɗin yadda Zainab tayi mata magana sai dai kuma baza ta iya tsawatar mata ba don tana ganin ai har yanzu Zeey ɗin yarinya ce shi yasa bata tauna magana kafin ta faɗeta tasan data ƙara girma zata daina duk irin waɗannan abubuwan da bata so ɗin.

*****

Tun da ya samu aikin contract ɗinnan sai yake ganin bama lallai ne sai ya sayar da filinshi ba yana ganin a cikin abinda zasu bashi ya isa yayi amfani da kuɗin ya biya tailoring school ɗin da yake son shiga sai dai kuma har wasu kwanaki mutanen basu ƙara tuntuɓarshi ba don haka ma yake ganin kamar dama dai wasa da hankalinshi kawai suke son yi, gashi ƴan kuɗaɗen da suka rage mishi a account ma har sun ƙare shima Sani telan bai ƙara nemanshi ba duk da tabbacin daya samu daga wurin Zeey na yayi styles ɗin ɗinkunan daya karɓa a wurinshi har ma yayi wa wasu da yawa irinsu kenan dai yayi ciniki sosai da styles ɗin, yayi mamaki da har yanzu bai dawo ba don shi kanshi sai da ya leƙa shafin shi na IG ɗin yaga yadda yayi ɗinkunan sosai da yawan likes da comments ɗin daya samu na masu son yayi musu irin wannan ɗinkin. Har tsawon sati biyu mutanen nan basu ƙara nemanshi ba don haka yaga baya fa da wata dabara baya ga ya saka filinshi a kasuwa duk kuwa da a farko burinshi ya gina wurin ne, daya samu contract ɗinnan har ya fara murna don yana ganin ba lallai ne sai ya sayar da filin ba amma yanzu idan har yana son shiga tailoring school ɗinnan tofa lallai ne sai ya haƙura da filin nan duk kuwa da yadda yake son gina wurin saboda yadda tsarin wurin yayi mishi, unguwa ce da babu hayaniya tsarin wurin yafi kama da tsari irin na GRA shi yasa ma ya zaɓi sayen fili a wurin saboda irin waɗannan unguwannin na burgeshi yadda basu da cinkoso da hayaniya rayuwar babu ruwan wani da wani bare aje ana saka maka ido a al'amuran rayuwarka.

Waya ya ɗauka ya kira Salim ya faɗa mishi abinda ke faruwa da abinda yake so yazo suyi saboda a yanzu shine kamar manager ɗin shi baya komai sai da shawarar shi, da shi kaɗai ya yarda a halin yanzu don shine mutum ɗaya tilo da bai juya mishi baya ba bayan Ummanshi da ƙannenshi guda biyu Maryam da Hadiza sai ko Zainab da duk abinda ya zama a yanzu yake ganin ita ce sila, he will forever be indebted to her don tayi mishi abinda wani makusancin bai yi mishi ba a rayuwa...

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
       *Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
       *DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA ƊAYA*

{51}
Chapter 82 · 0% Book details