← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 168

Sashe 24

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*****
Baqeer a cikin ɗaki yayi shiru, Hadiza da Maryam duk sun kirashi sunji yanayin jikinshi, Salim ya kira a waya wanda ringing biyu ya ɗauka yace “Baqeer akwai abinda kake so ne?”
Wani abu ne ya ɗarsu a ranshi, Salim abokinshi ne tun na yarinta sai dai zuwan Bello unguwar da kuma yanayin karatunsu na Art yasa shaƙuwarsu tafi ƙarfi tun daga nan ya tattara Salim ya ajiye, in har ka ganshi da Salim to sai dai haɗuwar masallaci ko kuma a hanya su gaisa ya wuce. Jiki a sanyaye yace “A’a dama tambayarka zan yi kaji labarin Bello kuwa?”
Ajiyar zuciya yayi da alama bai so yin maganar ba kafin yace “Kayi hakuri Baqeer kasan na faɗa maka Habi taji suna waya da Asiya akan tafiyarshi, ashe gasa yaje ɗazu Habi ta kirani take sanar dani abinda ke faruwa da link ɗin BBC inda suka ɗaura labaran, abinda ya bamu mamaki me yasa yayi amfani da initials ɗinka kamar yadda kake yi a matsayin sunanka? Sannan yaushe sunanshi ya zama Muhammad Bello?”
Hannunshi dake riƙe da waya ya ɗan matse kaɗan zuciyarshi nayi mishi zafi, yace “Komai ta wurin Asiya ake ji kenan?”
“To ni Habi bansan meya faru ba amma…..”
Sai kuma yayi shiru, Baqeer yace “Amma me?”
“Babu komai kawai dai ban san meke damun Bello ba.”
“Wayar da Asiya take yi da Bello akwai alamar tambaya ne?” Tambayar da Baqeer ya daki Salim da ita kenan, haka kawai yaji ƙwaƙwalwarshi tana ayyana mishi abu, in har Asiya ta rabu dashi ta bar ɗaukan wayarshi taya zata cigaba da hulɗa da abokinshi wanda ta dalilinshi ta sanshi? Sannan ace duk wani abu daga wurinta ake fara ji?
Salim yayi wata ƙaramar shaƙuwa yace “Ni dai wallahi ban sani ba kawai Habi ce dai bata son wayar da suke yi.”
Kashe wayar kawai Baqeer yayi don bai san me ma zaice ba, zuciyarshi na sake ayyano mishi abubuwa da dama.

********
Duk wani kayan ciye-ciye an jerashi a parlourn, Mummy ta shigo ta tabbatar Zeey tayi shigar daya dace, Nabeela na zaune akan gado tana murmushi don tasan Zeey in har ta leƙa wuein Najib to tabbas sai ta kwafsa, kallonta Zeey tayi tace “Aunty Beela ina fa kallon yadda kike kallona tun ɗazu.”
Dariya tayi tana kallon Mummy tace “Ni dai bance komai ba kawai dai ina jiyewa ne garin gyara a ƙara ruguza abu.”
“To ke kuma da baza kiyi fatan alkairi ba sai kiyi shiru.” Mummy ta faɗa tana hararar Nabeela.
Mai aiki ce tayi knocking ta sanar da su zuwan Najib sannan tace suna falo tare da Kabir.

Koya kuke ganin zata kasance da Baqeer akan Bello? Ga dai Kamalu an tafi neman Zeey, ga kuma Najib yazo ganin Zeey.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#Shalele
#Zeey
#Kamalu
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD

https://www.arewabooks.com/chapter?id=656d9ccf22d5844413e4fa27

*BAQEER*
     *NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*ƘARSHEN ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BIYAR*

MUMMY ce ta sake riƙe hannunta tace “Kin san ina bayanki a koda yaushe ko?”
Cike da sanyin jiki ta kalli mahaifiyar tata kafin ta rungumeta tace “Mummy dole ne sai Daddy ya aurar dani ga wanda yake so?”
“Sai haƙuri kin san shi ɗan siyasa ne shi yasa yake son aurar dake ga wanda yasan zai taimaka mishi a harkar siyasar shi.” Ajiyar zuciya Zee ta sauƙe tace “Am sorry Mummy amma bazan taɓa auren wanda bana so ba.” Daga haka ta zare jikinta ta bar cikin ɗakin, jiki a sanyaye Mummy ta kalli Nabeela tace “Nabeela please banda ke akan me bazaki dinga ƙarfafa mata gwiwa ba? Ya kuke so tayi ne? In har bazaku fahimceta ba?”
Wani murmushin takaici Nabeela tayi tace “Yaya wannan abin da kuke wallahi ba so bane, nasan kinsha wahala kafin ki sameta amma wannan bai kai dalilin da zai sa ku sangartata ba, ku dinga barinta tana fitsarar data ga dama ba.”
Nan da nan fuskar Mummy ta canza tace “In ke kina kanwata kin faɗi haka na waje suce me?”
Kai kawai ta kauda gefe zuciyarta na takaicin yadda idanunsu suka rufe saboda son yarinyar nan suka manta sam da abinda ya kamata suyi, hatta Daddy da ake ganin yana da zafi a kanta sam ita bata gani tunda zafinshi baya wani ɗaukan lokaci, tasan suna son Zeey amma a kalla…..
“Ki wuce falon yanda in kinga zata faɗi ba daidai ba ki taimaka ki daidaita.” Kalaman Mummy ne suka katse mata tunaninta, mayafinta kawai tasa ta fita daga ɗakin.

****
Ƙafa ɗaya kan ɗaya Najib ya ɗaura yana girgizawa shi a dole ta ƙona mishi rai yana jira ta bashi hakuri. Zeey ce ta shigo hannunta ɗauke da tray na drinks da fruits da aka yanka mishi, taga mai aiki zata kawo ta amsa tace zata miƙa da kanta.
Mummy data fito daga ɗaki ganin haka yasa taji wani daɗi ta kalli Nabeela tace “Ɗan basu minti goma su biyu.”
Zeey da murmushi a fuskarta ta shiga sai dai tana sauke labulan ɗakin ta canza yanayin fuskarta, kallonshi tayi tace “J?”
Wani kallo ya zabga mata tayi mishi alama da kai tare da nuna mishi tiren hannunta, sake watsa mata wani kallo yayi sai dai ya rasa me yasa yake sake kallonta, kyaunta yake ƙara gani sama da na jiya da alama kayan dake jikinta ne ya sake fito da kyaun nata don sanye take da lace an mata ɗinkin doguwar riga irin straight gown ɗin nan tayi kyau sosai a cik,i ba tayi kwalliya ba don mai kawai ta shafa sai ƴar powder data goga a fuskarta amma sosai tayi kyau kamar wata ƴar tsana.
Yanda ta kalleshi ne yasa yaji kamar an sakashi dole sai gashi ya miƙe yazo inda take ya amshi tiren, ta nuna mishi table ɗin dake tsakiyar parlourn tace “Ajiye acan.”
Ajiyewar yayi sannan ya koma ya zauna ya ɗaure fuska tamau, bata ko bi ta kanshi ba ta ɗauki remote kawai yaga ta kunna tv tana kallo, sun fi kusan minti biyar ba wanda yake magana sai ita kawai da take kallon drama na Turkey a tv tana murmushi, Najib ya cika ya cika har bai san ɓacin ran dake damunshi ba don takaicinshi ma ko kallon inda yake bata kuma yi ba tunda ya zauna.
A kufule yace “Zainab wai ba hakuri aka ce ki bani mu daidaita kan mu ba?”
Waigowa tayi ta kalleshi tace “Ince me kenan?”
“Kice kayi hakuri nayi kuskure amma bazan ƙara ba.”
Kai ta jinjina tace “Perfect gashi nan ka faɗa ai ko akwai sauran abinda kake son ji?”
Wani huci yayi yace “Gashi nan na faɗa?”
Ta ɗaga kai tace “Ka faɗa mana ko bayan haka da ƙari?”
A wannan lokacin Najib ya gama kaiwa bango, ya miƙe a zuciye yana sakar mata wani mummunan kallo, kallonshi ta sake yi jin alamun ana kallonta tace “Oh! Ba dai har zaka wuce ba?”
Kasa magana yayi kawai yana kallonta, ƴan mata nawa ne suke binshi yana wulakantasu? Ƴan mata nawa ne yake disgasu saboda yanda suke rububin shi? Kamar shi Najib Guy ace mace tana neman maidashi shashasha?”
A fusace yayi hanyar ƙofa, Nabeela ce ta turo ƙofar jiki a sanyaye ta kalleshi, zata yi magana ya ɗaga mata hannu, Kabeer ne ya taho don dama yana ɗaki haka kawai jikinshi ke bashi rainin hankalin Zainab babu abinda baza tayi ba.
Cikin sauri ya ƙarasa wurinshi yace “Najib menene?”
Rasa abin faɗa yayi don a ganinshi  ƙasƙanci ne ma ya faɗi abinda tayi mishi kamar ya zubarwa da kanshi aji ne, a fusace yace “Ka tambayi ƙanwarka sannan bazan sake dawowa ba taje can ta nemi wanda yayi mata.”
Nabeela tace “Kayi hakuri Najeeb ba wai har ranta tayi ba……” Bai jira amsa ba ya wuce, Kabeer ne ya bishi a baya da sauri, ita kuma Nabeela ta shiga ciki.
Tana shiga ta ganta tana shan fruits ɗin da aka yankawa Najib tana kallo yanda kasan ba ma da ita ake abin ba, kasa magana tayi kawai ta juya tabar parlourn.
Chapter 24 · 0% Book details