Sashe 162
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kabir na gaba suna biye dashi a baya a haka suka ƙarasa parlourn na Daddyn. Sanda suka samu labarin rashin lafiyar Daddyn basu ɗauka yayi sanadin daya rasa wani ɓari na jikinshi ba, sai duk jikinsu yayi sanyi da yanayin da suka sameshi a ciki. Zama Salim yayi a ƙasa shi kuma Baqeer na daga kan wheelchair ɗin shi sai dai russunawa da yayi ya gaishe da Daddyn alamun girmanawa. Bayan sun gaisa yana tayi musu ƴan tambayoyi duk don su saki jikinsu ya kuma wanke kanshi daga abinda yayi musu wancan zuwan da suka yi gidan.
"Yanzu wacce sana'ar kake yi ko har yanzu paintings ɗin dai kake yi?" Ya tambayi Baqeer don fa duk son da Zainab take yi mishi ba zai ɗauketa ya bashi ba idan har baya da ƙwaƙwarar sana'a duk da ma dai yanayin shigar jikinshi bata yi kama dana mara aikin yi ba. Ya buɗe baki zai amsa mishi kenan Zainab ta shigo, wani kallo yayi mata ya sakar mata kyakkyawan murmushin da yasa ta kusa rasa nutsuwarta, ajiye tray ɗin data ɗora kayan tayi akan center table sannan ta juya zata bar parlourn sai dai kuma Daddy bai barta tayi hakan ba sai cewa da yayi ta dawo ta zauna. Daga ƙasa ta zauna a kusa da ƙafar Daddyn tana satar kallon Baqeer da shima ya kasa ɗauke idanunshi daga kanta.
Gyaran murya Daddy yayi abinda ya tunatar dashi a inda yake tuni ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana jin kunyar Daddyn na yadda ya kasa ɗauke idanunshi daga kan Zeey.
"A yanzu ɗinki nake yi ina da shagon ɗinki a Hotoro sannan muna shirin buɗe wasu barnches ɗin ɗaya a Zoo road ɗayan kuma a Gadon ƙaya," ya bawa Daddy amsar tambayarshi. Jinjina kai Daddyn yayi yace "yanzu a hakan kana iya ɗinki? I'm sorry fa kawai ina mamakin jin yadda kake iya yin ɗinki ne." Murmushi kawai yayi don bashi ne na farko daya fara yi mishi irin wannan tambayar ba, wanda ya ganshi akan wheelchair sai yayi mamakin ta yadda ake yake iya yin ɗinki.
"Yawanci kekunan namu electric ne wasu ma are computerized don haka aikin yana zuwa mana da sauƙi, a yanzu kuma da nake da ma'aikata ban fiye hawa keke ba sai dai nayi designing na kuma yi yanka su kuma sai su haɗe kayan."
"Masha Allah,” kawai Daddy yake cewa don he's really impressed da yadda Baqeer ɗin yayi mishi bayanin, lallai tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace babu nakasashe sai kasashe shi dai Baqeer gashi nan nakasa bata hana shi tashi ya nemi na kanshi ba abinda ya kamata ace mutane masu disability sun yi koyi dashi kenan su tashi su nemi na kansu sai a daina yi musu kallon ƙasƙantattun mutane.
"Wanda ya kaɗeka fa ko har yanzu ba'a sameshi ba?" Zeey ce tace "Daddy bakasan...." da sauri ya kalleta ya girgiza mata kai alamar a’a sai akai dace itama kallonshi take yi don haka tayi shiru ba tare data ƙarasa faɗar abinda tayi niyyar faɗa ba, shima Daddyn yaga lokacin daya girgiza mata kan sai ya ɗauke kanshi kamar bai gani ba.
"A'a ba'a sameshi ba, ni kam ma tuni na yafe mishi don tuni na karɓi ƙaddarata a yadda tazo min don haka ko tunawa ma bana yi." Ya bawa Daddyn amsar a nutse don a ganinshi babu wani amfanin faɗa mishi Kabir ne ya kaɗeshi bayan Kabir ɗin yayi nadamar abinda ya aikata har ma yaje ya nemi gafararshi sannan bayan tashin hankalin da suke ciki baisan ya ƙara musu wani, balle ko badan komai ba ko dan darajar Zainab ai da matsayinta a gunshi ya kamata a bar maganar. Shi dai Kabir har ya sha jinin jikinshi yayi kif da ido yanajin yanda abin zaizo, sai yaji shiru hakan yasa ya kalli Baqeer wanda kalamansa yasa ya ji zuciyarshi ta karye, girma da darajar Baqeer suka karu a idanshi, kai kawai ya sunkuyar bai iya cewa komai ba.
Sun daɗe tare da Daddyn bayan ya gama yi mishi duk wasu ƴan tambayoyi da ya dace yayi mishi sai yace ya bashi auren Zainab duk lokacin da ya shirya sai ya turo magabatan shi a tsayar da magana. Anan parlourn Daddy da Kabir suka fita suka basu wuri sai sannan ya ware ya kalli Zeey, sosai kwalliyarta tayi mishi kyau. Ɗage mata gira yayi yace "Amarya to ya? Kina ji dai Daddy yace ya bani ke ko yanzu na shirya nazo na ɗauke ki na mayar dake wurin Umma."
Rufe bakinta tayi tana dariya tace "la'ila, yaushe aka yi hakan ina zaune ban ji ba? Ko kuwa kai kaji Salim?"
Girgiza kanshi yayi yace “Ahh kaga mutum? To nima dai ban ji ba watakila kuma a mafarki yaji hakan yayi tunanin da gaske haka Daddy yace."
Harararshi Baqeer yayi yace "To ɗan baƙin ciki, tukunna ma waya sa da kai daka wani tsomo bakin ka, magana ake ta tsakanin miji da mata idan ka shiga ma kai zaka ji kunya."
Baki buɗe Salim yake kallon shi, ƙwafa yayi yace "gobe ma rana ce, ina zaune zaka zo ka sameni da wata buƙatar lokacin zaka san ni ka yiwa rashin mutunci."
"Ni ba akwai inda kace zaka ba? Don Allah tashi ka tafi zamu tattauna da Sweetums ɗita."
“Kai Ya Baqeer," Zeey tace tana dariyar faɗansu.
"Ai ki rabu dashi Zainab, nima zan rama ne ai." Da sauri Baqeer yace "sai dai ka rame," tashi Salim yayi zai bar wurin Baqeer yace "idan kaje kace ina gaida Habi don nasan duk baƙin ran nan da kake yi akan yau na hanaka zuwa wurinta ne." Da mamakin yadda aka yi ya sani Salim yake kallondhi, ɗan taɓe baki Salim ɗin yayi yace "Wai kai ka ɗauka duk abinda kake yi ban sani ba ne, ƙyaleka nayi ka gama ɓoye-ɓoyenka don dole dai akwai ranar da zaka sanar mini tunda ba'a ɓoye za'a yi auren ba." Kasa magana Salim yayi, da ƙyar ya iya cewa "Hmm taya za'a yi nace ina sonta bayan abinda ƴar uwarta tayi maka."
Katseshi Baqeer yayi da cewa "to miye a ciki don kana sonta, Habi ai ba Asiya bace besides that ni na daɗe da mantawa da wata Asiya a rayuwata bayan Allah yayi mini mafi kyakkyawan sakamako da my Sweetums to kuma me zai dame ni."
Wani murmushin farin ciki Zeey ta saki jin abinda ya cewa Salim, duk da tasan Baqeer yana sonta amma bata ɗauka son da yake yi mata ya kai girman haka ba.
Girgiza kanshi kawai yayi ya fita ba tare daya ƙara cewa komai ba, ba zai yiwu yaje wurin Habi a yanzu ba don tara ta wuce sai dai ko gobe kawai dai ya basu wuri ne don su tattauna shi yasa ya tashi ya fito.
Salim na fita Zeey ta kalli Baqeer a shagwaɓe tace "Ya Baqeer," sosai yaji ƙiran sunanshi da tayi ya ratsa shi. Ƙasa-ƙasa kawai ya kalleta ya girgiza kai don bata san yadda duk tayi mishi magana da wannan muryar tasirin da take yi a jikinshi ba. Cigaba tayi da cewa "Me yasa ka hana na faɗawa Daddy Ya Kabir ne ya kaɗeka?"
Da mamaki yace "Ke yanzu idan aka ƙyaleki sai kije kina faɗa, abinda ya riga ya wuce ai ba'a dawo dashi baya don haka ko ba Daddy ba please kada kije kina faɗa don ni ko Umma ban taɓa faɗawa ga wanda ya buge ni ba ko Baba ma hasashe ne kawai yake yi amma baya da tabbacin Kabir ne ko bashi bane ni kuma ba faɗa mishi zan yi ba don haka please a rufe wannan maganar kada a ƙara dawo da ita don tuni na yafe mishi tun ma kafin nasan ɗan uwanki ne shi."
Idanunta ne taji sun cika da ƙwalla, nauyin da ƙirjinta yayi tun ranar da tasan Kabir ne yayi sanadin gurguncewar Baqeer taji ya yaye tamkar an sauke mata wani gungumemen dutse da aka sa aka danne ƙirjinta dashi. Cikin rawar murya tace "Nagode Ya Baqeer."
"No, thank you, for believing in me even when I didn't believe in myself, for loving me the way I am despite all my flaws. Thank you for being there for me when I needed it the most, I don't know what I would have done without you. I will forever be grateful for having you in my life. I love you so much Sweetums."
Bata san lokacin data buɗi baki tace "I love You too Ya Baqeer, fatana har kullum Allah ya bar mu tare cikin aminci har ƙarshen rayuwarmu."
"Ameen Habibty," ya amsa mata yana jin wani irin shauƙin sonta yana ratsa duk wata jijiya dake harba jini zuwa zuciyarshi. Bai dan wane irin do yake yiwa Zainab ba abu ɗaya ya sani rayuwarshi is incomplete without her. Sun daɗe suna tattauna suna tsara yadda suke so bikin su ya kasance, ita tace tana son yin events shi kuma yace a'a dinner kawai zasu yi, ba zai hanata yin wasu events ɗin ba idan tana so amma shi dai dinner kawai zai je. Da ƙyar ta lallaɓa shi ya amince zai je mata kamu amma daga shi yace ba zai je komai ba to itan ma ta yarda babu jayayya tunda dai ta samu ya amince zai je kamu da dinner ɗin ai shikenan.
Da ƙyar suka iya rabuwa shima sai da Kabir ya leƙo yace mata Daddy yace ta shiga gida haka nan sannan suka haƙura suka yi sallama ya tafi bayan ta rakashi harabar gidan inda motarshi take, sai da taga fitarsu daga cikin gidan sannan ta koma ciki tana jinta kamar tana yawo akan gajimare don shauƙi.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336