Sashe 81
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
****
Yau Dada haka kawai ta tashi da ciwon ƙafa da take fama dashi da kuma ciwon hakarkari wanda yawanci ciwonta ne tana fama dasu dama lokaci-lokaci balle in sanyi yazo to fa dama sai tayi su kamar sau biyu ko uku, tun dare ta fara ji tasha magani amma bai tafi ba, kwance tayi a ɗaki sai dai hankalinta ne ya kai kan Baqeer tana ganin ya kamata fa yaci abinci, haka ta miƙe da ƙyar ta fito ta nufi ɗakin shi yana zaune yana zana riga da skirt na mace ɗinkin zuwa mishi yayi bayan yayi sallar asuba to baya son ya gudu daga kanshi ne yasa ya ɗauko don ya zana, shigowa tayi sai dai jiri ta fara ji yana neman kamata, a rikice ya taimaka mata ta zauna yana tambayar meke faruwa, Dada kam ido kawai take lumshewa da alama wannan karon bayan ciwukanta har da wani yanayi take ji a zuciyarta.
Baqeer idanunshi ne ya cicciko da yaga ya kasa bata wani gudunmawa daya kamata, asibiti ya kamata ayi da ita amma taya zai iya? Cikin sauri ya kira Salim sai dai wayarshi ma a kashe take, ya sake kira nan ma haka, ganin yadda Dada ke sake bin katifa yasa hankalinshi ƙara tashi yanzu in ya kira Umma ya tabbatar ba lallai ma Baba ya barta tazo ba, number Zeey ya kira sam ba tare da wani dogon nazari ba.
Zeey kuwa a lokacin Mummy bata daɗe da barinta a ɗaki tana bacci ba don akwai inda zasu je amma tace bacci take yi, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka cikin bacci tana neman maida ita silent don yanzu ma tsautsayi ne yasa tabar wayarta a ringing. Wayar ta kalla sosai ganin sunan dake jiki, da sauri ta ɗaga ganin zata katse.
Baqeer hankali a tashe yace “Please in kina available ki taimaka mu kai Dada asibiti! Am really sorry.” Ai bata tsaya nazari ba tace “Ganinan zuwa.” Dirowa tayi daga kan gado duk ta rikice hankalinta gaba daya baya jikinta, kayan barcin bata canza ba ta saka dogon hijabin sallarta wanda yake har ƙasa kawai ta fito, ko Mummy bata tambaya ba tayi waje ta shiga mota zuciyarta da tunaninta sam basa jikinta.
Meya samu Dada? Meya faru? Tambayar da take mata yawo kawai akai kenan. Baqeer kuwa kusa da Dada yayi, cikin nishi take ce mishi “Baqeer babu komai kar ka damu zai daidaita.”
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN*
{50}
Hankali a tashe Zainab ta ƙaraso gidan, ita ta taimakawa Dada ta sakata a mota Baqeer na biye dasu akan wheelchair ɗin shi sai sannu take zubawa Dada. Wani private clinic ta kai su don tasan idan suka tafi asibitin gwamnati sai sun bi dogon layi, zasu daɗe sosai kafin su samu ganin likita ita kuma a yadda take ganin yanayin jikin na Dada sai take jin ba zata iya kaita inda zata kusa yini bata samu ganin likita ba. Duk wani kai kawon buɗe folder da kama Dada su shiga ɗakin ganin likita duk Zainab ce tayi shi Baqeer nashi kawai ya bayar da kuɗin da aka nema shima don yaƙi yarda Zainab ta kashe musu ko sisinta yace ɗauko su da tayi ma ya wadatar. Sai sintiri take yi ta kasa zama wuri ɗaya don ganin an bawa Dada kulawar data dace. Bayan fitowarsu daga wajen likita ma ita ta tafi da takardar da aka rubutawa Dada magani taje ta sayo a pharmacy, duk inda tayi yana binta da kallo yana tunanin matsayin data taka a zuciyarshi, yana mamakin irin muhimmancin da ya bata don bayan Umma da ƴan uwanshi itace mace ta farko da zai iya neman wata alfarma a wurinta idan buƙatar hakan ta taso don yasan kome take yi zata ajiye tazo inda yake. Anan ya ƙara tabbatar da lallai ta samu babban matsayi a cikin zuciyarshi da bai san lokacin da hakan ya faru ba, babu wani abu da zai yi ya biyata ɗawainiyar da take yi dashi. Tana ta wannan kai kawon a cikin asibitin ashe Mummy nata kiranta a waya ta saka wayar a silent bata sani ba. Sai da aka gama komai har magunguna sun karɓa sannan suka bar asibitin lokacin wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a hanyarsu ta komawa sun zo daidai kan traffic ɗin kwanar sabo ta kalli masu sayar da fruits daga gefe sai ta juya ta kalleshi tace "Am Ya Baqeer." Juyowa yayi ya kalleta sai yaga ita ma shi take kallo wani irin kallo mai ƙoƙarin fallasa asirin dake binne a cikin zuciya, idanunshi ya zuba a cikin nata yana yi mata kallo kwatankwacin wanda take yi mishi, zuciyarshi har bugawa take yi fat-fat kamar zata faso ƙirjinshi ta fito. Wani ƙayataccen murmushin daya saka Zeey jinta tana yawo tamkar akan gajimare don daɗi ya sakar mata kafin ya janye idanunshi daga kanta yana ƙoƙarin danne abinda yake ji yana taso mishi a kanta. Sai da yayi gyaran murya don daidaita muryarshi kada ta gane halin da zuciyarshi take a ciki yace "Wani abu kike so?"
A daidai lokacin kuma motar dake bayansu ta danna wani uban horn da yasa Zeey ta firgita, sai lokacin ta lura ashe har an basu hannu motocin gabanta duk sun wuce bata sani ba. Jan motar tayi suka bar wurin sannan tace "Na'am." Ita ma tace tana basarwa kamar bata fahimci tambayar da yake yi ba, girgiza kanshi kawai yayi ya basar don yasan da gangan ta amsa shi a hakan. Lokaci bayan lokaci suke satar kallon juna suna jifan junansu da murmushi mai ratsa zuciya. Ita dai Zeey ta gama haƙiƙancewa ranta son shi take yi da gaske ba da wasa ba shine dai har yanzu take tantamar anya kuwa ta samu zuciyarshi kamar yadda yayi kaka gida a tata. Ita dai Dada tana kwance a bayan mota bata san wainar da suke toyawa ba har suka ƙaraso gida. Da taimakon Zainab Dada ta shiga cikin gida, bata zauna ba tayi mata sallama ta tafi sai data fita sai taga har lokacin yana cikin motar ashe. Fitowa tayi da wheelchair ɗin daga boot ta buɗe ta ajiye a gabanshi daidai yadda zai iya hawa. Da kulawa take kallonshi tace "Zaka iya kuwa, ko na samo wanda zai taimaka maka ka hau?" Girgiza kanshi kawai yayi sannan ya daddafa da ƙyar ya koma kan wheelchair ɗin, ita kuwa sai faman jera mishi sannu take yi kamar mai ciwo, sai taji gaba ɗaya ya bata tausayi kamar ta ɗauke larurar ta mayar jikinta haka take ji. Kasa tafiya tayi har sai da taga shigar shi cikin gida sannan taja motarta ta bar wurin tana jinjina yadda ta ɗauki al'amuranshi da girma haka, sam bata iya sukuni idan har ya buƙaci wani abu bata yi mishi ba.