Sashe 142
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Hankalinsu ne ya tashi ganin sun rasa hanya sai daji kawai suke gani, da shuke-shuke, nan da nan Zainab ta fashe da kuka. Kallonta Baqeer yayi cike da takaici taya suna cikin wannan hali zata fashe mishi da kuka, gaba yayi yana cewa in taga dama ta biyoshi da sauri in kuma ba haka ba zai yi tafiyarshi ya barta don ba zai je dare yayi musu a daji ba, ganin da gaske Baqeer tafiya zai yi yasa ta fara binshi a baya da gudu tana kuka, faɗuwa tai cikin kwacalin dake cikin dajin, nan ta ƙara saka kuka, shi kuma ya ɗauka kukan ɗazu ne dai take tayi har yanzu yasa bai tsaya ba yana tafe yana masifa yana cewa in ta gaji da kukan tayi shiru, ta barshi ma yasan yanda zai yi su bar dajin ba wai ta dameshi da kuka ba. Ya ɗan yi tafiya mai nisa kaɗan sai ya fahimci baya jin muryar kukan Zainab, da mamaki ya waigo sai dai bai ganta ba, hankalinshi ne ya ƙara tashi ya fara ƙwala mata kira sai dai babu ita babu muryarta, da gudu ya fara komawa sai dai da yake daji ne shi kanshi bai san ina yake yi ba, hawaye ya fara shima don hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba balle daya tuna laifin nashi ne. Zainab! Zainab! Kawai yake kira sai dai sam ya rasata, maimakon yaga inda zai ganta sai gashi ya hango titi, kuka ya saka ya fara tunanin zuwa ya nemo taimako wurin mutane. Sai dai shima titin ya gani amma bai gane unguwarsu ba, wurin wani mai shago yaje ya sanar dashi ƙanwarshi ta ɓata a cikin dajin nan, mamaki ya kama mai shagon yace kai yanzu me ya kawo ku daji? Sannan ka sani ita ko wani ya ɗauketa ta koma gida? Ka koma gida in kuka ga bata nan sai ku dawo a sake nemanta. Abunka da shima har yanzu yaro ne kuma yasan babu abinda zai iya, sai mai shagon nan ya taimaka mishi ya kai shi hanyar unguwarsu nan Baqeer yaga mutane carko-carko da alama anyi nemanshi har an gaji, da kuka ya kira sunan Badaru yace “Baba!” Hankali a tashe Badaru ya kalli inda yake a guje ya arto ya rungume Baqeer yana tambayarshi meya faru don kana kallon wandonshi duk kwacalin datti don kayan saukar tasu farare ne, kuka kawai Baqeer yake yi haka suka koma ciki, Kamalu ko kallonsu bai yi ba don shi har addu’a ma yayi akan Allah yasa a nemi Baqeer a rasa. Tunda suka shigo ciki Badaru ke bin ko ina na jikinshi da kallo sai daya tabbatar ba ciwo sannan hankalinshi ya kwanta, Umma ce ta kalleshi take ce mishi ance an gansu da Zainab don yayanta yazo tambaya ɗazu take cewa Baqeer baya nan. Hannun Badaru ya kamo yana cewa “Baba ka taimaka ku ɗauko Zainab ta ɓata a cikin dajin can.” Kallon mamaki Badaru yayi mishi yana tambayarshi dama tare suka fita? Ya ɗauka basa jituwa? Nan Baqeer ya sanar dasu abinda ya faru, hankalin Umma ne ya tashi ta ɗaga hannu zata zabgawa Baqeer mari da sauri Badaru yace kina marinshi ina rama mishi, laifinshi ne? Uban wa yace ta bishi? Sannan shima ba yaro bane?" Umma takaici ya rufeta tace “Kenan don yana yaro sai ya maida kanshi ɗan shekara biyar? Ba zai kama hannunta a matsayinshi na babba ba? Wannan ƙaton yaron ne za’a dinga mai dashi ɗan ƙarami? Wallahi wannan banzan hali ne kadai san Alhaji Sulaiman in har yaji ba bari zai yi ba.” A fusace Badaru ke cewa ba damuwarshi bane ai su suke barin ƴarsu na yawo. Ai bai gama rufe baki ba sai ga Bashir ya shigo da gudu yana sanar dashi ana sallama dashi a waje. Baqeer ya kalla yace ya tashi yaje yayi wanka yaci abinci yayi sallah sannan ya kalli Fatima yace wallahi ta dakeshi ta shirya ganin ɓacin ranshi.
Yana fitowa yaga Alhaji Sulaiman, yana kumfar baki yake tambayarshi inda Baqeer yake don ance mishi sun fita da Zainab. Badaru ya murtuke fuska yana cewa kaje can bayan gari ku nemo ƴarku don Baqeer yace can ya ganta tayi don haka kar ku kuskura ku ɗaurawa yarona laifi." Baki kawai Alhaji Sulaiman ya saki ai zuciya ta kawoshi ya cakumo wuyan Badaru yana cewa “Ka fito da ɗanka yazo ya kaini inda yata take ko kuma wallahi ku fuskanci ɓacin raina.” Ko me ya tuna sai kuma ya sakeshi ya juya da sauri ya shiga motarshi yayi wurin ƴan sanda anan aka baza mutane daji neman Zainab sannan ya kai ƙarar a kama Badaru da Baqeer akan ƴarshi da suka ɓatar, da yake Baqeer yaro ne sai suka kama Badaru aka makashi a cell ya dinga masifa yana iface-iface shi kam Baqeer banda kuka babu abinda yake yi, su Abu da Jamila abun ma dariya ya basu, suka shige ɗaki suna dariya da fatan Allah yasa ma a haɗa da Fatima a rufe. Tashin hankali mara misaltuwa suka fuskanta don har zuwa dare babu Zainab ba labarinta, haka Alhaji Sulaiman yasa aka kama Umma ita ma, da har su Abu yace suka ce wallahi su basu da wani haɗi da Baqeer don haka babu inda zasu.
Haka aka rufe su, cigiya har gidan radio, Mummy kam tasha kuka don har idanunta sun kumbura, a koda yaushe Daddy ya mata maganar haihuwa sai tace bata so ita wadannan biyun ma sun isheta, to yau ga shi ba Zee dole kowa ya shiga jajanta mata. Ranar basu taɓa ganin tashin hankali irinshi ba, duk wani bincike anyi amma babu Zainab, haka su Badaru da Umma suka kwana a cell shi kuwa Baqeer a gida Kamalu ganin ba kowa ya takale shi fada sai da yayi mishi duka ya huce haushin tsanar da yake mishi, su Abu na zaune suna kallonsu har sai da Kamalu ya fasawa Baqeer goshi sannan suka raba faɗan su Maryam da Hadiza sai kuka suke yi. Haka aka kwana cikin wannan tashin hankali wanda gidan biyu banda su Jamila da Abu babu wanda ya samu bacci, su kuwa bacci har da makara sallar asuba. Badaru kuwa a cell sai da Alhaji Sulaiman yasa officer yayi mishi duka wai akan interrogation ake mishi ya fito da inda yayi garkuwa da Zainab, don Alhaji Suleiman yace ramuwa yayi saboda ƴar tsamar dake tsakaninsu, haka aka yiwa Badaru jina jina, Umma kam hawaye kawai take yi tana addu’a akan Allah ya bayyana Zainab.
Washe gari wani masallaci suka sanar da asuba akan an tsinci yarinya ta kwana a gidan liman jiya tsakar dare wajen sha ɗaya, nan wasu suka sanar akan sun ji cigiya a gidan radio, haka aka sanar da gidan radio nan suka sanar ma Alhaji Sulaiman, tare suka taho da Mummy suka ɗauko Zainab wacce ke kwance saboda zazzabin daya rufeta har lokacin ajiyar zuciya kawai take yi. Alhaji Sulaiman har kwalla sai da yayi saboda tausayin ƴar shi, baƙin cikin abinda ya faru yasa aka ƙara wahalar da Badaru akan sai ya fito da Zainab, sannan suka ƙara barinshi yayi kwana ɗaya sannan suka sakeshi, tare da gargaɗin babu shi babu gidan Alhaji Sulaiman sannan yaransu ma babu su babu su. Baƙin cikin wannan abu da tashin hankalin da suka shiga yasa Alhaji Sulaiman hana Zainab fita ko makaranta taje ɗauko ta ake yi, sai dai har lokacin bata haƙura da Maryam ba, Mummy ta sanar dashi akan har lokacin bata daina wasa da Maryam ba, wannan dalilin yasa su barin unguwar, sai dai tsautsayi da rashin sani sai gasu sun sake haɗuwa a unguwa ɗaya na secondary school, ita Zainab nayi private ita kuma Maryam na government school kasancewar makarantun ba nisa yasa duk sanda suka tashi suke haɗuwa, wani sa’in sai sun fara hira sai su hango Baqeer yazo ɗaukan Maryam hakan zai sa Zainab ta gudu ta ɓuya. Bayan sun gama secondary school basu sake haɗuwa da Maryam ba sai a graduation ɗin da suka haɗu daga nan kuma sai dawowar da tayi daga makaranta.
Zainab nada kiba da sosai sai dai da ta girma ta sirance ta rame sai kyaunta ya ƙara fitowa.
Wannan kenan……..
*****
Har Zainab ta isa gida kuka take yi, tana shiga tun a harabar gida ta hango motoci biyu ɗaya na Junaid ne ɗayan kuma bata san na wanene ba. Shafar fuskarta tayi ta wuce ciki tana fatan yanda take jin ɓacin ran nan Allah dai yasa ba zancen banza Junaid zai yi mata ba. A falonsu taga Kabir a zaune ya haɗe hannayenshi yana ganinta ya taso da sauri yace “Zainab wurin Baqeer kika je? Me kika ce mishi?”
Wani banzan kallo tayi mishi kawai tayi hanyar ɗaki, gabanta yasha da sauri yace “Daddy yasa su Junaid da magabatanshi sun zo.” Yanayin kallonta ne ya canza tace “And?”
Ya girgiza kai alamar rashin sani kafin yace “Kin dai san halinshi am sure aurenki zasu yi fixing.” Kai ta jinjina tace “Damuwar su kai ma damuwarka,” tana kaiwa nan tayi ciki ta banko ƙofar ɗakin, komai baya yi mata daɗi a duniyar nan, Nabila, Kabir, Mummy da Daddy, bata san ta ina zata samu nutsuwa ba in dai ba a wurin Baqeer ba to yanzu shima ya rabu da ita tasan shikenan ita da farin ciki kuma kila har abada, kayanta kawai ta shiga watsowa daga wardrobe ta zuge akwati ta shiga zubasu a haka.
Tun daga abinda Nabila tayi musu take tunowa kawo yau, kawai kuka take yi tana haɗa kaya. Ƙofar ɗakin aka turo, Mummy ce cike da tausayi ta nufo zata rungumi Zainab, hannu ta nuna mata alamar ta dakata sannan tace “Enough Mummy please, a matsayin uwa kike a wurina kar ki bari raini ya shiga tsakanin mu.”
Kallon mamaki Mummy tayi mata tace “Me kike nufi auta.”
Wani murmushin takaici tayi tace “please Mummy zaki iya tuna cikakken halayenki?” Bata jira amsa ba ta cigaba “Tsabar fake smile am sure kin manta yaushe kika yi wanda ya kai har zuciyarki, hmm da alama dukan mu bamu da hankali shi yasa idon mu ya rufe muka kasa gane wacece ke, taya ɗanki zai buge mutum wanda da abu yazo da ajali zai iya mutuwa amma ki taya shi ɓoyewa ki koya mishi ƙaryar da zai yi kar a gane shi yayi? How?” Ta saki wani yaƙen takaici ta cigaba “Imagine? Baki tashi maganar ba sai da kika ga na taho? Ko ɗazu bamu haɗa ido dake ba kin kalli inda nake tsaye ta gefen ido don ni nasan naga sanda kika ganni ban farga ba sai da ina haɗa kayan nan nake dawo da komai, sannan ban taɓa sanar dake wanene wanda nake so ba ya aka yi kika san Baqeer ne? Abu ɗaya ne yazo min taya ba zaki sanshi ba bayan ke kin san Kabir ne ya gurguntashi? Sannan duk wani hint na riga na baki?” Ta ɗan yarfe hannu tace “Bayana? Auta ta? Kinsan yanda nake ji dake? Yan uwan mamanku? Mahaifiyarku?” Ta Ɗan sa dariyar takaici tace “Taya zamu zama wawaye haka? Sannan Nabila da kike nuna baki damu da ita ba magana ta gaskiya ba wanda ma kika damu dashi sama da ita, kin sata tayi karatun law abinda kika san burin Daddy kenan nayi, kin koya mata duk wani aikin da mace ya kamata ace ta iya, sannan duk wani haɗin aure da ake yi mini in bana so me kike cewa? In tura Nabila in bana so ni kuma na ɗauka so ne hakan sai na wulaƙantasu na tura ta, I haven’t realised miji mai kuɗi kike nema mata a fakaice.” Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Mummy wacce ke kallonta cikin yanayin da ba zaka taɓa ganewa ba, hannayenta ta haɗe alamar roƙo tace “Thank god basu yi min bane kuma ko ba Aunty Nabila ba zan iya tura koma wanene, sannan Baqeer da kike ta zugani a fakaice shi nake so, kuma ko duk duniya zasu haɗu shi ɗin dai shi nake so, ba kuɗi ne a gabana ba farin ciki ne a gabana da wanda zan zauna dashi cikin kwanciyar hankali, congratulations Mummy burinki ya cika, kin taimaka na mutu kan Baqeer kin kuma sanar dani Kabir ne ya buge shi, kin kuma zuga Daddy yaga Baqeer, menene next plan ɗinki?”
Kasa ko magana Mummy tayi sai kallon Zee kawai da take yi, ƙofar ɗakin aka yi knocking nan da nan Mummy ta nufi ƙofa ta buɗe ganin Daddy yasa tace “Senate! Ya zamu yi? Zainab barin gida take son yi yanzu nake yi mata faɗa sai dai bana ji zata ji.”
A fusace ya ƙarasa shigowa ciki, kawai Zee tasa wata dariya kamar mahaukaciya, tana yi hawaye na zubo mata tana bin Mummy da kallo.