← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 168

Sashe 66

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana barin wajen tela, Mariri ta nufa don taje ta nunawa Baqeer yadda style ɗin da ya zana mata yayi da aka ɗinka, wani irin farin ciki take ji a cikin ranta don tana ganin kamar duk wasu matsaltsalun Baqeer ɗin sun zo ƙarshe idan har ya karɓi tayin tailor nan don ta lura kamar yawan damuwarshi ta ta'allaƙa ne ga zanen da ya daina yi yanzu bayan a baya shine komai na rayuwarshi. Haka ta ɗin ga zuba gudu a titi don ta matsu taga ya reaction ɗin fuskarshi zai zama idan yaga ɗinkin. Wani ƙayataccen murmushi ta saki don tasan dole ne ma ɗinkin ya burgeshi kamar dai yadda yayi mata. Tana tsayawa a ƙofar gidan Dada ta sunkuci ledar kayan ta fice tana ji kamar tasa gudu ko zata ganta gabanshi, sai da ta shiga soron gidan sannan ta daidaita nutauwarta ta koma yin takunta a hankali ta shiga tana yin sallama kamar bata so. Daga cikin ɗaki Dada ta amsa tana cewa "Muryar wa nake ji kamar Zainabu?"
"Nice Dada" ta bata amsa tana nufar hanyar ɗakin. A zaune ta iske Dada tana shan kunun kanwa da aka aiko mata daga gidan maƙwabtan ta inda aka yi haihuwa. Zama tayi akan tabarma kusa da Dada tana gaisheta. Bayan sun gama gaisawa Dada ta tura mata kwanon kunun, girgiza kai Zeey tayi tace "Meye wannan ɗin Dada?"
"Kunun kanwa ne aka kawo mini daga maƙwabta anyi haihuwa.”
Ɗan yanutsa fuska tayi tace "Kunun gyaɗa kawai nake sha Dada ko kunun tsamiya bana so ko da azumi idan aka yi a gida sai dai na sha tea ko Mummy tasa ayi mini kunun gyaɗa." Mayar da kwanon kununta Dada tayi ta ajiye tace "Shima Baqeeru irin wannan tsirfar ce dashi komai aka yi sai yace baya so yanzu ne ma naga yana karɓar duk abinda na bashi ko baya so ya tsakuri kaɗan ya ajiye sauran."
Murmushi Zeey tayi tace "Ina yake nema Dada? Wurinshi nazo daga wurin tela nake nace bazan koma gida ba sai na kawo mishi ɗinkin daya zana mini ya gani yadda style ɗin ya fita sosai," ta zazzage kayan a gabanta tana ɗagawa Dada ta gani.
"La'ilahaillallahu" Dada tace tana tafa hannu, "Wannan ai irin ɗinkin da Baqeeru ya zana miki ne rannan sak kwabo da kwabo kamar hoton na takardar aka yi, amma ni ɗin kin ku ne sai naga kamar ƴar tsana za'a sawa."
Dariya tayi tace "Ke kuma Dada wace ƴar tsana? Kedai kice yayi tsaf zan shige cike."
Kai ta jinjina tace "Ni mamakin ma yanda yai ɗinki nake, ko ya akai ya iya zanashi haka?"
"Wallahi kuwa Dada, ai ko lokacin da nake kwatanta mishi ɗinkin ban ɗauka haka zai fita ba sai da ya zana naga ya fita fiye ma da yadda ni nayi tsammani."

Tashi Dada tayi da kayan a hannunta tace "Yana ɗakin shi yau tun safe bai leƙo waje ba ina ganin ƴan miskilancin ne suka motsa gama tunda ya gamu da larurar nan ya ɗauki miskilancin dole ya ƙaƙabawa kanshi, taso muje," ta cewa Zeey tana yin gaba. Tashi tayi tabi ta a baya sai dai suna zuwa ƙofar ɗakin taja ta tsaya a wurin taƙi ƙarasa wa ta shiga, sai Dada ce ta shiga ta sameshi a zaune da takardu a gabanshi yayi sketches na ɗinkuna da yawa tun daga kan riga da skirt har zuwa dogayen riguna. "Au ashe kace zane ka samu shi yasa yau naji ka shiru" Zeey ta jiyo Dada tana faɗa daga cikin ɗakin abinda yasa ta shiga ciki babu shiri don taga zanen da Dada ke cewa yayi, a karan farko kenan data taɓa shiga ɗakin.
Tsayawa tayi tana bin sketches ɗin da yayi da kallo tana mamakin irin styles ɗin daya fitar. A mamakance tace "Ya Baqeer dama ka iya zana ɗinkuna ko kuwa dai yanzu ne ka fara?" Ta sunkuya ta ɗauki takarda ɗaya tana kallon style ɗin doguwar rigar daya zana. Ai dole ne ma ayi mata wannan ɗinkin don sosai ya tafi da ita. Kallonshi tayi tana murmushi sai aka yi dace shima ita yake kallo yana ganin yadda annurin farin ciki ke fita daga fuskarta kawai don tazo ta iskeshi yana zane sai kace wacce aka yiwa wata gagarumar kyauta. Ɗan turo baki tayi gaba tana ayyana yadda murmushi yake ƙara mishi kyau amma kullum ka ganshi fuska a gimtse kamar bai taɓa dariya ba. "Ba shiryawa mukai ba ɗinki na fa nazo na nuna maka yadda yayi kyau sai nazo kuma na tarar kayi sketching waɗanda suka fishi kyau ma."
Sai sannan ya lura da kayan dake hannun Dada tana ɗaga mishi, sosai shima yaji mamakin yadda style ɗin ya fita. Yasan tun daa can yana da passion for ɗinki amma koda Zeey tace ya zana mata style ya dai jarraba ne kawai ba don ya ɗauka zai iya ba ganin ko normal zanenshi da yake yi ya jarraba yin su sau babu adadi amma kamar an share ƙwaƙwalwar shi ya kasaiyawa sai gashi a gwajin farko yayi zanen ɗinkin gashi kuma kamar an buɗe mishi ƙwaƙwalwa ne sai wasu zanen yake yi har ma ya fara tunanin jarraba zana ɗinkin maza.

Hannu ya miƙawa Dada ta bashi kayan ya ɗaga yana kalla sai kuma ya waiwaya ya kalli Zeey da ita ma shi take kallo. "Good!" yace mata a daƙile kama baya so, ita dai murmushi kawai tayi sai kuma ta janyo kujerar roba guda ɗaya dake ɗakin ta zauna. Dada dai ficewarta tayi ta bar musu ɗakin don haka suka kasance shiru kamar ba zasu yi magana ba. Zeey ce ta fara kawar da shirun ta hanyar cewa "Ya Baqeer sketches ɗinnan naka sun yi kyau sosai wallahi ko dai ka taɓa yin sana'ar ɗinki ne shi yasa abun bai baka wahala ba lokacin da nace ka zana min style?" Bai amsata ba sai cigaba da yayi da jujjuya kayanta da har yanzu suke hannunshi. "Shi kan shi tailor fa baka ga yadda ya yaba da ɗinkin ba don ma sai da nayi warning ɗin shi akan bana so ya ɗinkawa kowa watakila da yanzu style ɗin ya zama uniform."
Sai sannan yace mata "What's there in it don an yiwa wasu irin ɗinkin ki?" Taɓe baki tayi tace "Nop! Gaskiya ni dai bana so gara kowa yaje ya nemi style ɗin shi amma ba nawa ba."
"Umhm" kawai yace ya hau tattare takardun shi daya barbaza don dama a zaune yake akan katifarshi yana zanen don yafi jin daɗin yi a haka akan idan yana zaune akan wheelchair ɗin.
"Kasan wani abu Ya Baqeer" ɗagowa yayi ya kalleta sai ta cigaba da cewa "Tailor ɗin nema yace wai na haɗaku please ka ɗin ga yi mishi sketches ɗin yana biyanka to na dai ce mishi sai nayi magana da kai duk abinda ka yanke zan faɗa mishi amma ni sai nake ganin why not ka karɓi tayin shi tunda dama can sana'arka kenan yin paintings in a way wannan ɗin ma kamar yin painting ne tunda dai duk zane ne amma me kake gani?" Tun kafin ma yayi magana Dada ta shigo ɗakin tana cewa "Me zai hana kuwa yayi Zainabu tunda dama dai sana'arshi ce ai ki faɗa mishi kawai zai yi babu wani ja." Kallon Dada kawai yayi yana mamakinta yadda kawai ta yanke mishi hukunci ba tare data jira jin ta bakin shi ba. Ɗan waiwayawa yayi ya kalli Zeey sai yaga shi ta zubawa ido tana jiran jin amsar bakin shi. "I don't think if I will do it, mutanen yanzu basu da amana nafi so komai zan yi yanzu ya zamanto ban haɗa sabgata da kowa ba" yace yana ɗaga kafaɗa, tunanin Bello da abinda yayi mishi ne kawai ya faɗo a ranshi don haka yaji tayin da Zainab ɗin tayi mishi bai kwanta mishi ba. "Ba zaka yi ba fa kace Baqeeru? To idan baka yi wannan aikin ba me zaka yi tunda dai ba wata sana'a ka iya ba face zanen?"
"Zan je na koyi ɗinkin da kaina sai nake yi." Salati Dada tasa tana sallallami tace "Da wace ƙafar zaka taka keken ɗinki ki akwai keken guragu ban sani ba Zainabu?" Ta juya tana kallon Zeey. Dariya ce taso suɓuce mata sai dai yadda taga Baqeer ya haɗe fuska yasa ta haɗiye kayarta bata yi ba. "Akwai keken ɗinkin mai aiki da wuta ai Dada wannan baya buƙatar a takashi da ƙafa, zai iya yin ɗinkin bawani abu bane don yana da lalurar ƙafa kawai dai ina ganin Ya Baqeer ko na wani ɗan lokaci ne kayi aiki dashi in yaso daga baya idan ka koyi ɗinkin ka ƙware sai ka koma aikinka da kanka amma dai ya ka gani?"
Ɗan jim yayi yana tunani sai kuma yaga yanzu ko tailoring school ɗin zai shiga ai dole sai da kuɗi don haka yaga gara kawai yayi accepting tunda dai ma zanen kawai zai a saya a wurinshi ba wai tare zasu yi zanen ba kamar dai yadda suka yi da Bello don haka yace "Okay."

"Yayyy" tace tana ɗan tsallen murna jin cewa yayi accepting. Kallonta kawai yayi yana mamakin yadda take yin abubuwanta kamar wacce bata da wata damuwa a rayuwarta. "In Sha Allah gobe zan ɗauko shi na kawo shi sai kuyi magana har ma ya ga sketches ɗin da aka yi,” tace bayan ta gama tsalle-tsallen murnar da take yi....

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
Da
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA ƊAYA*

{41}
Chapter 66 · 0% Book details