Sashe 100
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Me yake faruwa ne Aunty Nabs? Ni sai yanzu ma na lura da wasu changes a jikinki. Garin yaya hakan ta faru ke da ma ba wani yawan fita kike yi ba ba kuma wani kike kulawa ba da sunan soyayya, ta yaya hakan ta faru saboda Allah, kuma kada kice min ba haka ba ne ko wasa kike yi don ba irin wannan maganar bace ake wasa da ita.” Ta tsurawa Nabila ido tana jiran jin amsa daga bakinta, ita sai yanzu ma ta lura taga duk ta ɗashe jikinta ya saki alamun dai lafiya bata wadaceta ba, to ita kuwa tana ina har Nabilan ta shiga cikin wannan halin bata sani ba, to wai shin ma wanene yayi wa Nabila haka ya keta alfarmarta don ita dai ta tabbata idan har da gaske cikin ne da ita to sai dai idan raping ɗinta aka yi don a sanin data yiwa Nabila babu ta yadda za'a yi ta kai kanta har ta yarda a keta alfarmarta da gangan. Ƙara kallon Nabila tayi sai taga itama kallonta take yi, tausayinta ne taji ya kamata ganin yadda lokaci guda gaba ɗaya ta canja, kamanninta sun sauya duk jikinta ya yamushe kamar wacce tayi sati jikinta bai ga ruwa ba. Wani irin kallo Zainab take yi mata cikin ranta tana ayyana 'kada dai ace' sai kuma tayi maza ta kawar da wannan tunanin. Har ta buɗe baki zata sake yi mata magana sai kuma taji ba zata iya ba don tunanin da tayi ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, fita kawai tayi daga ɗakin tana girgiza kai cikin ranta tana fatan kada Allah ya tabbatar da abinda zuciyarta ta saƙa mata yanzun nan.
*****
Duk wani abu da Bello ya bar mata sun tasarwa ƙarewa gashi shiru har ana neman wata biyu da tafiyarshi tata tafiyar bata samu ba, tun yana yi mata daɗin baki da alƙawura akan akwai wasu shirye-shirye da yake yi yana gamawa zai yi mata shirin tafiya ta iskeshi har yazo ya daina sai ma wayarta da ba koyaushe yake ɗauka ba sai tayi ta kiranshi bata samu idan kuma tayi dacen samun shi to ba lallai ne ta samu ya amsa ba. Yanzu ma wayarta ta ɗauka ta danna mishi kira don kayan abincinta sun tasarwa ƙarewa dama kuɗaɗen da ya bar mata tuni suka ƙare saboda sayi banza sayi wofi data riƙa yi dole ta haƙura take cin abincin da Habi take girka musu. Har wayar ta katse bai ɗauka ba sai data ƙara kira sannan ya ɗauka daf da zata katse murya a cunkushe. Tana jin muryarshi ta fara masifa akan don me tana ta kiranshi yaƙi ya ɗauka, yana lallashinta ma yana ƙoƙarin yi mata bayani taƙi tsayawa ta saurare shi har sai da yayi spark ya fara yi mata masifa abinda bai taɓa yi mata ba tunda suka fara soyayya don haka bata san lokacin da tayi shiru ba tana mamakin wai yau ita Bello yake yiwa tsawa “Enough haba wai ke uwata ce?” Abinda ya faɗa kenan wanda ya sakata jin ta kasa magana.
Shi ɗin ma ganin tayi shiru sai kuma ya sassauto yana cigaba da lallashinta akan akwai abinda yake shiryawa very soon itama zata biyoshi ta ƙara haƙuri kaɗan. A shagwaɓe tace "To ka turo mini wani abu mana kafin lokacin na faɗa maka kuɗaɗen hannuna fa duk sun ƙare.” Kwantar da murya yayi yana bata haƙuri akan har yanzu ba'a fara biyanshi ba shi yasa bai turo mata komai ba tunda ya tafi shine ma dalilin da yasa har yanzu bai samu ya kama musu gidan da zasu zauna ba amma ana biyanshi zai ƙarasa shirin tafiyarta taje ta iskeshi don sosai yake missing ɗinta. Murmushi kawai take saki tana sauraren yadda yake ƙara fasa mata kai yana bayyana mata yadda yake jinta a cikin ranshi, basu ajiye wayar ba sai da katinta ya ƙare.
Yana sauke wayar daga kunnenshi ya saki wani dogon tsaki, yanzu har fargabar ganin kiran wayarta yake yi don yasan rigima kawai zasu yi shi yasa a mafi yawan lokuta yake ƙin amsa kiran nata don ƙarairayin da yake yi mata har sun fara ƙarewa ya fara rasa ƙaryar da zai yi mata akan dalilin daya hanata tafiya tuntuni bayan a yadda suka tsara bai fi yayi sati uku zuwa wata ɗaya ba zata bishi. Tunda yaje basu fara yin abinda ya kai su ba sai da aka yi musu wata test wacce da ita ne za'a tantance matakin da za'a ajiye kowanne daga cikinsu a lokacin basu fi sati ɗaya da tafiya ba, a wannan lokacin ya gane ba shi da wayo domin duk wasu zane da yake yi ada da taimakon Baqeer yake yi bai taɓa yin zane nashi na kanshi shi kaɗai ba tare da taimakon Baqeer ba don ko waɗanda yayi presenting a wurin gasar da tun asali Baqeer shi ne ya kamata yaje yayi munaƙisar da shi ya tafi a madadinshi da taimakon Baqeer ɗin ya zana su shi yasa har ya samu yin nasara a wajen gasar da tayi mishi sanadin tahowa bunƙasa ilimin shi a harkar zane sai dai tun ba'a je ko ina ba suka koreshi daga makarantar don sun ce baya da wata fasaha a harkar a taƙaice ma basu yarda takardun zanen da suka saka shi yin nasarar nashi ne ba, tun daga wannan lokacin yake gararanba yana buga-bugar neman yadda zai yi ya samu aikin da zai riƙe shi ko na taƙaitaccen lokaci ne ko ya tara abinda zai ishe shi ya dawo gida ya kama wata sana'ar don dai duk ɗan abinda ya tara ya tafi ne wajen shiryawa Asiya biki na garari na ƴan ƙarya irin wanda za'a daɗe ba'a daina zancen shi ba, to gashi tun ba'a je ko ina ba ya fara ganin iyakar shi don zanen daya dogara dashi yake ganin shine zai zama silar arziƙinshi ya gane ashe shi ba komai bane a harkar idan har babu Baqeer a cikinta, a yanzu kuwa yasan ko giyar wake ya sha bai isa ya tunkari Baqeer da wani zancen daya danganci harkar zane ba bayan cin amana mafi muni da yayi mishi, ture batun auren Asiya da yayi bayan a irin son da yake yi mata da kuma tafiya wajen gasa a madadin shi tunda suka kai shi asibiti dama bai ƙara leƙa shi ba sai sau ɗaya shine kuma lokacin da yaji ƙaddarar data afka mishi yayi amfani da wannan damar ya tafi wajen gasar da yasan Baqeer ɗin yaci burin tafiya. A yadda abotarsu take da Baqeer yasan daya faɗa mishi cewar yana so yaje a maimakon shi tunda baya da lafiya wallahi ƙarfafa mishi gwiwa zai yi amma sai bai yi hakan ba ya zaɓi ya munafurce shi gashi abinda ya janyowa kanshi don yasan shi ba kowa bane idan har babu Baqeer. Baqeer ɗin da ya so shi da zuciya ɗaya ya aminta dashi ta inda bai ji ƙyashin koyar dashi duk wasu dabaru na sana'ar shi ta zane ba duk da ƙalubalen da yayi ta fuskanta daga wajen mahaifin shi akan baya son abotarsu amma ga da abinda ya saka mishi, tabbas bashi da kaico domin komai ya faru dashi shi ya janyowa kanshi.