Sashe 55
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waya Zeey ta yiwa Junaid ta sanar dashi ya shigo, ta fito ta wuce Baqeer tayi waje, kallon Dada yayi da mamakin kafin yace “Dada waye zai zo?”
Tace “Wallahi ban gama sani ba kai dai zai zo gani.”
Da mamaki yake sake kallonta yace “Baki san wa zai zo ba har zaki barshi ya shigo?”
Tace “To ba dai da Zainabu suke ba?”
Kallonta yayi lallai Dada bata san zamani ba, waigawa yayi waje ya hangosu suna tafe a tare fuskarsu ɗauke da fara’a, kallonsu yayi yanda suka dace da juna nan da nan yaji takaici ya kamashi, kallonshi ya sake yi tun daga sama har ƙasa to kai Baqeer babh ƙafa ma me kake tunani? Menene ma naka a ciki?
Wani abu ya haɗiya kamar zai koma sai yaji Dada tace “Baqeeru ina zaka? Bayan wurinka aka zo?”
Haɗa ido suka yi da saurayin kafin suka ƙaraso ciki, Zeey ce tace “Physiotherapist ne zai duba ka ne kafin kuyi making appointment kaje asibiti ya sake ganin taimakon da zasu iya yi maka.”
Hannu Junaid ya miƙawa Baqeer wanda shima ya miƙa mishi, dukkansu fuskarsu babu walwala, Junaid zuciyarshi cike take da son sanin wanene wannan da Zee duk ta damu dashi?
Hannunsu na riƙe da juna Junaid ya kalleta yace “Kamar gaske in kina magana da serious voice.”
Ta saki murmushi tace “Ban gane kamar gaske ba? Kai ma dai kasan in na canza yanda nake.”
Dada ce ta kalleshi ganinta yasa ya saki hannun Baqeer sannan ya rusuna ya gaisheta ta amsa fuska a sake sosai, nan suka shiga ciki Baqeer ya tura keke suka shiga sosai, kusa da Baqeer ya zauna sannan ya dan tsuguno yace “Sauƙe kafar daga kan keken muga.”
Baqeer yasa hann ya ɗaga cinyarsa sannan ya sauke, kallonshi yayi yace “Well done! Bari muga.”
Yayi maganar yana ɗan daga ƙafafunshi, Zeey da Dada dake tsaye suna kallonsu, ya ajiye ƙafar ya sake ɗaga ɗaya ƙafar, kallon Baqeer yayi yace “Zaka iya motsa yatsun ƙafafunka?”
Baqeer duk yanda ya gwada abun bai yiwu ba ya girgiza kai zuciyarshi na wani irin zafi. Junaid yace “Babu komai dama dai gwadawa ne ai, ya sake momotsa ƙafafun yanayi yana nazari, yace “Takardun da aka baka na asibiti suna nan?”
Yace “Dada takardun da Umma ta aiko dasu suna kusa?”
Da sauri ta wuce don ta ɗauko, Junaid ne ya dawo inda Zeey take yace “Me kike tunani?”
“Babu komai, ya kake gani?”
“Haka kika yarda dani?”
Murmushi tayi tace “Kaima ka sani ai.”
Kalaman da suke yi duk Baqeer na jinsu, wani abu ne yake ji yana tokare mishi maƙoshi wanda bai san ko menene ba, yawun bakinshi ya haɗiya yana mamakin abinda yake ji.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
#Baqeer🦼
#Zeey
#RayuwadaKaddara
#Hawayena
#Samudarashi
#UmmuAsgar
#Ayushermuhd
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA HUƊU*
{34}
Ya ɗauki wani lokaci yana duba takardun kafin ya ɗago kai ya kalli Baqeer yace "naga anan ance accident kayi shine cause na paraplegia ɗin ko?" Ɗaga kanshi kawai yayi alamun amsawa ba tare daya buɗe baki yayi magana ba don baka nan tsayuwar Zeey a kusa da saurayin ke saka mishi ɓacin ran da bai san dalili ba. Kallon Zainab Junaid yayi yana murmushi yace "In Sha Allah with proper care and treatment ko bai taka ba zai samu ya iya motsa ƙafafun da kanshi sai dai kuma kin san ciwo ke shiga farat ɗaya sauƙi sai hankali, ba wai daga fara session ɗin mu zai warke ba, it will take time before we can be able to see some changes". Daɗi ne ya kama Zeey jin cewa Baqeer ba zai dawwama a haka ba akwai yiwuwar ya warke, mutane su daina wulaƙanta shi saboda nakasar shi. "Thank you J, i really appreciate it" tace tana murmushi. Daɗi Junaid yaji yana ganin yayi wani abu daya faranta ran Zeey duk da bai san alaƙarta da patient ɗin ba, sanin wacece Zeey ɗin mai lafiya ma ba kowa take so ba bare nakasashe yasa yake danne abinda yaje ji yana mintsinin zuciyarshi akan Baqeer ɗin. Murmushin ya mayar mata shima yace "it's my pleasure".
Kallon Dada tayi tana yi mata bayanin abinda Junaid yace, itama sosai farin ciki ya kamata jin akwai yiwuwar warkewar Baqeer ɗin, sai ga Dada na share hawayen farin ciki don sosai take jin tausayin Baqeer da yadda mahaifinshi ya juya mishi baya saboda ƙaddarar data sameshi. "Da kanka ma zaka iya yin exercises ɗin zan nuna maka yadda zaka yi kana daga zaune da hannayenka, In Sha Allah with time komai zai zama tarihi amma sai kayi haƙuri ka sakawa ranka juriya don irin wannan abun is very tiring" Junaid yace yana kallonshi. Ciki-ciki ya amsa mishi da "to" don yana lura da wani irin kallo da yake jifan Zeey dashi wanda yake ƙara saka mishi nauyin zuciya, haka nan yaƙi jinin yaga Zeey ɗin a tsaye a gefenshi, shi sai yaga ma kamar yau tafi koyaushe fara'a saboda tana tare da saurayinta.
An ɗauki tsawon lokaci yana exercising mishi ƙafafun sannan ya nuna mishi yadda zai dinga mommotsa ƙafafun da hannayenshi yace "wannan exercise ɗin zai taimaka wajen tada jijoyoyin da suka mutu su koma aiki, Allah ya baka lafiya". Dada ce ta amsa da "Ameen" sai faman washe baki take yi tana saka mishi albarka daga shi har Zainab data kawo shi. Sun yi mata sallama suka tafi Zainab nace mata sai sun dawo ƙara dubashi don yace ba kullum zasu dinga yin treatment ɗin ba za'a na yin tsallaken kwana ɗaya idan anyi yau gobe ba za'a yi ba sai kuma jibi. Bayan fitarsu Dada ta kalleshi tace "Allah dai ya yanke maka wahala Baqeeru yasa a dace". A cikin zuciyarshi ya amsa da 'Ameen' don bai ji zai iya buɗe baki yayi mata magana ba saboda hatta ita haushinta yake ji ganin yadda take ta wani nan-nan da Junaid.
*****
Yau ta tashi ɗakinta babu komai ko ƙwayar shinkafar da zata dafa babu, ƴan kuɗaɗen da ta samo wurin Umma tuni suka ƙare. Kallon ɗakinta tayi tana tunanin abinda zata ɗaga ta sayar ta samu ta saya musu abinci, ita yunwar cikinta ba damunta ma take yi ba don idan da sabo zata iya cewa har ta saba da ita to amma yaran fa ya zata yi dasu su da basu san babu ba. Fitowa tayi tsakar gida ta kalli uwargidanta dake tsugunne a gaban murhu tana girki. "Sannu da aiki Maman Aisha" ɗagowa tayi ta kalleta ta watsar don tasan wani abun zata tambayeta ganin yau tunda ta tashi bata ɗora sanwa ba tasan bata da komai ne ita kuwa kayan abincinta nata ne da ƴaƴanta ba zata iya ɗauka tayi neman suna ba alhalin itama nema take yi. Duk da taga kallon wulaƙancin da tayi mata sai tayi kamar bata gani ba tace "don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Wallahi yau na tashi bani da komai ga yara sun kusa dawowa daga makaranta bani da abinda zan basu". Mafici ta ɗauka ma ta hau fifita wutar girkin da take yi tayi kamar bata ji abinda Hadizan tace ba. Duk da taji haushin ƙyaletan da tayi bayan tasan sarai taji ta tsabar wulaƙancinta ne ya tashi amma sai ta haɗiye fushinta tunda tasan idan ba wurinta ba bata da inda zata je ta samu, idan ma tace ta tafi gida wajen Umma kafin ta ƙarasa ma yaran sun dawo gashi haka nan ta turasu makarantar ko ɗan kokon ma yau basu samu ba. Kwantar da murya tayi tace "don Allah Maman Aisha kiyi haƙuri ki bani aron wallahi ba zanyi miki wasa da kuɗinki ba zan baki". A fusace ta ɗago tana nunata da yatsa tace "bafa na son rainin da kike neman kawo mini Hadiza, da can ni nake baki abincin da zaki nemi ki takura mini ko kuwa ni na ajiye ki, ha'an haka kurum mace baki san ki tashi ki nemi na kanki ba sai dai a ɗauko kina daga kwance a baki idan ya ƙare ki nemi takura mini kamar nj na ajiye ki".
Kamar tayi kuka haka take ji sai dai bata da yadda zata yi don haka ta ƙara cewa "kiyi haƙuri don Allah wallahi zan baki". Tsaki taja ta juya ta cigaba da aikin girkinta tana barta anan a tsaye tana jin takaicin rashin tashi ta nemi na kanta tun da gatanta sai kawai tayi kwance duk wata Ya Baqeer na ajiye mata kayan abinci don haka bata da wata damuwa a lokacin gashi yanzu tazo abincin da zasu ci ita da ƴaƴanta na neman yafi ƙarfinsu, shi dama maigidanta babu abinda ya dameshi idan yayi ficewarshi tun safe baya ƙara waiwayarsu sai lokacin kwanciya bacci yayi acan inda yake fita yake cin abinci don haka bai damu da ko suci ko kada suci ba.