← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 168

Sashe 92

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Tunda Badaru ya shige ɗaki abun duniya ya taru yayi mishi yawa, ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi yaji daɗi. Yana ji yana gani duk wani buri nashi na rayuwa ya wargaje, dama akan Baqeer yake da hope to gashi shima abinda yayi mishi yayi watsi da duk wasu sadaukarwa nashi yayi fatali da burinshi ya watsa mishi ƙasa a ido yana ji yana gani yayi bankwana da tsohon burin daya gina rayuwarahi akai. Tashi yayi yana zagayen ɗakin ya kai gwauro ya kai mari ya rasa abinda ke yi mishi daɗi, yadda al'amuranshi suke ta cakalkalewa shi yafi damunshi gashi yanzu kasuwar ma sai asara kawai yake tafkawa, ya rasa ta inda kuɗaɗenshi suke ƙarewa sai kaɗar da dukiyarshi yake yi yana ƙara jari amma da ƙyar yake iya haɗa uwar kuɗin bare a fitar da riba. To ko dai filin Baqeer zai saka a kasuwa ya ƙara jarin tunda ma ai shi yayi ta wahala da Baqeer ɗin har ya zama abinda ya zama da yayi mishi sanadin mallakar filin, wani murmushi ya saki da yin wannan tunanin don yasan idan har aka sayi filin da daraja ba ƙaramin alkhairi zai samu a ciki ba in yaso sai ya ƙara jarin ya tashi kasuwancin shi abinda yayi ragowa kuma sai ya buɗe shago a ƙofar gida ya zuba kayan masarufi.
Tashi yayi ya janyo jakar da yake ajiye duk wasu muhimman abubuwa nashi, zama yayi dirshan a ƙasan ɗakin ya buɗe jakar yana yi mata filla-filla yana neman takardar filin da yasan ba nashi bane. Hankalinshi ne ya fara tashi da yaga har ya kusa gama fitar da kayan cikin jakar bai ga takardar ba. Jiki na rawa ya cigaba da dubawa amma har ya gama bai ganta ba, zazzage jakar yayi a ƙasa ya fitar da komai amma bai ganta ba. Ai tuni hankalinshi ya tashi ya dinga bin takardun nan ɗaya bayan ɗaya yana ƙara dubasu amma bai ga takarda mai kama da wacce yake nema ba. A sukwane ya tashi ya fita daga ɗakin har yana tuntuɓe da dokin ƙofa ya fita yana ƙwalawa Kamalu kira.
Ai ba Kamalu da ake yiwa kiran mafarauta ba kowa a gidan sai da ya fito idan ka cire Umma da bata shiga sabgarsu idan har ba an saka da ita ba. Gaba ɗaya suka tsaya cirko-cirko suna kallonshi, yana ganin Kamalu yaje ya cakumi wuyan rigarshi yana cewa "Wallahi ƙaryarka tasha ƙarya, duk inda ka kai mini takardar filin nan sai ka fito da ita don wallahi bazan ɗauki asara ba." Kici-kicin ƙwace wuyan rigarshi yake yi amma ya kasa don ba ƙaramin ruƙo Badaru yayi mishi ba, sai da Abu taga yana neman halakar mata da yaro ta taso ta ɓamɓare hannunshi da ƙyar tana cewa "Haba Mallam kashe shi zaka yi ne?"
"Ki rabu dani na kashe ɗan iskan yaron nan wanda babu abunda ya sani sai shaye-shayen banza da wofi, wallahi Kamalu ka fito min da takardun filina idan ba haka ba kotu zan maka ka don bazan kamunta ba ka kasheni tun kwanana bai ƙare ba,"
Da ƙarfi Kamalu ya ture Badaru jin shakar dayamai yasa numfashinsa ya fara sarƙewa, Badaru baya yai sai kuwa ya bugi bango, ihu ya kwalla jin wani uban zafi ya ziyarce shi a kugunshi, Kamalu a tsorace ya kalleshi yana sauke numfashi, su Abu da Jamila kuwa sunyi kanshi, Jamila ce ta saki salati cike da ƙara tace "Wannan ɗa lalai anyi haihuwaf asara, kashe shi kake sanyi? Inalilahi yau naga abinda yafi ƙarfina Malam, sannu."
Badaru da kyar ta taimaka mai ya miƙe yana rike da kwankwaso, Kamalu da sauri yai waje dan Abu ce tamai alama da yai maza ya fita daga gidan, gaba ɗaya Badaru dakyar yake tafiya ji yake kamar ya gurɗe kugunshi, magana kuwa ya kasa yinta saboda uban azabar dake ratsashi, ɗaki Jamila ta kaishi ya kwanta tana mai tausa, wai yau kamar shi danshi zai hankaɗe? Lalai gobe in ya warke dole ya sallami Abu ta koma kauye, matsala ɗaya ƴar uwarsa ce yanzu tana tafiya mutanen kauye zasu isheshi da zirga zirga sai dai dole ta tafi daga ita har ɗanta, Fatima kam tunda ta fito taga abinda ya faru ta koma ciki, ita yanzu zaman gidan kawai yinshi take dan ba yanda zatai dan babu wani abu dake burgeta a ciki. Ranar duk yanda yai bai samu bacci ya daukeshi ba, filinshi kawai yake tunani, ga azabar ciwo da yake ji, wajen asuba ma da gyangyadi ya daukeshi yai mafarkin wai Kamalu ya saida filin ya cinye kuɗin firgigit yai ya farka, hankali a tashe ya yai dafa kirjinshi dake mai nauyi, lalai Kamalu dole ya bar mai gida dan ya tabbatar wannan tsaf zai nakasa shi.

******
   Baqeer kam komai Alhamdulila dan ya turawa mutanen nan zane nan kai tsaye sukace komai yayi akan zasu turo mai kuɗi, sunyi mamakin kwarewarshi dan shi kanshi yanzu yasan kwarewarshi tafi ta da saboda karatun da yake yi yanzu, yanka kuwa inya maka shi lalai sai ka dauka wanda ya shekara biyar yana ɗinki ne, haryanzu dai matsalarshi ɗaya itace ta taka keken ɗinki wanda Tanimu ke taimaka mai suma makarantar basu damu ba saboda su kansu mamakin kwarewarshi a yanka da fitar da styles suke, yau suna tasowa yai tunanin wucewa asibitin Junaid dan yanada appointment da physio ɗin dake taimaka mai, da yamma wajen hudu suka isa anan unguwar sukai sallah sannan suka ƙarasa shi da Tanimu suna tafe ba wanda yakewa wani magana dan Baqeer ba kasafai yake zance ba shi kuma Tanimu bai fiya san damunshi da hira ba, wannan dalilin ne yasa zamansu ya ƙara kwari, a bakin gate ɗin suna shiga ya canza yanayin fuskarsa sakamakon motar Zee daya gani, bayan yau kwana biyu kenan bai sata a idanshi ba amma shine zai ganta gun saurayinta? Fuskarnan tasa ta sake murtukewa da yaso ma yace su juya ya fasa dole ma ya shiga ya nuna ya ganta. Kasan ranshi ne ya tambayeshi to in ka ganta sai akai me? Auranka ne akanta ko kuwa soyayya kuke? Bai gama tunani ba yaji Tanimu na cemai "Ya Baqeer mukaje wancan satin zamu?" Kallanshi yai wani abu na sake tasomai yana bin office din Junaid da kallo, kawai ya fara tura kekenshi zuwa office ɗin Junaid sai daya kusa isa aka budo ƙofar office ɗin da sauri ya fara neman shan kwana, ganin haka yasa Tanimu ya taimaka mai, dariyar Zee ya fara juyowa tana cewa "Kai dai wallahi baka rabuwa da neman magana, nidai Allah na faɗa ma kasan yanda zakai ka dai san halina ba mai tilastamin in banyi niyyar abu ba," ta ƙarasa maganar tana kallan Tanimu, kai taɗan karkatar Junaid ne yace "Hmm ina mamakin yanda bakya tunanin halin da zan shiga kike faɗar abinda ke ranki, ki koma mu gama magana please bansan saurin me kike ba." Ganin yanayinta yasa yasan batama san me yake cewa ba, hakan yasa ya tsaya gurum yana kallanta, Baqeer jin kalaman Junaid yasa ya cigaba da tura kekensa, Tanimu na biye dashi, itama Zeey bayansu tabi tana tafe tana murmushi, Tanimu ne ya kalleta cike da jin daɗi ya gaisheta, tana murmushi ta amsa tace "Kanin Ya Baqeer ashe kuna hanya?" Tai maganar tana kallan bayan Baqeer, tsayawa da tura keken yai yanajin yana san ganinta amma kishi ya hanashi, Junaid kuwa cike da takaici ya biyota dan shi ya tsani yaga tanaba gurgun nan mahimmanci, ganin Baqeer baice komai ba ya cigaba da tafiyarsa itama yasa ta kalli Tanimu tace "Daga makaranta?" Kai ya ɗaga sannan yace "Ko gida bamu koma ba." Ta jinjina kai tana cewa "Shi kuma yayan naka yau bayajin yin magana ne?"
Junaid yai saurin cewa "Malam Baqeer ashe kana tafe, muje yau ni zan dubaka ma." Kallanshi Baqeer yai sai a lokacin idanunsa suka haɗu dana Zainab, da sauri ya ɗauke idanshi, mamaki ya ƙara kamata ganin ko jiya sunyi waya menene hakan? Me kuma ya faru? Haka sukabi Junaid nan ya dinga sashi yin exercises kala, kala yana ɗan taimaka mai, suna gamawa ya kalli Zeey yace "Paper towel please kiga harna haɗa gumi." Daukowa tai ta mikamai, idanunta nakan Baqeer da ko kallanta yakiyi, wato shi bataga gumin da yakeyi ba shima? Saurayinta kawai ta sani? Kallan Junaid yai yace "Mungode sosai!"
"No karka damu, Allah ya kara sauki it seems like kana abubuwan daya kamata am sure we will get there." Kai ya jinjina kawai ya tura kekensa, Zee ta mike zata bishi yaji Junaid yace "Zeey yauwa tunda kin dawo bari ma na nuna miki abu, da na ɗauka sauri kike ashe baki gaji da ganina ba." Waigowa Baqeer yai idanunsa na kanta, kishi yake? San gwadashi taji tanayi tace "J kaima kasan anything for you, nunamin." Idanun Baqeer ne sukai jaa wani abu yaji ya tokareshi, kallan Tanimu yai yamai alama kawai su fita, da kallo ta bishi suna fita ta kalli Junaid tace "Bye."
Hannu yasa ya riko hannunta da sauri yace "Zeey wai meke damunki? Menene tsakaninki da gurguncan? Kedai nasan kinfi ƙarfin gurgu shiyasa nake ta ƙoƙarin ganin na cire shirman tunanin nan a raina but yanda kike be having akanshi yana tsoratani."
Hannunta daya rike ta kalla wanda hakan ya sashi sakinta tace "J karka sa alaka ta zumincin dake tsakanina dakai ta kare, sannan kalamanka duka ka jira amsar da zan baka a kansu for now banda lokacin ka." Tana kai nan ta juya ta fita, ranta a ɓace tana jin kalaman daya Baqeer ma sunfi wanda ya mata ɓata mata rai.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
Chapter 92 · 0% Book details