Sashe 155
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna ce ta kalli Mummy cike da mamaki tace “Kina nufin hatsari yayi amma baki ma san halin da yake ciki ba? Sannan kizo kice min umara zaki? Wani irin ibada ne wannan Halima?” Murmushi tayi tana kallon Inna kai kace ba faɗa ake mata ba tace “Inna kenan, to ni in na zauna acan ma me zan yi mishi, gwara naje nayi mana addu'a kila Allah ya sassauta, ni ban san me yasa ba na gaji da murmushin ƙarya da nake yi sai nake ji yanzu komai ya isa bazan iya ba bare jinya.” Cike da takaici Inna ke mata wani kallo kafin ta ajiye kulun da take saƙa tace “To wallahi wannan karan ba dani ba, wani irin mugun hali ne wannan? Mutumin daya riƙe mu hannu bibbiyu kika rabashi da matarshi, kika sa ya dinga biya ma ƴar ki kudin makaranta ba tare da saninshi ba har ta zama abinda ta zama yanzu sannan kice baza ki iya jinyarshi ba?” Ganin yadda Inna take faɗa yasa tace “Inna don Allah kinga karki kawo min ƙabali da ba’adi, sanda nasa aka maida ke Hajiya ai baki ce mun haka ba.” Baki kawai Inna ta buɗe tana mamakin kalaman da Mummy ke furta mata, muryar Nabila ce ta katse mata tunani da cewa “Ai ba ita tace ki maidata Hajiyan ba, sannan in ma maidata Hajiyan ne ai da badon ita ba kema baki isa ki zama ba,” ta ƙarasa maganar cike da tsiwa da takaicin kalaman Mummy. Miƙewa Mummy tayi fuskarta a murtuke don har mayafin kafaɗarta na faɗuwa tace “Nabila how dare you?” Kanta tsaye tace “Ke da kike faɗawa Inna baki yi tunanin zata ji zafi ba? Ko kuwa mu muka saka kije kiyi yawon banza har ki same…….” Marin da Mummy ta zabga mata ne yasa ta yin shiru sai waigowa da tayi tana mata wani kallon raini, jikin Mummy har wani rawa yake yi saboda mamakin abinda take ji, Nabila? Yarinyar da akanta tayi komai saboda tana so ta bata rayuwa mai kyau? Duk da tsanar da tayi mata saboda tsautsayin daya faɗa mata a can ƙasan ranta tana son taga ta zama wani abun ba tare da gori ba. Bazata taɓa mantawa ba tana makarantar da tayi diploma ranar da suka yi graduation suna ta murnar gama makaranta, to saurayin da take so malamin makarantar ne, yace tazo suyi magana kafin ta tafi gida, haka ta sulale ta gudu wurin shi ba tare da ta sanar da su Inna da suka zo mata taron ba, lokacin tana ji da rawar kai, matan babansu biyu Inna da Dada, ita Dada tana da yara da yawa ita kuma Inna duk inta haihu sai ɗan ya koma sai data yi haihuwa shida sannan Allah ya bar mata Halima, shi yasa ta ɗauki son duniya ta ɗaura mata, ita kuma ta taso cike da rashin kunya don bata ganin kowa da gashi sai Innarta, gata ta iya yiwa maza wayau don su bata kuɗi bawai don tana sonsu ba, wani sa’in haka zata kira a rikice wai zata asibiti kai Babanta sai sun turo kuɗin ta cinye, to shi wannan Malamin da gaske take sonshi don akan shi tasha yin faɗa da class mates ɗinta tana ganin ita kaɗai ta dace dashi, yau kuwa tunda taji yace tazo ta lallaɓa ta gudu tana ganin yau dai zai furta mata kalmar ƙauna tunda dai ta gama school duk da tasan akwai maganar wani akanta don Babanta yayi alƙawarin bayar da aurenta ga ɗan abokin shi, da zuwanta ya shiga da ita ɗaki ya fara yi mata zance soyayya da yadda ya daɗe yana sonta, da kuma kunyar sanar da mutane yake saboda ita dalibarshi ce, jin haka yasa ta ƙara tabbatar da soyayyar shi, haka ya dinga mata daɗin baki har sai da ya keta mata budurcinta, bata damu ba don gani take yi ai aure zasu yi, haka ta dinga biye mishi suna shan shagalinsu sai dai har sama da wata bai je ko kofar gidansu ba, ita ke zuwa inya kirata bata auni ba sai da cikin jikinta yayi wata hudu sannan ta fahimci ma bata al’ada sam a lokacin fa hankalinta ya tashi nan ta rikice tayi gwaji pt sai ga ciki, Inna ce ta fara fahimta ta tsareta da tambayar haka ta sanar da ita tana kuka, sai dai me? Duk yanda aka yi Malam ya amsa yace bai san zance ba shi hasalima aurenshi saura sati biyu a lokacin, haka suna ji suna gani ya sawa idanunshi toka yace in suka yi misi sharri ma ƙara zai kai su, Inna kuwa tsoron mutane su san abun kunyar daya faru yasa ta yin shiru, nan fa Halima tsoro ya kamata tayi kuka har ta gaji, gashi Dada sai tayi ta binta da kallo tana son tasan ƙibar da tayi da yawan saka hijab da take yi na menene. A lokacin da mahaifin Halima ya frga da cikin jikinta ne yace sai dai ta fita ta bar mishi gida ita kuma Inna tace in dai ya kori Halima sai dai ya haɗa ya koresu gaba ɗaya don babu inda ƴarta budurwa zata tafi ta barta, shawara ta bawa Inna akan su je ƙauyen Innar in ta haihu sai su dawo sai dai bayan sun kama hanya ta kalli Inna a tsorace tace “Inna ina ga mu bar ƙasar in na haihu, yanzu muje inda ba’a san mu ba muce ni matar aure ce hijira muka yi bayan na haihu babyn ya ɗan tasa sai muje wani gari muce abinda na haifa naki ne in yaso in muka ga babyn ya girma ko shekara biyu ne sai mu dawo kinga ba wanda zai gane.” Da wannan shawarar suka shigo garin Kaduna suka kama haya da kuɗin gadon Inna na fili da suka saida bayan ta haihu, Nabila na shekara biyu suka dawo Kano don a lokacin zaman Nigeria ya fara yi musu daɗi suna ganin gwara ta ƙara ko shekara biyu ne, Inna sam auren ma sai taji bai dameta ba don Halima na fita ta samo kuɗi, bayan sun dawo Kano ne suka kama haya anan ne kuma ta ga rayuwar Ummi wanda ta fara kwaɗaituwa da inama ita ce? Ta sani sarai yara dasu ake cutarka shi yasa taja su Zainab a jiki ya zama kafin ma Ummi taji matsalar su sun sanar mata. Dawowa tayi daga ƙaramin tunanin data tafi tana kallon Nabila wacce har yanzu itama tana tsaye a kanta. Inna ce tace “Dukanku ya isa haka, wannan wani irin abin kunya ne?” Tayi maganar cikin raunanniyar murya, wani abu Mummy ta haɗiya ta fito daga gidan ba tare da tayi magana ba, Nabila kusa da Inna taje ta rungumeta kawai tasa kuka, Inna ma hawaye kawai take sharewa wannan wani irin rayuwa ne? Nabila tana kuka tace “Inna ki yafe min wallahi nasan ina son Kabir amma ƙaryar ciki da nayi kawai fansa nake son ɗauka akan Mummy ganin ta banzatar dani taje tana neman suna wurin yaran da ba nata ba, nayi dana sanin haka don daga ɗaukan fansa kan Mummy soyayyar Kabir ta mamayeni har na aikata abinda nayi, ki yafe min.” Kai kawai Inna ta girgiza don bata san me ma zata ce ba, wannan wani irin bala’i ne? Tashi kawai tayi ta koma ɗakinta ta kulle ta baza tagumi lallai son zuciyarta ne ya ja mata don a zamansu sun yi niyya ne in Halima ta haihu su koma yanzu gashinan ita rayuwar ma ba daɗi take yi mata ba, tsoronta ta mutu ƴan uwanta basu sani ba, bare mijinta da kila ma baya raye. ***** Kabir ne ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Salim kafin ya ɗau robar ruwa ya kwankwaɗa yace “Yanzu ba yanda zamu yi mu haɗa su? Ya kake gani in muka yi amfani da matsayin mu? Kai ka kira Baqeer ni na kira Zee muce mu haɗu anan?” Salim ya jinjina kai yana dariya yace “Haka zamu yi am sure in dai sun haɗu tofa tsumar ƙauna zata tashi.” Hannu suka sake yin musabaha wai deal ya haɗu, Kabir yace “Karfa ka manta an jima ƙarfe biyar na yamma.” Salim ya jinjina kai alamar gamsuwa yace “Kai ma kar ka manta.” Da haka suka yi sallama duk sunaji sun ƙosa gobe tayi. Baqeer kuwa kallon mai gidan yayi bayan ya amshi takardun gidan yace “Nagode sosai,” ya dawo mota Tanimu ya tuƙa suka koma gida. Yana shiga gidan yaji muryar Umma na cewa “Koma dai menene kar ki yiwa Baqeer magana yanzu, don na kula yanzu a wuya yake sam bashi da haƙuri sai ya maida abun wani abu, aiki ai ba dole bane.” Dada ce ta cafe da cewa “Tunda ya rabu da Zainab ya zama mara fara’a ga saurin fushi, ni amma Maryama dole ne aikin nan? Ki zauna kiyi biyayya kamar yadda muka yi.” Kekenshi ya tura zuwa cikin gidan, Umma ce ta kalleshi a ranta tana fatan Allah yasa bai ji ba, kallon Maryam yayi wacce tayi saurin goge ƙwallarta tace “Ya Baqeer sannu da zuwa, ni yanzu nake shan labari wai da gaske Zainab budurwarka ce?” Wani abu ne ya taso mishi ya ɗan motsa baki zai yi magana Dada tayi caraf tace “Tsohuwar budurwa dai ko? Yo ni Baqeeru kama taɓa zuwa zance?” Ji yayi kalaman Dada kamar sun ƙara taso mishi da ƙaunar Zainab, murmushin yaƙe kawai yayi yace “Hajiya Dada kenan,” yayi maganar yana juyawa maimakon ya shiga ciki, Umma ce tace “Ina kuma zaka?” Yace “Abu zan amso Umma ba daɗewa zan yi ba," yayi maganar yana murmushi. Waya ya yiwa Tanimu akan ya taimaka ya kaishi wani guri, ba musu ya dawo don dama ba abinda zai yi a gida, gidan Maryam suka nufa don yana son yin magana da mijinta ya sani ba sai an faɗa ba mahaifin mijin ne ya hana aikin, don ya daɗe shi ke shirya su in sun yi faɗa lallai ya daina sakin fuska tunda har Maryam ta gwammace faɗawa Umma akan shi bayan bata yi, wayar Salim ce ta shigo ya ɗaga nan ya sanar dashi wai akwai wani mutumi da yazo yana son ganinshi a Gusto wai yazo daga Abuja ne zai wuce, ajiyar