Sashe 51
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Zeey ce ta ajiye littafin dake hannunta tare da yin miƙa tana ɗan bubbuga bayanta, fuskar Inna a tamke tace "Sai kace wani abu kike yi, bayan tun safe in kika tashi ko gadonki ba iya gyarawa kike ba, yarinya sam an sangartata kamar ba mace ba."
Zeey tayi gyaran murya tana kwanciya akan kujera tace "Inna wallahi ni ban san me yasa kika takura mini ba, ni kenan komai nayi ba daidai ba."
Kallon kazar da take figewa tayi tace "Taso ki tayani to, tunda ke ko kunya ba kya ji irin taimakon nan ma baki iya ba, ke wai a haka ma zaki yi auren?"
Kallon kazar tayi kamar tace bazata iya ba sai dai yafda Inna ke kallonta yasa ta sauka tana cewa "Dama ni mijin da zan aura ai komai yi mini zai sa ayi, nifa ko kitchen ba shiga zan yi ba idan nayi aure, iyakaci na bakin ƙofa nace a dafa kaza."
Tsaki Inna taja tana mikewa tace "Shirmen banza kenan, ita Nabeela dana koya mata komai kina nufin talaka zata aura?"
Da mamaki ta kalleta tace "Inna me ya kawo zancen Nabeela daga hira?"
Kai Inna ta girgiza tace "Sam ni mamakin tarbiyar da aka baki nake, manya na magana kina magana, sannan Nabeela ma kike kiranta?"
Baki Zeey ta turo don dama in dai tazo gidan Inna an dinga ɓata mata rai kenan shi yasa ko awa biyu cikakke bata iya yi a gidan, anya zata iya zama a gidan nan saboda son ganin Baqeer kawai? Muryar Nabeela ta jiyo ta miƙe ba tare da ta kalli kazar ba, Inna ta girgiza kai kawai ta dawo ta cigaba da figar kazarta.
"Seee ji mana." Zeey ta faɗa tare da yi mata murmushi, baki Nabeela ta buɗe ta tsaya tana kallonta cike da mamaki, a tare suka sa dariya kafin tace "Saukar yaushe?"
"Ke kai yawon yaushe?"
Kai ta girgiza cike da jin daɗi tace "Ke dai wallahi neman maganarki yayi yawa In....." Da sauri Zeey ta rufe mata baki kafin tace "So kike dai a fasa mini jiki a kuma koreni."
Dada tana figar kazarta tace "Banda dai jikina babu ƙarfi ai da tuni na aikata."
Nabeela ce ta shigo ciki sosai tace "Meke faruwa?"
Kafaɗa ta ɗaga tace "Zuwa nayi daukarki."
Ai kamar Inna aka taɓa sai cewa tayi "Ɗaukan ta zuwa ina? Inda ba'a ganin girmanta?"
Kallon Inna suka yi ta gefen ido sannan suka yi ɗakin Nabeela, gida ne madaidaici wanda aka ƙawatashi, ɗaki huɗu ne a gidan sai dai uku suka gyara ɗayan a ajiye kawai yake Inna na tara shirgi, akan gadon Nabeela ta kwanta ta sauke nannauyar ajiyar zuciya yanayinta a hankali ya canza.
Nabeela ce ta zauna kusa da ita, tana kallonta cike da mamaki kafin tace "Meke damunki ne?"
Zeey ta miƙe tare da janyo pillow ɗin dake kan gadon ta ɗora akan cinyarta tace "Aunty Nabs." Ta kira sunanta cike da sakalci.
"Tunda kika dawo kema kin shareni ga Mummy sai baƙaƙen maganganu take yaba mini son ranta, ni kam ba shiri na tattara na bar muku gidan ku."
Ta sake maida kanta kan katifa tana kallon ƙwan wutar ɗakin tace "Ni kaina ban san meke damuna ba, ga abu ina son faɗa amma daga nazo yin maganar sai na rasa abin cewa."
Kai Nabeela ta girgiza tace "Wai da a duniya kina rasa abin cewa? Ni ai na ɗauka wannan sai dai mu."
Tashi tayi ta zauna da sauri tace "Ya guy ɗin nan yanzu ya san kina sonshi kuwa?"
Iska ta furzar tace "Ko kaɗan tsabar ma bai sani ba ni yake tambaya shawara akan ƴan matan shi."
"Ba kanta kuma sai ki bashi?"
"To ya zanyi?"
Kai ta girgiza tace "Ba dani ba nifa sai dai mu hakura da abotar kawai kowa yasha zamanshi amma bazan maida kaina ƙawar ƙarfi da yaji ba, shi yasa nifa har yanzu ban fahimci ya kuke wannan son ba, shi yasa kuma nace bazan yi aure ba sai nima na samu wanda nake yiwa irin wannan son da ake faɗa."
Dariya Nabeela tayi tace "Hmm ai ke ko in Allah ya tashi kamaki akan so ko? Harda hakkin mutanen da kika wulaƙanta zai haɗa miki, mu ganki a cikin ɗaki kina kuka shaɓe-shaɓe......" ai bata ƙarasa ba Zeey ta je kai mata duka, a guje ta fita ita ma tabi bayanta, bayan Inna ta ɓoye tana cewa "Wasa nake asibiti zamu kai ki a ƙara miki ruwa."
Inna ce ta kalli Zeey dake neman jawo Nabeela tace "Wai ni kam Zainab baki san kunyar idon uwa ba ko?"
Tsayawa tayi tana kallonta, ta cigaba "Shin Nabeela ba Auntynki bace kike neman dukanta? A gabana mahaifiyarta?"
Takaici ne ya kama Zeey kawai ta koma ɗaki ta kwanta, shiru tayi tana tuno yadda ta bar Baqeer ɗazu, ko ya koma gida yanzu? Me yayi daya daɗe a tsaye ɗazu? Ji tayi zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, nan da nan kuma taji hankalinta ya tashi, wayarta ta ɗauko ta dubo number Dada data amsa akan in mutumin ya iso zata kirata ta sanar da ita.
Ringing uku ta ɗauka tace “Assallamu Alaikum wanene?”
Zeey ce tayi murmushi tace “Hajiya Dada ba dai har kin kwanta ba? Naga dai ba’a daɗe da yin isha’i ba.”
Jin muryar Zainab yasa ta fara magana a rikice “Zainabu na shiga uku, tun ɗazu nasa a nemo Baqeeru amma har yanzu ba’a ganshi ba.”
A wani zabure ta mike tsaye tace “Kamar yaya ba'a ganshi ba?”
“Wallahi tun fitar da yayi har yanzu bai dawo ba.”
Ai bata gama jin wani abu ba ta zari key a guje ta fito daga gida, Inna ce ta kalleta tace “Dama kece zaki iya zaman nan? Ke da ko faɗa ba kya so?”
Ta kalli Innan sannan ta kalli Nabeela tace “Aunty Nabs zan je na dawo ki faɗawa Inna ta taimaka ta maida wuƙar.” Tana kaiwa nan ta fita cikin hanzari.
Da yake babu nisa tsakanin Ɗanladi nasidi zuwa Mariri inda Dada take yasa bata daɗe ba ta iso, maimakon tayi gidan inda ta ganshi ɗazu tayi sai dai babu shi babu alamar shi, hankali a tashe ta cigaba da nemanshi, tunanin zuwa wurin Dada tayi ganin tayi nisa cikin layin don har bata san inda ma take ba.
Kamar a mafarki ta ganshi zaune gefen wasu yara kamar almajirai suna hira yana zaune yana kallonsu, can taga yana nuna musu abu kamar a takarda sai kuma suka sa ihu suna tafi.
Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tana jin zuciyarta na sauka a hankali, lallai ba kanta ƙalau ba, to wai ma Baqeer yaro ne da zata rikice haka? Amma ba laifinta bane tunda yanzu duniyar ce ta koma haka.
Miƙa musu takardun yayi sannan ya fara ƙoƙarin burga kekenshi wani ta gani yazo da sauri cikin yaran yana turashi, bata san me suke cewa ba amma tabbas fuskar Baqeer ta canza da alama ya samu nutsuwa zaman da yayi dasu.
Motar taja a hankali tana binsu a baya, waigawa yayi gefe nan suka haɗa ido da ita, da sauri ta ɗauke idanunta kallon yaron da yake turashi yayi ya mishi alama daya bari sannan suka yi magana sai taga ya juya.
Fitowa tayi daga motar ganin bashi da niyyar cigaba da tafiya, daga ɗan gefenshi kaɗan ta tsaya, sanye take da kayan ɗazu.
Shiru suka yi sai kallon gari da suke, a hankali tace “Me kake yi anan? Hankalin Dada ya tashi.” Shiru yayi babu alamar amsa a tattare dashi, haka kawai taji duk takaicin kanta ya rufeta, tana mace mai aji me take yi haka ne wai? Ba tunani ba komai? Juyawa tayi sai dai bata yi taku ko ɗaya ba taji yace “Me iyayen yaran nan suke tunani da suka kawosu almajiranta?”
Waigowa tayi ta kalleshi ba kallonta yake yi ba sai dai har yanzu idanunshi nakan gefe inda yaran suke, kallonsu tayi kafin tace “Neman ilimi, sannan da rage dawainiyar yaran da suke dashi.”
Kai kawai ya jinjina ga mamakinta bai ce komai ba ya fara tura kekenshi, so take ta tura mishi amma baza ta iya ba, so take yi ta bishi nan ma bazata iya ba, Baqeer kuwa tunanuka kala-kala ne suka zo mishi a fitar nan da yayi, anan ne kuma ya gane tabbas Allah na sonshi da rahama da bai ɗauke mishi hannayenshi ba, yaga abubuwa da aiyuka kala-kala, tsofaffi haka suke famar aikin ƙarfi don su tallafi iyalansu, zuwanshi wurin almajiran nan hankalinshi ya tashi ganinsu babu abinci babu wata suturar kirki, babu wani abun yi amma basu karaya ba, sai bi suke yi suna neman abun yi don a biyasu ko naira ashirin ne su samu suci abinci, nan ya tsaya wurinsu yana gani suna hirar yanda mutane ke cutarsu in suka yi musu aiki su hanasu hakkinsu wanda hakan ba ƙaramin tada mishi hankali yayi ba, sai dai ga mamakinshi duk da hakan basu karaya ba gobe ma komawa suke yi, kusan sama da rabinsu babu ma mai takalmi, almajirin ne taga ya sake tahowa da gudu ya bi inda Baqeer yake ya riƙe keken, yana turashi, barinta zai yi anan babu ko magana? To wa ya kawoki Zeey? Abinda zuciyarta tace mata kenan wanda ba shiri ta shiga mota, kiran Dada tayi da sauri ta ɗauka tace “Zainabu? Kinga nama sa an siyo minu kati na kirashi wai fita kawai yayi yanzu zai dawo.” Tace “To Alhamdulillah, sai da safe.” Nan ta kashe wayar ta kwantar da kanta a kujerar motar, ko Dada hankalinta bai tashi ba sanda ta kirata amma ita kalleta harta rugo kamar ance mata mahaifinta aka rasa. Babu shiri taja mota ta wuce, yana kallon sanda motarta ta wuce, da kallo yabi motar tabbas ƴar gidan masu kuɗi ce kuma yanzu ya tabbatar ta ɗauke shi ne a matsayin irin mutanen da suka saba taimakawa don haka dole ya miƙe ya bambanta kanshi daga ragwayen maza.
Tana komawa gidan Inna ɗaki ta wuce ta canza kaya tayi brushing ta kwanta, ko abincin ma bata jin ci sam ta kasa gane abinda ke yawo akanta sai dai yanayin Baqeer ya kasa fita a ranta, tabbas wani abu ya canza a tattare dashi amma bata san menene ba.