Sashe 97
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan yayi sallar asuba ya daɗe yana addu’oi tare da godewa Allah da al'amuranshi suke sake daidaituwa, ji yake yi sai yanzu ne ma ya cika namiji tunda da kanshi yake neman kuɗi ba wai Baba ne yake tsaye akanshi ba, yayi karatun Alkur'ani sannan ya ɗan yi exercise na ƙafar shi, yanzu sosai yana jin ƙafar a jikinshi dkn har yatsun ƙafar shi ya fara iya motsawa, bayan ya gama komai ya dubi agoggo karfe bakwai da rabi gashi yau babu makaranta hakan yasa ya kwanta akan gado, wayarshi ya sake janyowa don tun kafin ya tashi yaga sakonta yace sai ya gama abinda yake zai yi mata reply.
Fuskarshi ɗauke da murmushin da shi kanshi bai san yana yi ba ya rubuta “In kina so ki sani kizo wurin Dada ta sanar dake!” Ya kifa wayar tare da sa hannunshi a bayan kanshi, mamaki yake yi wai shine yake murmushi haka kawai inya tuno Zeey? To shi ya san tafi ƙarfinshi ya kuma san bai cancanci mace kamarta ba yana gurgu sannan ita me yayi mata? Ita kuwa abubuwan data mishi har ba zai iya ƙirgawa ba, a hankali yake lumshe ido yana buɗewa a haka bacci yayi gaba dashi.
Can cikin baccinshi yake jiyo muryar Maryam ita da Hadiza, mamaki ne ya kamashi hakan yasa ya miƙe tare da duba agoggo karfe sha ɗaya na safe, haka ya tashi ya shirya sannan ya ɗauki wayarshi saƙonta ya gani akan in tazo kyautar me za’a mata? Ba tare da dogon tunani ba ya maida mata “Ƙawarki tazo kizo ku gaisa!” Yana kaiwa nan ya fita wurinsu Maryam wanda ganinshi yasa duk suka saki fara’a, wani irin jin daɗi ne ya kamasu don Maryam karyar ma tayi akan zata je wani taro a makarantarsu Areef ta samu ta gudo ganin Baqeer, har ga Allah bazata iya cigaba da daɗewa haka ba tare da ta ganshi ba, ita kuwa Hadiza dama ba hanata zai yi ba in dai yaji ba shi zai biya kuɗin adaidaita ba, haka suka shiga ɗakin Dada suka gyara shi tsaf sannan suka gyara na Baqeer suna tsokanarshi akan yanzu ya zama tailor don haka ɗinkin su na sallah na wuyanshi, murmushi kawai yayi yace “Ai ku kuma yanzu shikenan kun samu pass ku shirya har na mazajenku ma sai ai muku,” ya ƙarasa maganar yana duba agoggon jikin wayarshi ya kamata Zeey tazo gashi ya ce mata Maryam na nan amma shiru, zuciyarshi tana so taga yanayin yanda zasu yi magana ita da Maryam har ya samu yaji ya alaƙarsu take daga nan ya bugi cikin Maryam akan me ta sani akan Zeey.
A bangaren Zee kuwa tunda taji labarin Maryam na nan ta san babu ita ba zuwa don tabbas in taje tasan shikenan Baqeer zai san ita wacece daga nan kuma alaƙarsu tasan tazo ƙarshe, gashi tana son ganin Baqeer, tsoro ne ya shiga yawo a zuciyarta kenan a haka zasu cigaba da alaƙa a sirrance? To alaƙar mecece tsakaninsu? Kanta ta kwantar saman pillow don bata san amsar da zuciyarta ke nema ba, Mummy ce ta turo ƙofar kallonta tayi bayan ta zauna kusa da ita tace “Ni kam yiwa yaron nan waya kice yazo ina son ganinshi don tabbas bazan taɓa yarda ya maida mini auta ta haka ba.” Zeey ce ta dago tana kallonta aranta tace “Kema in kin san wanene ba barina zaki yi ba.” Amma a fili sai cewa tayi “Mummy ban taɓa shakkar abu ba irin alaƙata tsakanina dashi, ban san matsayina a wueinshi ba, ban san ya zata kasance ba in har ya san ko ni wacece, Mummy shikenan rabuwa zai yi dani ko?” Da mamaki tace “In yasan ke wacece kamar ya? Akwai wata alaƙa ne tsakaninki dashi?” Kai ta kauda da sauri sannan tace “Ba haka nake nufi ba kawai dai kinga bai san komai nawa ba.”
Kai Mummy ta jinjina tace “Taso muje falo so nake muyi magana akan matar Kabir ina ga is time yayi settling Daddynki yana tunanin Zinnira ɗiyar oganshi.”
Saman goshinta ta ɗan daka tace “No wonder ashe neman auren dole kuke yi mishi shi yasa jiya ya dawo cikin wani yanayi, Mummy please ku ƙyaleshi ya zaɓi matar da yake so da kanshi.”
“Cikin wani yanayi kamar ya?” Tayi tambayar tana kallonta, baki ta taɓe tace “Aunty Nabs dai ta kareshi amma ni ban yarda ba am sure wani abun yayi ashe kune.” Mummy bata ko tsaya jin ƙarashen maganar ba ta miƙe don dama maganar auren da take cewa yayi saboda Nabila ne tabbas bazata yarda da wannan haukan ba.
Ƙofar ɗakin ta buɗe da karfi, akan kujera ta ganta a kishingiɗe tana danna waya, duk fuskarta ma taga ta sake ɗashewa, a fusace tace “Uban me ya haɗaki da Kabir har Zainab ta ganki?” Ta sani sarai bakin Zeey bazai yi shiru ba hakan yasa ta miƙe zaune tace “Bafa komai abu kawai na…….” Yunƙurin amai ta fara yi, nan da nan Mummy hankalinta ya ƙara tashi, a fusace ta kalleta tace “Wuce muje asibiti wallahi bazaki ja mini abin kunyar da za’a dinga nuna ni ba sannan Kabir aure zan yi mishi don haka ki tattara ki bar gidan nan, na dai faɗa miki.” Tana kaiwa nan ta juya, ga mamakinta Nabila biyota tayi waje tana dafa bango alamar jiri take ji, Mummy ce ta kalleta tace “Meye hakan kike yi? Ki koma ki kwashe kayanki yau zan maida ke da kaina ma….”
Ƙarar data saki ne yasa Mummy tsayawa ta saki baki tana kallonta, Zeey ce ta fito da gudu tazo inda take, Nabila na ganin Zeey ta sulale a ƙasa tana riƙe ciki, hankali a tashe Zeey ta ƙaraso ta ɗagota tana cewa “Menene Aunty Nabs?” Hawaye ne ya zubo mata tace “Zeey ni kam tsintata akayi a titi hala? Wannan wace irin ƙiyayya ce ke tsakanin ya da ƙanwa? Ki taimaka ki kaini gidan Inna shi yasa sam bana son zuwa gidan nan, Mummynki ke kaɗai take son gani a gidan nan na gaji da gidan mu ayi ta wulakantani Zeey…” Fashewa tayi da wani irin kuka, Zee ta kalli Mummy cike da rashin jin daɗi tace “Wai don Allah Mummy me yasa kike haka? Sai kace bare? Ƙanwarki uwa ɗaya uba ɗaya tilo amma kin kasa kyautata mata?”
Takaici ne ya rufe Mummy ganin yanda Nabila ke kuka wiwi, muryar Daddy suka ji yace “Ke Nabila tashi ki koma ciki ke kuma ki zo ina son magana dake.”
Bin bayanshi tayi don takaici ma ya hanata magana amma duk abinda za ayi sai dai ayi dole Nabila ta bar mata gida.
Haka Daddy ya sata a gaba yana faɗa, jinshi kawai take yi don shi a duniya duk abinda zaka ce akan Nabila baya gani shi a kullum gani yake yi ma ba kowa ne ya kaita tarbiyya ba, yana gamawa ya fito ya shiga mota ya bar gidan zuciyarshi duk babu daɗi.
Da ƙarfi driver ɗinshi ya ja birki ganin motar data kawo kai, wanda har saida Sulaiman Karaye ya ɗan bigi kujera kaɗan, driver ya juya yana bashi hakuri sannan ya kalli motar, kafin driver ɗin ya fita har shi mai ɗaya motar ya fito yana tafe yana riƙe ƙugu, glass ɗin ya ƙwanƙwasa hakan yasa drivern ya fita waje yana cewa “Yallaɓai kayi haƙuri ban kula ka taho bane.”
Wani kallo yayi mishi sannan yace “Eh da kasheni kayi ma kenan haƙuri zaka bawa iyalina? Ko?”
Zai ƙara magana idanuwanshi suka kai kan Sulaiman dake zaune, wani mugun tamke fuska yayi yace “Da walaki ai tunda ka ɗauko ɓarawo ai dole dama idanunka ba zasu kula da hanya ba, aikin banza wallahi da kun bigeni da sai na kai ku ƙara wurin ƴan sanda, munafikai kawai.”
Sulaiman ne ya zuge glass yace “Ka tabbatar kaje asibiti an baka gado dkn da alama ƙusumbi ne ya fito a bayanka, kai Mamman mu tafi don Allah.” Badaru takaici ya rufeshi yace “Kasan Allah ka shiga hankalinka dani, kafi kowa sanin tsaf zan ma tijara ni ba kunya gareni ba.”
“Tunda tsufa yayi gardama dama kai kam menene ma baza kayi ba?” Mamman ne ya shiga suka ja mota suka bar Badaru yana ta masifa da zage-zage, kwankwason shi ne yayi ƴar ƙara ya ja tsaki yace “Wallahi Kamalu sai kasan kayi dani.”