Sashe 19
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yadda Umma ke kallonta ne yasa gaba ɗaya jikin Hadiza yin sanyi cike da kulawa take bin Umma da kallo tace "Ba dai har lokacin tafiyar tasu Abuja yayi ba?"
Umma zata yi magana suka jiyo salatin Bashir yana haɗawa da sunan Baqeer, cikin hanzari Umma ta miƙe ta fito ita ma Hadiza tabi bayanta, kafin su iso har Abu da Jamila sun fito, gaba dayansu ɗakin Baqeer suka nufa, a ƙasa suka ganshi ruwa duk ya malale a ƙasan, cikin sauri Umma ta ƙarasa kuda dashi tana cewa "Baqeer meya faru? Menene?" Kasa magana yayi sai hawaye kawai dake cigaba da taruwa a idanunshi, Bashir ta kalla tace "Me ya faru?"
Yace "Ni ban sani ba na shigo zan ɗauki aron laptop ɗinshi na ganshi a ƙasa da alama ma ya daɗe da faduwa". Nan da nan Umma taji hankalinta ya tashi, Abu ta kalli Jamila kafin tace "To Fatima wannan fa ina ga sai dai ki sakashi kusa dake inba haka ba wani abun zai iya samunshi ba'a sani ba." Takaici ne ya kamata don tasan wulakancinsu ne ya tashi idan ba haka ba taya zasu ce ta mayar da Baqeer dakinta? Bata ko kulasu ba suka juya suna ƴan ƙananun maganganu, Bashir ne ya taimaka mata suka mayar dashi kan katifa sannan ya fita, Hadiza kam a ƙame take ƙam tana jin zuciyarta kamar zata fashe, me take gani haka? Meke faruwa? Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta kasa gasgata mata abinda take gani, idanun Baqeer ne ya sauka kanta, sai a lokacin hawayenshi suka zubo ganin yadda take hawaye wani na bin wani, jan ƙafafunta ta shiga yi zuwa inda yake ta kama ƙafafuwan shi kawai tasa wani irin kuka, ganin haka yasa Umma ta miƙe ta bar musu ɗakin tana share ƙwalla, ta sani Baqeer kamar uba yake a wurin su ta daɗe tana tunanin yadda zasu ɗauki wannan abun, tafi minti goma tana kuka don har ƙarfinta na kukan ya fara raguwa kafin ta ɗago, kallonshi tayi kai kawai ya kauda tare da runtse ido, ta dawo inda yake tace "Yaya ba zai yiwu ba ka tashi kayi tafiya dan Allah! Na rokeka da Allah ka tashi kayi tafiya."
Hannunta da tasa tana jan hannunshi ya kalla ya kai hannunshi na dama sai riketa yaji wani uban zafi ya maida hannun wanda hakan yasa ta kalleshi da sauri sai a lokacin ta kula da yanda aka naɗe hannun, a rikice ta sakeshi ta fashe da kuka tana cewa "Na shiga ukuna Yaya menene haka? Laifin me muka yi da Allah zai jarabce......"
Hannu yayi saurin sawa ya rufe bakinta yana girgiza mata kai, hannu tasa ta goge hawayen idanunta tace "Meya faru Yaya? Yayan mu dan Allah ka tashi."
Yawun bakinshi ya haɗiya don ko magana yanzu baya son yi, Baba da Asiya sun sake tabbatar mishi abinda yake tsoro. Bakinshi ya sake motsawa kafin yace "Mijinki fa? Babu dai wani abun ko?"
Nan fa hawayenta suka ƙaru tace "Yaya wa ke tani kana cikin wannan halin? Yaya duk abinda nake ciki bai kai kwatan naka ba, na shiga uku."
"Kin tabbatar ba wani abun?"
Ji take yi kamar tayi ihu, wannan wani irin abu ne take fuskanta? Da gudu ta tashi ta bar ɗakin tana shiga ɓangaren Umma ta wuce ɗaki ta faɗa kan gado, shikenan su kuma sun zama marayu don dama Allah ne gatansu Baqeer gatansu, duk su biyun rayuwar auransu kowane na cike da kalubale amma babu wanda ya sani a gidan sai Baqeer saboda shi kaɗai ke saita musu komai ba tare da manya sun shiga cikin maganar ba, yanzu ya zasu yi? Kuka take sosai har ƙarar kukanta ya tashi yarinyarta Aydah dake kwance daga bacci.
Umma ta shigo ta ɗauketa ta fita da ita don tasan dole Hadiza tayi kuka, samun Baqeer yasa su kwanciyar hankali wanda a koda yaushe take alfahari da yadda yake kula dasu.
*******
Asiya ce kishingiɗe akan gado tana jin Inna da Habi nata aikin waina a waje amma tana kwance a ɗaki don ita sam bata son aiki ba kuma ta son girki especially da murhu, shi yasa tace gidanta inba gas cooker ba sai dai a siyo takeaway amma ba zata iya aikin hayaƙi ba.
Waya take yi cike da fara'a, Habi ce ta shigo ɗakin sai gumi take yi na hayaki idanunta sunyi jaa ta shigo ɗaukan radion Inna ne data ara jiya da daddare, ganin Asiya tana waya yasa tace "Waye? Baqeer ne?" Asiya ta kauda kai alamun a'a sannan tace "Yanzu kana Abujan?"
Daga jin haka yasa Habi ta matsa tasa kunnenta gefen wayar tana son jin abinda ke faruwa, Asiya tace "To shikenan Bello Allah ya bada sa'a sai ka dawo."
Miƙewa Habi tayi tana wa Asiya kallon tuhuma harta kashe wayar, cike da mamaki tace "Bello kuma? Yaushe kuka fara waya akai-akai haka? Don jiya ma naji sanda ya kira yace miki kiyi mishi addu'a wai zai yi tafiya."
Tsaki Asiya tayi tace "Koma yaushe muka fara menene damuwarki a ciki? Kawai kirana yayi yace in sakashi a addu'a akwai abinda yaje yi Abuja yana so Allah ya bashi nasara shikenan sai nace bazan yi ba?"
"Ji wani munafurci, addu'ar iyayenshi bata isheshi ba sai ya haɗa da taki? Ko sanda Baqeer yake nemanki a waya kin ɗaga ne? Wallahi dai kunji asara daga ke har shi in ma wani abun kuke tunani, aikin banza kawai." Tana kaiwa nan ta juya ta ɗauki radio ɗin ta fita a fusace ranta a mugun ɓace, baki kawai Asiya ta taɓe don ita ƙarfin halin Habi har mamaki yake bata.
*******
Da ƙyar Hadiza ta saki ranta, jin shirunta yasa Umma ta shiga ɗakin ta zauna kusa da ita ta sanar da ita duk abinda ke faruwa, ta kalleta a rikice tace "Yanzu suna nufin shikenan ya rasa ƙafafuwan shi?"
Kai Umma ta ɗaga tace "Addu'a ce tamu amma haka suka ce."
Ta goge hawayenta wanda idanunta har sun ƙanƙance saboda kuka tace "Umma ɗazu fa da alama ruwa yaje sha ya faɗo dan ga jug na ruwa nan a ƙasa, kina nufin haka zai dinga rayuwa?"
"Wanda kuma Allah ya halicce shi a haka fa? Wanda kuma Allah ya jarabceshi da rashin ƙafa? Hannu da ido fa? Ko kuwa wanda Allah ya jarabceshi da ciwon da baisan inda yake ba fa? Ba haka suke cigaba da rayuwa ba?"
Hadiza tayi ƙasa da kai don ita kam bata san me zata ce ba "To ya zamu yi? Mun isa jaa da hukuncin Ubangiji ne?"
"Bamu isa ba sai dai ina ganin mu samu wani ya dinga kula dashi bazai iya zama shi kaɗai babu mai taimaka mishi ba." Hadiza tayi maganar cike da jin tausayin ɗan uwan nata.
"To Hadiza in mun samu wani waye zai dinga biyanshi?" Umma tayi maganar tana kallonta, nan ta dago tana jin zuciyarta na zafi ace duk abinda yayansu yayi musu yanzu su lokacin rama mishi yayi amma babu hali? Ita mijinta ba mai babban karfi bane gashi kullum cikin rigima suke dashi saboda ba ita kaɗai bace a wurinshi gashi baya son haihuwa tunda suka yi aure bata dade da samun ƴan biyunta ba ya fara ito mata da halayenshi sai gashi kuma babu daɗewa ta ƙara samun cikin Aydah anan ne yace sai dai taje asibiti a zubar ita kuma tace sam, haka suka yi ta rigima data so yin yajin Baqeer ya daidaita su, sai autar Umma Maryam ita kuma mijinta dan kasuwa ne yana da kuɗi kuma yana kyautata mata bakin gwargwado sai dai matsalar uban miji wanda ya addabeta ya hana samun zaman lafiya da mijinta, gaba ɗaya zaman aurenta bata sati ɗaya ko biyu sai Baqeer yaje yayi sulhu akan saɓanin da uban mijin ke haddasawa a tsakanin su.
Jin kalaman Umma yasa Hadiza tayi shiru, shikenan su babu yadda zasu yi? Miƙewa tayi ta koma wajen Baqeer ta gyara ƙasan ɗakin ta dawo ɗakin Umma ta ɗauki drawer ɗinta ta gefen gado ta kai ɗakin tasa kusa da inda katifarshi take tasa aka siyo ruwan pure water tasa a saman drawer ɗin, sannan tasa spoons da plate da wasu ruwan a cikin drawer ɗin, ta ɗauko papers da pencils tasa a na ƙasa nan ta fara kale-kale tana neman wasu abubuwan da zai buƙata, duk abinda Hadiza take yi idanun Baqeer na kanta, kallonta kawai yake yi don kwanan nan sam baya jin magana mutuwa kawai yake jira tazo ta ɗauke shi, ɗazu ma daya faɗi shi yasa ko ƙira bai yi ba azo a taimaka mishi, jira yake yana daga kwancen nan rai yayi halinshi, sai gashi nan garau sai ma wani tashin hankalin daya sake shiga.
Wayarta ta ɗauko kawai ta cire sim ɗinta na mtn ta bar airtel a ciki ta ajiye kusa dashi tace "Yaya ga wayata sim ɗin bana amfani dashi data kawai nake siya idan na samu dama, Umma tace an sace maka waya dama kaine ka saya mini ita kaga yanzu sai ta dawo wurinka, ina zaka iya rayuwa babu waya babu aikin daka saba babu komai a ɗaki? Sannan anjima Salim zaizo sai mu turaka tsakar gida ka dinga samun iska kana shaƙa ba wai kullum kana ƙunshe a ɗaki ba."
Wayarta ya miƙa mata kawai ya girgiza kai alamun a'a cikin dakewa ta girgiza kai tace "Don Allah Yayah ka rufa mana asiri kaine gatan mu, wannan rashin maganar Yaya baza mu iya ɗauka ba ka taimakemu ka dawo yanda kake kar baƙin ciki yayi maka illa don Allah!"
Murmushi yayi na yaƙe, ta sake miƙa mishi wayar sannan ta fito, kallon wayar yayi yana ji kamar ya kira Asiya sai dai inaa bazai iya ba don shi yanada zuciya baya zama inda ba'a sonshi, balle yanzu da yake neman komawa ga Allah, hakan yasa ya ajiye mata wayar a gefe.
Hadiza tana fitowa ta ɗauki wayar Umma ta kira Maryam tace Inda hali tazo gida in ta dawo daga ɗauko Areef daga makaranta. Ba tare da wata damuwa ba tace to zata biyo.