← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 168

Sashe 30

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ya ƙarasa kasuwa zuciyarshi baƙi ƙirin yake jinta, ya rasa inda zai saka kanshi yaji daɗi, duk ya tuna wai Bello yaron da jajircewar Baqeer a kanshi ce tasa ya ƙware a harkar zane ne wanda ya tafi a madadin Baqeer har ma ya karɓo award sai yaji kamar ya kwanta a ƙasa yayi ta burgima ko ya samu yaji sauƙin raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyar tashi, gashi mutane da gulma da kinibibi yayi wa yawa sai faman tararshi suke yi suna tambayar ba'asin yadda aka yi Baqeer bai tafi gasar ba sai dai abokin shi ne yaje a madadin shi, har rasa amsar bayarwa yake yi don ashe wai duk ɓoye-ɓoyenshi na kada asan halin da suke ciki da Baqeer ɗin mutane sun sani, har wani gugar zana ake yi mishi ana cewa yaron daya fifita fiye da sauran ƴaƴan shi gashi kuma inda rayuwa ta kaisu bai zama abinda yake kuri da cika bakin zai zama ba a harkar zane.

Yaran shagon shi kansu sun san yau zuciyarshi a wuya take, ɗan kuskure ƙalilan zasu yi sai dai ya rufe su da faɗa don haka suke takatsantsan dashi don sun daɗe da sanin halinshi dama shi yasa suke haƙuri da tijarar shi idan ya fara sai dai suyi ta bashi haƙuri. Yana zaune a cikin shagon shi inda yake sayar da kayayyakin sawar mata kama daga su atamfa, leshi, shadda, material da voiles yana kallon shige da ficen mutane masu shigowa yin sayyaya ɗaya daga cikin yaran shagon yazo ya russuna yace mishi yayi baƙo. Ɗan tsaki yaja irin na an takura shi ɗinnan ya cewa yaron ya cewa baƙon ya shigo daga ciki. Ƙara tsuke fuska yayi ganin mahaifin Bello Alhaji Bala ya shigo da fara'arshi. Hannu ya miƙa mishi haɗe da yi mishi sallama sai dai da ƙyar ya buɗe baki ya amsa sallamar ba tare daya bashi hannu sun gaisa ba. Sai ajiye hannunshi Alhaji Bala yayi ganin Mallam Badarun baya da niyyar mayar mishi. Bai fasa abinda ya kawo shi  ba duk kuwa da yaga irin karɓar da yayi mishi. Da farko tambayarshi ya fara yi yanayin jikin Baqeer sai dai Mallam Badaru yayi kicin-kicin da fuska yaƙi amsa mishi don haka ya bar wannan maganar ganin kamar baya sonta ya fito da envelope daga aljihun shi ya miƙa mishi yana cewa "Dama zuwa nayi mu gaisa na kuma kawo maka ɗan wani abu daga abinda Bello ya samo a wajen gasar da yaje ganin komai ya zama Baqeer ne sila nace ai ba'a yi tuya a manta da albasa ba tunda ma banda Allah ya aikowa da Baqeer wannan tsautsayin kujerar ai tashi ce to kana naka ne Allah yana nashi ta Allah kuma ita ce daidai, dama can Allah ya nufa Bello ne mai zuwa wannan wurin shi yasa nace bari na kawo maka wannan kasa albarka, shi kuma Baqeer Allah ya bashi lafiya ya tashi kafaɗunshi ya bashi ikon cinye jarrabawar da yayi mishi.”
Da ace Alhaji Bala ya lura da yadda maganarshi ta fusata Mallam Badaru yana ƙara hawa kamar farashin mai a Najeriya da tuni yayi shiru sai dai da yake shi da zuciya ɗaya da kuma kyakkyawar manufa yazo wurin shi yasa bai lura da yadda yanayin shi ya canja ba har sai da ya daka mishi tsawa yace "Dallah Mallam yi mini shiru munafukin banza munafukin wofi, har ni zaka kawowa munafurci kazo da wani kuturun wulaƙanci kana ce mini haka Allah yayi ba Baqeer bane mai zuwa wajen gasa Bello ne? Ni dama na daɗe da sanin abotar Baqeer da ɗanka babu inda zata kai shi sai a ajin dana sani, shine bai sani ba har ya janyo Bello a jikinshi ya nuna mishi yadda ake zane ya baje mishi dukkanin wasu sirrikan samun nasararshi gashi nan yanzu yayi mishi halin ƴan adam ya munafurce shi ya tafi wajen gasar a madadin shi bayan yasan Baqeer baya da wani buri a rayuwa face zuwa wannan wuri, da Allah tattara gayyar tsiyarka ka fice mini daga shago idan ba haka ba nasa yara suyi maka dukan mutuwa wallahi.”

Baki buɗe Alhaji Bala ke kallonshi yace “Dama abun arziƙi ya taɓa zama na tsiya? Daga zuwa nayi maka alheri ganin komai Bello ya zama ɗanka ne sanadi shine zaka bini da baƙaƙen maganganu kana nema ka zageni?”

A harzuƙe ya tashi tsaye shima yana nuna shi da ɗan yatsa yace "An zageka ɗin, nace maka an zageka ɗin, kai ɗin har wata tsiya ce da ba za'a zageka ba, munafukai masu saka alheri da sharri, duk alherin da Baqeer yayi wa Bello bai yi mishi baƙin ciki ba ya nuna mishi kan sana'ar shi amma ya rasa da abun da zai saka mishi sai wannan?” Haka dai suka yi ta cacar baki da ƙyar aka samu aka fitar da mahaifin Bello daga shagon don sosai ranshi ya ɓaci da tijarar da Mallam Badaru yayi mishi daga abun arziƙi. Har ya bar kasuwar zuciyarshi nayi mishi zafi, dama takaicin maƙwabcin shi daya tare shi da gulma wai yanayi mishi jaje sai kace ance mishi yana buƙatar jajenshi, a yanzu shi abu ɗaya ne zai wanke mishi zuciya yaga Baqeer ya dawo daidai ya koma harkokinshi kamar da.

*****
Tunda ta kwanta sai faman juye-juye take yi akan makaɗeɗen gadonta da yaji shimfiɗa ta alfarma. Koda wasa ta kasa runtsawa data rufe idanunta shi kawai take gani yana yi mata gizo, ta kasa yardar wa ranta cewa wai wannan gurgun da take yawan gani ana tura shi a wheel chair Baqeer ne wanda ta sani tun suna yara, yayan ƙawarta Maryam mai yawan tsokanarta yana sakata kuka har ya janyo ta daina shiga gidansu saboda yawan tsokanarta da yake yi. Juye-juye kawai take yi tana saƙa da warwara maganar na cinta a rai ta kasa furtawa kowa ko don bata saba barin abu a ranta ba yasa wannan ɗin ta dameta ganin ta kasa faɗawa kowa yadda ganin Baqeer ɗin a keken guragu ya ɗaga hankalinta.

Yaye duvet ɗin data lulluɓe rabin jikinta tayi ta sauko daga kan gadon a nutse ta saka bedroom slippers ta fita zuwa ɗakin Nabila dake daura da nata. Cikin sanɗa ta tura ƙofar ɗakin ta zura kanta a hankali, switch ɗin fitila ta danna haske ya gauraye ɗakin. A naɗe akan gado taga Nabila tana bacci hankalinta kwance alamun babu abinda yake damunta, ƙarasawa tayi gaban gadon tasa hannu zata yaye duvet ɗin data rufe ilahirin jikinta dashi sai kuma ta fasa, yanzu idan ta tasheta tace me ya hanata bacci, ita dai tasan ko kusa ba zata iya fitowa tace mata ga abinda yake damunta har ya hana mata bacci ba don haka ta juya ta kashe mata fitilar ta bar ɗakin. Ɗakinta ta koma ta hau kan gado ta kwanta sai dai cikin ranta ta ƙudurce gobe zata koma gidansu ko don ta ƙara tabbatarwa da kanta cewa Baqeer ne dai data sani wannan gurgun.

Da ƙyar ta samu bacci ya ɗauketa koda ta tashi sai ta tashi da ciwon kai saboda rashin samun isashen bacci da bata yi ba. Haka ta fio idanunta a kumbure, Mummy na ganinta ta tashi ta tarota cikin tsantsar kulawa take cewa "Kinga yadda fuskarki ta kumbura kuwa Zeey? Ba dai wani abu ne ya sameki ba ko? Dan tun jiya na kasa gane kanki.” Tana yi tana taɓa jikinta sai dai babu alamun zazzaɓi don haka ta ɗan kwantar da hankalinta sai dai Zeey ɗin nace mata headache ne take fama dashi ta ƙara rikicewa har sai da Nabila tayi magana tace "Haba Sis, headache ɗin ne zai ruɗar dake kamar baki san Zeey da raba dare tana kallo ba, yanzu haka kwana tayi tana kallo bata kwanta da wuri ba shi yasa kanta yake ciwo amma daga taci abinci ta sha magani zai warware.”

Kallonta Mummyn tayi tace "Wai haka ne My Zeey?" Ɗaga mata kai kawai tayi don yau sam bata jin son yin magana, zama tayi akan kujerar dining table. Da kanta Mummy ta taso ta haɗa mata tea sannan ta ɗauki plate ta haɗa mata breakfast duk ta tura a gabanta tana cewa "daure kici kin ji baby sai ki sha magani kije ki kwanta ki huta". Da kai ta amsa mata sannan ta fara cakalar abincin kamar mai cin maɗaci, haka dai ta caccakala ta tashi ta koma ɗakinta bayan ta sha paracetamol tayi wanka sannan ta hau gado ta kwanta.

La'asar nayi ta tashi ta shirya cikin wata free English gown beige color sai ta yafa farin jersey veil a kanta, bata yi wata kwalliya ba sai perfume da ta fesa. Ɗakin Mummy ta shiga tace mata "Mummy don Allah zan ɗan fita yanzu zan dawo ba zan daɗe ba". Kallonta Mummy tayi tace "har kan naki ya daina ciwo da zaki fita? Wai shin ina ma kike yawan zuwa kwanannan da kullum sai kin ƙirƙiri fita bayan kin sani sarai Daddynki ba son yawan fitarki yake yi ba".

"Kiyi haƙuri Mummy wallahi ba zan daɗe ba yanzu zan dawo.”

"Ni dai don Allah kada ki daɗe bana so Daddynku ya dawo bai sameki ba".

"Thank you Mum" tace haɗe da hugging ɗinta, fita tayi tana ɗokantuwa da son sake saka Baqeer a idanunta.

Zuciyarta sam ta kasa nutsuwa, wai Baqeer dai Baqeer?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
     *NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA  GOMA SHA TARA*
Chapter 30 · 0% Book details