← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 168

Sashe 168

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watansu shida da aure sai ga Zeey da ciki, murna a wajen waɗannan ma'aurata abun ba'a magana, kusan kowa daya kamata yasan da batun cikin nan sun faɗa mishi don yadda suke ta ɗoki da murna, ita dai Umma sai dai ta kallesu ta girgiza kai idan taga yadda suke giringiɗishi da rawar kai akan cikin. Haka suka yi ta rainon cikin su cikin kwanciyar hankali kuma inda Allah ya taimaki Zeey bata yin wani laulayi sai ɗan abinda ba'a rasa ba.

*****
Asiya da Bello na zaune a layin ganin likita sun kawo ɗansu da baya da lafiya. Kallon asibitin Bello yake yi yana jinjina ta yadda zai fara biyan kuɗin asibitin gashi tun ba'a je ko ina ba ɗan abinda ya riƙo ya tafi a wajen buɗe folder. Tsaki ya saki yana jin takaicin nurse ɗin data turo su wannan asibitin da kana gani kasan na masu hannu da shuni ne. Kallon Asiya yayi yace "wai shi likitan dole sai anan asibitin za'a iya ganinshi ba zai yiwu a ganshi a asibitin gwamnati ba? Nifa bani da kuɗi kin sani daga ganin wannan asibitin kuwa kin san za'a kashe kuɗi."

A kaikaice ta kalle shi cikin ranta tana tir da wannan halin rashin babu na Bello, ace wai kuɗin asibitin ɗansu ma sai yayi mita akai kamar shi ya yanke wa talauci cibiya. A daƙile ta amsa mishi da "kana jin dai abinda nurse ɗin tace sai muyi ta zuwa wancan asibitin bamu samu ganin shi ba saboda shine babban likita a wannan ɓangaren in har muna son ganin shi dole dai nan ɗin zamu zo idan kuma kana ganin baka da kuɗi a barshi sai mu koma gida musa yaron a gaba muna kallo har Allah yayi ikon shi akan shi."
Bai ƙara cewa komai ba sai wani tsakin daya kuma yi. Kamar ance ɗaga kanka ka gani kawai sai hango Baqeer yayi akan electric wheelchair ɗin shi Zeey na daga gefenshi hannayen su cikin na juna suna fitowa daga cikin asibitin sai murmushi suke yi kana ganin su kasan basu da wata damuwa a rayuwa. Hannu yasa ya mutsitsika idon shi sai dai tabbas Baqeer ne yake gani, gaba ɗaya ya canja ya zama babban mutum kana ganin shi kaga wanda hutu ya zauna a jikin shi, ga matarshi da nesa ba kusa ba ta kerewa Asiya a komai. Juyawa yayi ya kalleta sai yaga itama ashe su take kallo idanunta sun tara ƙwallar ɓakin ciki, kaico da dana sani dafa yanzu itace kusa dashi. Tabbas ba ƙaramar asara ta tafka ba da barin Baqeer data yi gashi tun ba'a je ko ina ba Allah yayi mishi sakayya, ita ta guje shi saboda ya gurgunce sai gashi ya samu matar data fita a komai, Bellon data komawa gashi nan yanzu baya da komai sai kame-kamen rayuwa suke yi, tasan a yanzu Baqeer yayi mata nisan da har abada bata isa ta kamoshi ba.

Shima Bello a cikin ranshi yana jinjina yadda yau Allah ya mayar da Baqeer bayan duk abinda yayi mishi, yasan da ace bai butulcewa Baqeer ba da yanzu wannan arziƙin dashi za'a ci don duk wani alheri da Baqeer ya samu a rayuwa shine mutum na farko da yake fara janyowa ciki amma shine yayi mishi halin ƴan adam ya munafurce shi ya guje mishi a lokacin da yafi buƙatar kasancewar shi a tare dashi, yayi watsi da abotar shekara da shekaru son zuciya da kwaɗayi suka rinjaye shi ya aikata cin amana mafi muni ga abokin shi gashi nan yanzu inda rayuwa ta kawo shi, Asiyar da yake ganin kamar ita ce koma shi yayi mishi ƙwacenta ta zame mishi ƙarfen ƙafa don a yanzu dai da suka fara tara zuri'a bai isa yace zai yakice ta ba bayan haka ma wacce mace ce zata yi haƙurin zama dashi da wannan baƙin talaucin da yayi mishi katutu. Kiran sunan ɗansu da aka yi ne ya katse su daga tarin dana sanin da suka tafi suka tashi suka shiga ɗakin ganin likita, waiwayawa Asiya tayi ko zata sake ganinsu sai dai taga wayam babu su babu alamar su don tuni suka fice daga cikin asibitin ma.

*****
Suna zaune a mota Zeey ce ke tuƙawa shi kuma hannayenshi sun kasa tsayawa waje ɗaya sai tsokano ta yake yi. "For the last time Ya Baqeer ka bari idan dai ba so kake yi na watsar damu ba, tom," tayi mishi maganar a shagwaɓe idanunta na kan titi don bata son abinda zai yi distracting ɗinta daga tuƙin da take yi. Ɗauke hannunshi yayi kamar yadda ta buƙata sai kuma yace "tunda yarinya taga sardeden saurayi ɗan kyakkaywa gaba ɗaya tabi ta sukurkuce ta rasa nutsuwa duk da yake gurgu sai data san yadda tayi ta janyo hankalinshi ya fara sonta sannan hankalinta ya kwanta."

Rufe bakinta tayi tana dariya tace "yau kuma nan wurin ka tafi? Ai dai wallahi kasan wuce nan, abinda ma kai ka fara nuna min soyayya a fakaice daga ka ganni a gidan Dada sai ka gurguro kekenka ka wani ajiye mini gift bag har da su kyautar rose flower, sarai kuma kasan me kyautar rose take nufi don haka kai ne ka ganni ka fowler mini har sai da kayi yadda kayi na afka maka shine yanzu zaka zo kana wani zance."

"Um um fa Sweetums faɗi gaskiya, tunda kika ga wannan ɗan gurgun kika rasa nutsuwa har sai da kika nemo gidansu sannan hankalinki ya kwanta." Girgiza kanta kawai tayi tace "Allah Ya Baqeer kai ko," "Ni ko gaskiya, ai dai kin san abinda kika yi har ban san lokacin dana fara son ki ba."
Wani irin kallo tayi mishi tace "I Love You Ya Baqeer."
"I Love You too my Sweetums, Allah ya bar mu tare har tsufan mu."
"Ameen," ta amsa tana jin wani irin shauƙi yana ɗibarta.
**
Cikin hukuncin Allah Zainab ta haifi ɗanta namiji kyakkywa mai kama da uban shi sak kamar yayi kaki ya ajiye. Murna a wajen ahalinsu abun ba'a magana, ranar suna yaro yaci sunan *SALIM* saboda Baqeer yana ganin hakan kawai zai yi ya nuna mishi tarin matsayin shi a gareshi don Salim ya wuce aboki, ya tashi daga amini sai dai a kira shi da ɗan uwa. Ai kuwa yayi farin ciki sosai har ma ya rasa da bakin da zai yiwa Baqeer godiya shi kuma Baqeer yace komai yayi mishi bai biya shi tarin alkhairin shi a gareshi ba.
To muma dai mun ce Allah ya bar zumunci har Aljanna.
Suna ta shirye shiyen bikin Salim da Habi, Umma ta samu taje Umara ita da Dada wacce girma ya ƙara kamata, don Hajj tayi tsada sai dai a hankali, Baqeer yace wata shekarar zai biyawa Baba su kuma Jamila da Abu sai a hankali wata rana zai biya musu, yayi ƙoƙari sosai ganin ya haɗe kan ƴan uwanshi wanda suke uba ɗaya, wacce ke takaru ma a Makka ya sata ta dawo gida, Bashir na aiki sosai a wurinshi don ɗinki yake yi, Kamalu kuma an dage da zaman shago duk rawar kan nan an daina, gashi Badaru ya hana a bashi ajiyar kuɗi duk abinda aka siya ɗayan yaron shagon ake bawa.
Randa Umma ta dawo daga Umara Jamila da Abu haka suka mata yi girke-girke dukkanin su burinsu su faranta mata ko Baqeer ya fara kai su makka, Maryam kuwa aiki take yi sosai shi yasa yanzu ganinta ya ragu sai dai duk ƙarshen wata suna haɗuwa a wajen Umma, Hadiza ma sana’a sosai take yi na atamfofi da laces wanda  bazata ce komai ba sai hamdallah don rufin asiri kam na abinda zasu ci baya gagararsu. Badaru kam yayi sanyi don faɗa ma ba kasafai zaka ji yana yi ba dama girma yayi kawai dai rashin haƙuri ne da rashin tunani irin nashi a da, amma yanzu ya canza sosai.
Baqeer har wannan lokacin ƙafar dai bata takuwa sai dai muna fatan wata rana ya taka ko da sanda ne, zaune suke a kan kujera shida Zainab, hannunshi ɗauke da Salim, ɗaga Salim yayi ya sumbaci goshinshi yace “Sweetums ya zaki yi da baki aureni ba?”
Hular dake kanshi ta zare tasa a saman kanta tace “Baby Salim tambayar mana shi ya zai yi idan bai aureni ba?”
Kuncinta yaja yace “Bari na tashi na koma.”
Dariya tayi tace “Ka gani ko? Ban san ya zaka yi da baka aureni ba kana aiki ka gudo gida don ka ganni.”
“Faɗa mini gaskiya addu’a kika yi mini ko?”
Dariya sosai take yi yanayinta ne ya canza, wanda hakan yasa yace “What?” Yana ɗan ɗaga gira tace “Love you!”
“Love you too!” Baqeer ya faɗa yana kallon Salim ta sani sarai so yake tayi magana murmushi tayi tana jin daɗin rayuwar nan tare da fatan Allah ya barsu tare.

*TAMMAT BIHAMDULILLAH*

_A nan muka kawo karshen wannan littafi namu mai suna BAQEER, muna roƙon Allah daya yafe mana kura-kuran da muka rubuta a cikinshi, ya kuma yafe muku wanda kuka karanta kuma ya bamu Ikon aiki da duka abubuwan alkhairin dake cikinshi_

_Saƙon gaisuwa na musamman da kuma godiya ga dukkanin waɗanda suka sayi littafinmu na ƴan tagwaye, mun yaba muku kuma mun jinjina muku Allah ya ƙara muku buɗi, lafiya da kuma ɗaukaka, mun gode. Allah ya haɗamu a wata tafiyar cikin aminci_

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
Chapter 168 · 0% Book details