← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 168

Sashe 125

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*****
Yaye bargon da ya lulluɓa dashi tayi sai hura hanci take kai kace iskar gari take san shaƙewa, ta sa hannu a kwankwaso tana girgiza ƙugu tana cewa “Na rantse da Allah Malam baka isa ba ka tashi mu wuce ka sayi ticket mu tafi banga uban daya isa fa ya sani zama a ƙasar nan ba.”
Kallonta yayi cike da mamakin yanda ta rainashi yace “Wai ba na sanar dake nima koro ni aka yi ba? To in ma tafi dake muje ina?”
“Oho sai ka nemo inda zamu.” Miƙewa yayi yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin, caraf ta kamo bayan rigarshi yana ja tana ja yana ja tana ja, da ƙarfi ya fincike ai kuwa ya ƙarasa ɗaya ɗakin gudu-gudu sauri sauri yana shiga ya kulle yana haki wannan wani irin bala’i ne? To wallahi dole ya tsawatar mata ya nuna mata shi ba sa’an wasanta bane, kallon ɗakin yayi shima tayi kaca-kaca dashi, takaici da dana sani sun gama isarshi ace kai da gidanka baka da kwanciyar hankali, to shi yanzu kuɗin hayar gidan ma in ya ƙare bai san ya zai yi ba bare.

*****
Mummy tun safe har dare ta kasa cin komai, gashi sai kiran Daddy take yaƙi ɗauka, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin Zainab na Dambatta. Ita kam bata san ya zata yi ba, wayar Inna ta kira don sam ta kasa samun nutsuwa.
Inna ce ta ɗauka bayan sun gaisa tace “Inna na rasa ya zan yi Senate fa yaƙi dawowa gida.”
Inna ta sauke ajiyar zuciya tace “Halima ina tunaninki yake? Kin manta komai na rayuwarmu kece kike tsara mana yanda zamu tafiyar dashi? Ya kike neman maida kanki mara wayau? In ya tafi ki bishi inda yake mana.” Ido Mummy ta runtse kafin tace “Zainab ma taje Dambatta, ina tsoron kada su faɗa mata wani abu in ta dawo ta sanar da babanta.”
Yanzu kam hankalin Inna ya tashi tace “To kiyi maza ki yiwa tufkar hanci amma ke garin yaya kika barta ta tafi?”
Shafar fuskarta tayi tace “Ban sani ba wallahi kin san fushi take dani, Inna kinga abinda kuka ja min ko? Shi yasa nake ce miki ki bar yarinyar nan a wurinki yanzu ga abinda ya faru.”
Inna jiki a sanyaye tace “Kiyi hakuri Halima wallahi ni haushi nake ji ne in naga yaran can kun sadaukar da komai saboda su amma sam baki damu da Nabila ba.” Ƙasan leɓenta ta ciza tace “Kema Inna duk gatan da Nabila ta samu dole sai ta samu sama da hakan? Yanzu wa gari ya waya?” Shiru Inna tayi don bata san me zata ce ba, kashe wayar Mummy tayi cike da takaici don a ganinta duk da sun zauna gidansu sirrin nan ba zai taɓa fitowa ba har abada.
Miƙewa tayi ta shirya sannan ta kira drivern Daddy ta tabbatar inda yake kafin ta fito, kai tsaye driver ɗinta gidan Daddy inda suka taso ya kaita, har ta shiga falo baya nan sannan ta wuce ɗaki, yana kishingide a kan gado yana waya, yana ganinta ya kauda kai ya cigaba da wayarshi wanda tana ji ma tasan da Deputy Governor ne daga yanda yake yi mishi magana, zama tayi a gefenshi tana ɗan matsa mishi kafa, bai ko kalleta ba ya cigaba da wayarshi sai da suka gama sannan ya kashe, kusa dashi ta dawo ta jawo hannunshi tana matsawa tace “Senate please!”
Wani irin kallo yayi mata yace “Ni Halima? Ni zaki munafurta? Shekara ba ɗaya ba ba kuma biyu ba ashe ke a soko kike zaune dani, wallahi ke kin san da badon ban san career ta siyata ta sake gurguɗewa ba da kin tafi gidan ku, amma nayi saki ɗaya bana son sake wani.”
Yatsa tasa da sauri ta rufe mishi leɓenshi, hawaye ne suka ciko mata tace “Senate kana tunanin a son raina na ɓoye maka? Wallahi a’a babu yanda zanyi ne, na daɗe ina son sanar da kai amma ban san ta ya zan fara ba, am so young sanda abin ya faru sannan ƙaddara ce ta afka min wanda har yanzu zuciyata ma tariyo mini abinda ya faru, in baka manta ba sanda Aunty ta fara barina ina shigowa gidan ku ba tausayi na bane ya kamata? Har nake zuwa ina tayata yan aikace aikace, ka tuna da kyau Senate a wani hali nake a lokacin?”
Kallonta yayi don bazai iya tunawa ba amma yasan tabbas mahaifiyar Zainab ce ta jawota jikinta har wani sa’in take kwana a gidan saboda gidan da suke zaune ɗaki ɗaya ne shi yasa a lokacin da yace zai aureta aka dinga ganin wai cin amana zai yi wanda shi kuwa yasan so ne sannan da kyawawan halayenta da kuma guarantee da yake dashi na wanda zai kular mishi da family ɗin shi ya kuma ƙarfafa mishi gwiwa, abu mafi mahimmanci kalmar da ya fara girmama ta tsakaninsu sanda tace mai tana ji a jikinta zai zama governor nan gaba.

(Hmmm mudai kam bamu da bakin magana🥴)

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA BAKWAI*

{77}
Chapter 125 · 0% Book details