Sashe 145
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Baqeer tunda Zee ta tafi ya turo ƙofa ya rufe ɗakin shi, abincin data bashi ya tura gefe don ko alamun yunwa ma baya ji, ko idanuwanshi ya runtse sai ya dinga ganin Zee tana yi mishi murmushi, hannu yasa ya ɗan matsa saman girarshi sannan ya janyo takarda ya fara sketch, yi kawai yake yi kamar wanda ake zubowa basirar, ji yayi hannunshi na ɗan zafi hakan yasa ya ajiye pen ɗin tare da dafa saman kanshi dake ciwo, maimakon ya daina sai ya janyo shaddar daya siyo kawai ya bajeta ya sauka daga kan kenenshi ya fara yankawa, sai daya gama fitar da komai sannan ya ajiye scissors ɗin tare da duba agoggo, magriba yaga tayi ya turo kekenshi ya fito.
Dada tana ganinshi tace "Anga dama an fito? Banda shirme in kana sonta da gaske ai ba haƙura zaka yi ba, sannan ko kunya ka shige ɗaki ka barta ta tafi gida da kanta." Shi dai bai ce komai ba sai bandaki kawai daya wuce. Bayan yayi sallah ya ji zuciyarshi ta kasa nutsuwa sunan Zainab ya kalla cike da damuwa ya danna kira ai dai ko ba komai ta cancanci kulawar shi don yadda ta bar gidan nan yana tsoron wani abun ya sameta, da sauri ya kashe kafin wayar ta shiga ya kifa kan wayar tare da sake wani dogon numfashi, yadda yake jin zuciyarshi na zafi ko Asiya da suka dade tare bai ji rabin abinda yake ji akanta ba bayan sun rabu. Wayarshi ce yaji ta fara ƙara da sauri ya ɗauka yana fatan Allah yasa Zainab ce, ga mamakinshi Umma ce yanayinshi kaɗai zaka san ba haka yaso ba sai dai Umma ce ita kanta yana son jin muryarta. Ɗauka yayi bayan sun gaisa cike da kulawa tace "Baqeer dama Zainab sonta kake yi?"
Yawun bakinshi ya haɗiya kafin yace "Ba dai Baba ya huce akan ki ba? Umma don Allah ki kwashe kayanki daga gidan nan zan zo na ɗaukeki," yayi maganar a ɗan hasale. Cikin sanyin murya tace "Ba maganar da muke yi kenan ba, taya zaka nemi janyowa kanka magana Baqeer? Kafi kowa sanin wanene Alhaji Sulaiman ka kuma san abinda zai yi akan yaran shi, ka sani ko da ƙafafunka ma ba baka Zainab zai yi ba." Baqeer ji yayi wani abu ya tokare mishi a maƙoshi, mikin da yake ƙoƙarin dannewa na neman tasowa, muryarshi ce ta ɗan sarƙe yace "Umma ban sani ba wallahi, sanda kuma nasan ita wacece nayi nisa da har nake jin zan iya gwada sa'a ta, duk wannan lokacin a matsayin ƙawar Maryam kawai na santa, ta canza kama sannan ban ma taɓa kawowa Zainab dana sani zata kula dani haka ba. Umma ita ce wacce a dalilinta nake zaune cikin kwanciyar hankali yanzu, na tabbatar Allah ne ya kawo min ita cikin rayuwata a lokacin da nake buƙatar wanda zai fahimceni, wanda zai nuna min hanya ya hanani faɗawa wani hali, Umma tunda nazo gidan Dada nake roƙon Allah ya ɗauki raina na huta sai dai ita ce ta nuna min kuskurena ta kuma sani fara sana'ar da nake yi yanzu, ni....ni!" Kasa cigaba da magana yayi kawai sai ya runtse ido yana haɗiyar wani abu mai ɗaci da yaji ya tokare mishi maƙoshinsa. Umma tausayin ɗan nata ya kamata, lallai da ta sani tun sanda tasan Zainab ce data tuntuɓeshi kila da lokacin bai mato a sonta kamar yanzu ba don kalamanshi kaɗai sunsa tasan yana sonta sosai. Murmushi yayi na yaƙe yace "Baba yayi halin nashi ko?"
Cike da tausayin ɗan nata tace "Babu komai ni faɗanshi baya damuna, kai kuma In Sha Allahu Allah zai dubeka ya baka lafiya zai kuma baka wacce iyayenta zasu soka."
Murmushi kawai yayi don Ameen ɗin ma ji yayi ya kasa cewa don in dai aure ne to da Zainab kawai yake son zama, ɗan shiru yayi kafin yace "Don Allah Umma karki sadaukar da farin cikin ki saboda ni, babban burina a duniyar nan na faranta miki shi yasa babu amfani na ganki cikin ɓacin rai, ki bar gidan kamar yadda yace miki kizo mu zauna, ni hankalina zai fi kwanciya in kina nan zan kuma fi maida hankalina wurin sana'a ta, sau da dama barin Dada ita kaɗai baya mini daɗi ta kawo girman da take buƙatar wani tare da ita," ya ƙarasa maganar yana rage murya zuwa rashin jin daɗi. Ta sani sarai duk abinda ya faɗa daidai ne hakan yasa tace "Shikenan zan yi tunani skai." Cike da jin daɗi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Number Zainab ya sake dubowa ya kwantar da kanshi a bayan wheelchair ɗin yana tunani, sai dai baya ji yana da ƙarfin iya kiran ta.
****
Yau kwana huɗu kenan da tafiyar Zee Ɗambatta sosai suka ƙara shakuwa da Ummi da Inaya, shi kanshi Mubashir da bashi da yawan magana sosai sai da Zee tayi ƙoƙarin janshi a jiki, ko waya Abba yayi haka Inaya zata yi ta bashi labarin abubuwan da suka yi da Aunty wanda abun ba ƙaramin daɗi yake yi mishi ba, yana son Ummi sosai shi yasa yake jin daɗi ganin tana cikin farin ciki, yaso Ummi da farko sai dai bai sanar da ita ba saboda shi abokin yayanta ne, in yazo wurin abokinshi yana ganin Sulaiman yazo zance, wannan dalilin yasa bai sanar da kowa son Ummi da yake yi ba, yaja bakinshi yayi shiru har tayi aure shima yai aurdnshi, sai dai aurenshi bai daɗe ba matarshi ta rasu a wajen haihuwa ta koma ita da babyn da ta haifa, wannan dalilin yasa ya ajiye batun aure ya maida hankali wurin aikinshi, shekarar matarshi huɗu da rasuwa auren Ummi ya mutu, yazo Ɗambatta hutu ya ganta wannan dalili yasa ya sanar da yayan Ummi don baya son ya sake bari ya huce, bayan aurensu Ummi ta haifi Mubashir daga nan kuma sai ta dinga ɓari babu haihuwa, ƴan uwanshi suka fara canza mata saboda suna son yayi aure suna ganin aikin da take yi ne kila yasa ma cikin yaƙi zama. Ƴar uwarshi suka bashi akan ya aura yace fir ba zai aureta ba, sai dai Ummi ta nuna mishi rashin dacewar hakan, daga baya ya amince da auren sai da aka zo daf da auren suka gane ashe akwai wanda take so, auren shi kawai zata yi saboda yana da kuɗi amma ba wai don ta rabu da saurayinta ba. Ba ƙaramin ɓacin rai ya shiga ba yaci zarafinsu akan kar wanda ya kuskura ya ƙara yi mishi maganar ƙara aure matarshi ta isheshi baya buƙatar ƙari.
Tun daga nan Ummi ta samu salama suka daina ƴan maganganu, daga baya Allah ya bata cikin Inaya, wanda ganin tasha wahala sosai wajen haihuwarta yasa yace to haihuwar ta isa haka su biyu sun isa, da kanshi ya zaɓawa Inaya sunan Zainab don ya san tsananin son da take yiwa ƴaƴanta kawai dai kawaici take yi take kauda kai.
Shi yasa yanzu ya tabbatar Ummi na cikin farin ciki wanda hakan shi kuma ba ƙaramin daɗi yake yi mishi ba.
Yau Ummi ce a kitchen ita da Zainab da Inaya, aikin girki ake taya Ummi, sai dai Zainab duk ta zama ƴar kallo tana tsaye tana ganin yadda Inaya ke taya Ummi yanke-yanke amma ita tana farawa Ummi tace ba haka ba.
Baki ta turo tace "Ummi to wai ita wannan ƴar mitsilar ya aka yi take iya yin wannan yankan ƙanana?"
"Kema haka nan zaki koya kuma ga naki nan kada na kuskura naga kinsa Inaya ta miki." Baki ta turo ta shiga daddagewa tana yankawa, ganin ta yanka daidai yasa ta daka wani tsalle ta kalli Ummi tace "Ummi Ummi kalla, wallahi ni nayi." Kai kawai ta girgiza ganin yadda take murna kamar wacce tayi wani abun kirki.
Sosai Ummi ke ƙoƙarin janta a jiki da kauda mata tunanukan da take yi, sai dai duk sanda tazo kwanciya sai tayi kuka ta gaji saboda tunani da rashin Baqeer tana ji son Baqeer ya zama jinin jikinta, tunda tazo Daddy bai nemeta ba in ta kira kuma yana amsa gaisuwarta yake kashe wayar ko dama baya bata suyi magana, Mummy kuwa ko waya basu sake yi ba balle da Ummi ta bata labarin yadda ta shiga jikinta dasu har ta auri Daddy wannan dalili yasa ta ƙara tabbatar da makircin Mummy.