Sashe 98
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Zeey kam da ƙyar ta samu ta lallashi Nabila ta daina kuka hakan yasa ta koma ɗaki takaici yasa ta ɗau key kawai tabar gidan tana ganin kiran Mummy amma taƙi ɗauka, Baqeer kawai take skn gani amma tsoron haɗuwarsu da Maryam take, ganin yamma ce yasa ta ɗauki waya tayi mishi text tace “Wani abu ya riƙeni kaɗan amma zanzo, suna nan dai ko?”
Reply ya mata akan sun tafi, wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta sauke tare da yin hamdallah sannan taja mota tayi gidan idanunta taf da ƙwalla, sam bata son wannan hatsaniyar dake faruwa tsakanin Mummy da Nabila, ace ƙanwarka amma kullum cikin faɗa? Waya ta ɗauka ta kira Nabila akan taji ya take ciki sai dai me? Nabila na dauka ta cigaba da kuka tana cewa “Zeey na shiga uku ina ji ciki ne dani kuma cikin…..”ɗif kuma sai komai ya tsaya kamar an ƙwace wayar, gaban Zeey ne yayi wani irin faduwa da sauri taja gefen titi ta tsaya tare da dafa saman goshinta, ciki? Ciki? Ciki kamar ya? Jikinta ne kawai yake rawa sam ta kasa samun nutsuwa, wayarta ce ta fara ƙara ganin sunan Baqeer yasa ta ɗauka da sauri tana sauƙe ajiyar zuciya “Dama Dada ke cigiyarki tana son jin ko zaki zo?” Numfashi kawai yaji tana saukewa wanda nan da nan hankalinshi yayi mugun tashi yace “Zainab! Menene?” Kawai ji tayi ta kasa magana, nan fa hankalinshi yayi mugun tashi yace “Kina ina?” Hawayenta ta share tana son yin magana ta kasa, “Yi mini text ɗin inda kike.” Yana kaiwa nan ya kashe wayar, ajiye takardun da yake zane yayi ya fara tura kekenshi cikin sauri, Dada na zaune tana cin abincin da su Hadiza suka dafa musu tuwo miyar zogale tana ci tana jin radio gefenta yarinyar maƙota ce da ta shigo tayata wanke-wanke itama an zuba mata tuwon tana ci, da mamaki take kallonshi tana cewa “Kai kuma sai ina?” Yanda taga yana tura keken da sauri ne ya bata mamaki yana tafiya yana cewa “Ina zuwa Dada.” Da kallo ta bishi tana fatan Allah dai yasa lafiya….
Baqeer adaidaita ya tara yana jin gaba ɗaya hankalinshi ya tashi, meya sameta? Bayan yarinya ce da kullum fuskarta ke ɗauke da farin ciki da walwala? Ba dai Junaid bane? Haka ya isa inda ta kwatanta mishi ta text duk zuciyarshi babu daɗi, gaban motarta yace a ajiyeshi, kallon juna suka yi shi da ita dake cikin adaidaita ita tana mota, hawaye ne taji sun gangaro mata, da sauri ta fito ba tare da tace komai ba ta fito da wheelchair ɗin haka ya fito ya shiga ta turashi jikin mota sannan ya shiga ta sake nade wheelchair ɗin tasa a bayan mota sannan ta dawo ta zauna seat ɗin driver, kallon juna su kayi ga mamakinta kawai ta rasa abin cewa sai rauni da zuciyarta ke yi, anya bata da matsayi a zuciyar Baqeer kuwa, in ba haka ba taya zaizo daga sanar dashi? Kallonta yake yi kafin yace “Me ya sameki?”
Hawaye ne suka zubo mata wanda tana ganin damuwa ƙiri-ƙiri cikin zuciyarshi yace “Menene? Junaid ne?”
Wani kallo tayi mishi ta girgiza kai, yace “To wanene?”
Kanta ta kwantar jikin kujera tana kallonshi tace “Ya Baqeer ban san ya zan yi ba, bana so naga Mummy na samun matsala da ƙanwarta sai na dinga ji kamar komai dalili na ne, don Inna tasha faɗa mini cewa nice na rabasu.” Bai san kan zancen da take yi ba sai dai ya fahimci abin daga gida ne ya kuma gane inda matsalar take, yace “In ƙanwarta ce ko sun yi faɗa zasu shirya, Umma ma tana samun saɓani da ƴan uwanta amma suna shiryawa.”
Hawaye ta goge tace “Matsalar ina ga ta yanzu ba mai shiryuwa bace, sannan in Daddy yasan abinda ƙanwarta tayi Mummy ban san yadda zata yi ba…..” ta ƙarasa maganar tana hawaye, idanunta tasa cikin nashi wanda suka cika taf da ƙwalla kana kallonshi kaga damuwarta tsantsa a ranshi, yace “Meya haɗa laifin ƙanwarta da nata? Sannan in har laifin babba ne ku samu kakanni ko magabata suyi magana kafin abun ya girma
Wani abu ta haɗiya tana kallonshi yaji tace “Ba ita ta haifemu ba ni da yayana, shi yasa danginta basa sonmu.”
Daga Umm Asghar har Ayusher kallonta suka yi ,yau me muke ji? Mai karatu kai fa? Ka taɓa kawo haka?
Ku biyo mu wasa farin girki🙌🏻
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Muhd Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN*
{60}
Cike da mamaki Baqeer yake kallonta ga kuma wani tausayi da take ƙara bashi ganin yau ce rana ta farko da yake ganin hawaye a fuskarta haka, zuciyarshi ce ke ingizashi akan yasa hannu ya share mata amma inaa ba zai iya ba, tissue ɗin dake ajiye tsakanin inda take da inda yake yasa hannu ya ɗauka, miƙa mata yayi ta ɗauki biyu ta goge fuskarta tana murmushin yaƙe tana cewa "Ya Baqeer am sorry....."
Katseta yayi da cewa "Ki koma gida kiji me ke faruwa tukunna and then make a decision." Cike da rauni ta kalleshi sannan ta ɗaga mishi kai alamar to, shiru suka ɗan yi sai dai shi zuciyarshi cike take da tambayoyi amma baya son ya juye mata su yanzu saboda abinda ke damunta, cikin sanyin jiki yace "Birth mother ɗin ku fa?"
Kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace "Tana raye sai dai ta sake wani auren a garinsu, ta sake haihuwar yara mata biyu." Ta ɗago tana kallonshi idanunta taf da ƙwalla tace "Amma na daɗe ban ganta ba kuma itama ba wai ta damu da mu bane."
Shima idanuwanshi na cikin nata yace "Ita ta faɗa miki bata damu daku ba?"
Yanayin kallonta ne ya canza ta maida idanunta ƙasa tana goge fuskarta tana cewa "Akwai abinda ba sai an faɗa ba kake ganewa, sannan ina da Mummy na har cikin raina a matsayin wacce ta haifeni nake ɗaukan ta don ƙaunar da take yi mana ta dabance a kanmu ta haƙura da neman haihuwa tace mu kaɗai mun isheta rayuwa ba sai ta nemi wasu ba.” Ta ƙara kallonshi sannan tasa kanta a jikin stearing motar wani shauƙin ƙaunarshi na ƙara ratsata tace “Kana ganin duk da haka sai na dinga bibiyar wacce bata damu dani ba?”
Ga mamakinta gani tayi ya ɗaga mata kai alamar eh, mamaki ne ya kamata tace “Why?”
“Saboda ita ta haifeki, baki san uzurin ta ba baki san me yasa bata zuwa ba, sannan don tayi aure ta haihu ba shi zai sa ta daina sonku ba.”
Baki ta ɗan taɓe tace “Hmm baka san ta bane shi yasa, matar da ko waya bata yi mana taji ya muke? Ya Baqeer mu bar maganarta please, ni yanzu tsorona kada Mummy ta shiga wani hali a dalilin Nabila.”
Kallonta yake kawai bai ce komai ba, sai ma gani tayi ya maida hankalishi waje, baki ta turo tana neman sake zubo da ƙwalla, daidai nan ya waigo da sauri yace “Please kukan nan ya isa haka nan, bari na sauka kamar yadda nace ki koma gida kiji menene ya faru tukun.”
Baki ta turo tace “Bari na kai ka gida sai naje.”
“No kar ki damu zan hau adaidaita.” Ido ta zuba mishi wanda har ya kalli waje ya sake kallonta yace “Me?”
Kallo take mishi na sakalci da harara tace “Allah a’a ba saboda ni ka fito ba? Ni naga saurin zuwanka ma Ya Baqeer faɗa mini gaskiya a ruɗe ka iso ko?”
Gyaran murya yayi yana ɗan gyara kwalar rigarshi cikin son ya waske yace “Dama ina waje sannan ni bana son harkar kuka.”
“Waje a ina kenan?” Kallonta yayi yace “Ba sai kinji ba uzuri na ne.”
A shagwaɓe tace “Ya Baqeer please ka bari na saukeka Allah it's not easy shiga adaidaita da wheelchair,” ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya alamar lallashi, kai ya ɗaga alamar to, murmushi ta saki shima bai san sanda ya saki murmushi ba yana ɓoyewa don kar ta gani, motar ta kunna sannan suka fara tafiya, shiru suka ɗan yi kaɗan, baya son damunta da tambaya amma yana son yasan me yake faruwa a rayuwarta, ashe itama tana da nata matsalolin kawai dai bata nunawa ne, katse mishi tunani tayi da cewa “Baka fada minu me *ASF* ɗin yake nufi ba.”
“Dama an taɓa bada assignment a faɗi amsa ba tare da an gwada ba?”
Ɗan kallonshi tayi tana dariya kaɗan tace “To ai haka ake yi in aka bada assignment a school ko baka san answer ba za’a sanar da kai sannan ba kace zaka fada mini ba?”
“Yaushe kenan?”
“Kai lallai ma Ya Baqeer Allah wayau zaka yi mini.” Hannunshi yasa a aljihu bai ce komai ba, wata nutsuwa yake ji na ganin ta saki ranta.