Sashe 114
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Badaru na zaune a kasuwa wani abokin shi da suke harkar kasuwanci tare ya kawo mishi ziyara. Bayan sun gama gaisawa yace "Mallam Badaru ashe yaronka ya fara gina filinshi dake unguwarmu babu labari? Nace to Badaru mantawa yayi bai faɗa min za'a fara ginin ba bayan muna haɗuwa kusan kullum a kasuwa, ai irin wannan sai ka sanar dani yadda zan saka muku ido sosai a harkar ginin ba wai naga an fara ba bayan tare dani aka yi duk wasu shige da fice har Allah yasa aka sayi filin." Tunda ya fara magana Badaru yake kallonshi fuska ƙunshe da mamakin jin cewa wai an fara gini a filin Baqeer. To ta yaya ma za'a fara gini a wajen ba tare da an sanar dashi ba? Kada dai ace Kamalu sayar da filin nan yayi shine har aka fara gini bai sani ba. Ai da yin wannan tunanin ya miƙe zumbur ya zari makullin motarshi ya fice daga shagon ba tare daya tsaya yayi wa abokin nashi bayani ba duk kiran da yake ƙwala mishi kuwa bai sa ya tsaya ba sai ma sauri da yake ta faman zambaɗawa yana fatan yaje gida ya iske Kamalu yau babu me rabasu sai dai Allah.
Kamar wanda zai tashi sama haka ya kwaso mota a guje, hukuncin Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya. Ko tsayawa ya daidata parking motar bai yi ba ya fita da sauri har yana cin tuntuɓe da wani dutse Allah dai ya kiyaye bai faɗi ba. Yana shiga cikin gidan da Abu ya fara cin karo ai kuwa ya kai mata damƙa yace "ina Kamalu yake? Ina yake nake tambayarki?"
Jiki na rawa don ta tsorata da yanayin data ganshi a ciki fatanta dai Allah yasa ba shagonshi ya ƙara zuwa ya ɗebo mishi wasu kayan ba. "Mallam lafiya?"
Wata uwar harara ya zabga mata yace "ina fa lafiya ɗan iskan yaron nan ya kassarani yaje ya sayar da filin nan har an fara gini a wurin."
"Kamalun ne ya sayar maka da fili Mallam? To yayi me da kuɗin?"
"Oho nima na sani zai wuce yawon iskancin shi zai tafi da kuɗin."
"Gaskiya Mallam ka daina cewa shi ya sace maka fili tunda dai ba ganinshi kayi ya ɗauka ba, ko kuwa wani ya gaya maka ya ganshi lokacin da ya ɗauki takardun filin?"
Tsaki yayi yace "Har sai wani ya faɗa mini, ki gaya mini duk gidan nan akwai wani ɗa daya gagara ne bayan shi? To wallahi ki faɗan gaskiya ko na tsine mai." Shiru tayi dan mamakinshi ya hanata magana, sai cewa yayi "Kin gani kema kin san gaskiya."
Umma ce ta fito daga ɗakinta jin abu na neman kaiwa ga tsinuwa yasa ta fito tace "Takardun fili dai ni na ɗauka na kaiwa mai filin ya sayar yayi amfani da kuɗin."
"Ke kika sace mini takardun filin fa kika ce Fatima?"
Girgiza kai tayi tace " Haram, ni ban sace maka komai ba takardar filin Baqeer na ɗauka don nasan ko nace maka ka bani ba bayarwa zaka yi ba kuma mai filin yana da buƙatar kayanshi shi yasa ni kuma na ɗauka na kai mishi."
Baki buɗe yake kallonta don ya rasa wane mataki ya kamata ya ɗauka a kanta. "Habawa ashe shiyasa kike da kuɗi? Kudin sata kike ce to wallahi Fatima ki karɓo min takardar filina in har ba barauniya kike san zama ba, idan kuma ba haka ba wallahi zan yi matuƙar saɓa miki akan takardun nan zaki iya bar min gidana."
Murmushi tayi tace "Filinka ko na Baqeer kuma idan kace na bar maka gidanka sai me tunda ka iya korar ɗan cikinka bayan ka gama cin moruyarshi ma bare ni da ka sameni da girmana," daga haka tayi shigewarta ɗaki ta barshi anan da sakakken baki.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
Da
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA TARA*
{69}
Abu bata san sanda dariya ta ƙwace mata ba, ganin wani mugun kallo da Badaru ya watsa mata yasa tayi saurin cewa “Malam to yaya? Kamalu dai sai ka nemi yafiyarshi watakila ma atamfofin su ke sata ba’a sani ba.”
Ai kuwa tana kaiwa nan ya hayayyaƙo mata don dama a wuya yake saboda kalaman Fatima, a fusace yace “Gurgun ne kike nufi zai je kasuwa yayi sata? Ko kuwa kina son cemin shi yaron shagon nawa bai san Kamalu ba? In Baqeer ɓarawo ne shima Kamalun ɓarawo ne aikin banza ka haifi yara taron ɓarayi a gida ni dai kam banji daɗin haihuwa ba.” Jin yanda ya rufeta da masifa yasa tayi sum-sum ta shige ɗaki, maimakon ya koma ciki sai ya nufi ɗakin Fatima yana masifa “Kina ina munafukar banza da wofi, ni Fatima har kin yi idon da zaki yi mini sata? Ni? Ni?”
Tana daga cikin ɗaki ko motsi bata yi ba yi tayi ma kamar bata san me yake yi ba, ai kuwa ya ƙaraso cikin dakin yana hayagaga yana cewa “Eh lallai idanunki sun isa yanka, to tashi maza ki bar mini gida na.” Maimakon ma ta bashi amsa gani yayi ta janyo hijabi ta saka ta jawo akwatin ta a ƙasan gadonta na ƙarfe tana neman watsa kayanta ciki, wani tunani ne yazo mishi in har ta tafi shikenan bashi ba kuɗin filin nan don ya tabbatar kuɗin na hannunta ko Baqeer amma ko yaya in ya ajiye Fatima ai dai ko banza zai iya ƙwace kuɗin shi a hankali, wani kallo yayi mata kafin yace “Kina sa ƙafa kika bar gidan nan Allah ya isa.” Da mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a idanuwanta ta kalleshi, idanuwanshi sun yi jaa saboda tsabar masifa ya sake yi mata wani muzurai don ta ƙara shakkar shi sannan ya fita, kai ta girgiza don baƙin ciki ya isheta taso ta tarkata ta tafi duk da itama bata son tafiya har sai Baqeer ya zama abinda Badaru da kanshi zai yi ƙwallar da na sani, amma da zaran ta tattara ta koma wurin Dada tasan neman faɗanshi kaɗai sai ya sa ya bita har can, sannan wannan kishiyoyin nata masu gulma tasan bazasu barta ba haka zasu yi ta sawa ana musu leƙen asiri, amma da tuni itama tayi yaji don ba abinda yake zaune da ita a gidan.
Badaru kam ɓacin ran da yake ciki ne yasa ya fito waje, yana ƙoƙarin fita Kamalu na shigowa, daga ɗan gefe kawai ya raɓa yana neman wucewa ba tare da ya yiwa Badaru magana ba, kamar ya shaƙo wuyanshi ya kifa mai mari yake ji amma baƙin ciki ya hanashi gashi yana tunanin haukar yaron nan kar yasa ya ƙara bigeshi wanda ya tabbatar a rashin kanshi zai iya aikatawa, shi dai kam bai yi sa’ar yara maza ba, duk yanda yake kulafucinsu gashinan duk sun zo babu wanda yayi mishi rana.
Tafiya kawai yake yi don bai masan inda yake saks ƙafarshi ba, yanzu filin nashi da gaske Fatima ta sace? Mai zai yi mata da zai ƙuntata mata? Don wallahi bataci bulus ba, dama ɗanta ya cireshi daga sahun yaranshi don shi kam babu abinda zai yi da Baqeer to yaranta mata ma aikin banza duk ba wani jin dadi suke yi ba, ƙwafa yayi yana waigawa suka haɗa ido da Suleiman Ƙaraye yana zaune a cikin mota a baya ya sauke glass yana sauke wani irin numfashi na ɓacin rai, don yau shi kaɗai yasan ɓacin ran da yake ciki wanda yake jin ƙwaƙwalwarshi ma ta kasa tunani mai kyau, wani kallon-kallo suka yiwa juna sannan yace wa driver ya hanzarta su tafi bai son tsayuwa a wurin. Badaru ya ƙara tamke fuska ya juya ya cigaba da tafiyarshi abun takaicin ma shine sai yake ganin kamar kowa yana cikin farin ciki ne banda shi.