← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 168

Sashe 54

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Junaid ya sauka a garin Kano ya wuce gida inda ya huta yayi bacci, tashi yayi ya watsa ruwa sannan yasa riga t-shirt da wandon jeans ya fesa turare sannan ya fito, a falo yaga Mamy ta jera mishi abinci, murmushi yayi sannan ya zauna yana cewa “Mamy inyi maza-maza dai in kawo miki suruka kema ki huta.”
Dariya tayi tace “Ah to ka dai ce kana dawowa zaka kawo mana Zainab.”
Wayarshi ya kalla dake ƙara ya dagota tare da kallon Mamy yace “Gata ma ƴar halak.” Ya ƙarasa maganar yana saka wayar a kunnenshi.
“J ya? Ka iso?”
“Duk hankalinki dai da alama yana kaina, hope anyi mini shirye-shirye ne shi yasa kike jirana.”
Dariya tayi kaɗan tace “Kada ka damu in muka je kaga mara lafiyan daga nan zan kai ka yawo.”
Wani sanyi yaji a ranshi da alama ita ma ta fara cireshi daga bangaren aboki yace “Shikenan ki bani zuwa bayan la’asar In Sha Allahu.”
“Shikenan zan zo sai mu wuce.”
“Wai zuwan ma ɗauka na za ayi? Ki bari zan zo na ɗaukeki.”
Ajiyar zuciya tayi tace “Kai da kasha hanya? Kai dai ka shirya zan zo.”
Da yake yasan dagiyar Zeey yasa yace to kawai, Nabeela dake tsaye tana gyara drawer ce ta kalleta tace “Waye kuma J?”
Zeey ta kwanta akan gado tana ɗan wasa da kafarta tace “Junaid.”
Da mamaki tace “Junaid dai naki?”
“Nawa ko nasu? Shi dai ya dawo yau.”
Kallonta Nabeela tayi cike da zargi da sauri Zeey tace “Kada ma ki fara babh abinda ke tsakaninmu.”
Dariya ta saki tace “Wannan karan kin bani mamaki kece yau kwananki biyu a gidan nan?”
“Ni kaina mamaki nake bawa kaina, don ma yanzu mitar Inna ba wani bani haushi yake ba.”
“Dama can bai kamata ya baki ba tunda kin san halinta.”
Ajiyar zuciya tayi tace “Matsalar bana iya yi mata shiru ne.”
“Dama ina zaki mini shiru kina kwance kowa yana aiki banda ke?” Suka jiyo muryar Inna data shigo ɗauke da kayan gugar da aka kawo, ta miƙawa Nabeela tana kallon Zeey dake kwance akan gado tana magana tana cin soyayyiyar cashew, ko a jikinta ma.
Fita tayi hakan yasa Zeey ta miƙe tace “Bari nayi wanka fita zamu yi da Junaid.”
Kai kawai Nabeela ta ɗaga ita kuma ta shiga toilet, ƙwalawa Nabeela kira tayi wai ta miƙo mata towel ta manta bata ɗauka ba, ɗauka tayi ta miƙa mata sannan ta cigaba da aikin, tana mamakin Zeey sam halinta na ko in kula abinda ke gabanta kawai shi take yi amma ragowar ba damuwarta bane, gadon ta gyara sannan ta ɗauko tsintsiya ta share ɗakin ta fito falo inda ta samu Inna zaune tana sauraren radio, kallonta tayi tace “Inna me za’a dafa?”
Innan ta kalleta tace “Me kike gani? Ni ko menene ma bani da matsala.”
“Ko muyi shinkafa da wake?”
Kai ta ɗaga alamar 'eh' kafin tace “Allah yayi miki albarka ya kawo miki mijin da zaki aura wanda zaki ji daɗin shi."
“Ameen Inna,” ta faɗa cikin jin daɗi. Inna tana zaune tana binta da ido har ta shiga kitchen, ajiyar zuciya tayi don tana tsananin tausayin Nabeela.
Zeey kam kaya ta saka ta fara jawowa tana tunanin wanda zata saka, atamfa ta ciro doguwar riga irin buba ɗinnan, tasa ta ɗaura ɗankwali irin na Zarah Buhari, nan fa ta fito cass tasa turare, kallon kayan data cire tayi kamar baza ta kwashe ba sai kuma ta ɗauke tace “Kafin yanzu a hauni da masifa.”
Jaka ta ɗauko ta ɗauki wayarta, falo ta zauna gefen Inna tace “Inna wai ni kam radio ɗinnan kunna shi kawai kike yi amma dai ba saurara kike ba ko?”
“To ko ma dai menene ai kunnena ne ko?”
Baki ta taɓe, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka da sauri ta fashe da shagwaɓa tace “Mummy Allah Inna ta takura mini.”
“Kin gani ko? Ki tattaro ki dawo don ni har yanzu mamakin zaman nan naki nake yi.”
Tana kallon Inna dake harararta tace “Wasa nake yi wannan karon Inna lallaɓani take yi? Ko Inna?”
“Ahaf ita tasan bazan lallaɓaki ba ai, tunda su sun gama sangartaki.”
Dariya tayi tace “Mummy gaba ɗaya Inna fa bata gajiya da mita.”
Mummy ta sauke ajiyar zuciya tace “Daddynki ma ya ƙosa ki dawo gidan babu daɗi da ba kya nan.”
Tana murmushi tace “In Sha Allahu Mummy, kema kin san ina missing ɗinki, love you Mummy.”
Nan suka yi sallama Inna tayi tsaki tace “In ma roba ne can ku kuka sani.”
Zeey tasa dariya sosai tace “Love you ake cewa.”
“Can muku nace kuce samira ko tangaran ma bai dameni ba.”
Miƙewa tayi tana cigaba da dariya don Nabeela dake kitchen ma dariya take yi musu, Zeey ta fito ta shiga mota ta fita har lokacin ta kasa daina dariya.
Inna ce ta bita da harara, Nabeela ce ta leƙo Inna tana kallonta tace “Ki tabbatar in zata koma kun koma tare, gwara kije can ki huta ni in Basira ta zo tayi mini abinci na ya isheni, sannan ki rage wannan saurin fushin naki.”
Kai ta ɗaga sannan ta koma kitchen ta cigaba da girkin.

*****
Gidan su Junaid ta nufa bayan sun yi waya bai dade ba sai gashi ya fito, tunda ya shiga mota ya zuba mata ido yana jin ƙaunarta na shiga mishi rai sosai, kallonshi tayi itama tace “J kallon ya isa haka nasan baka saba ganina da atamfa ba duk shine.”
Ido ya lumshe sannan ya buɗe, a kyau bai kai Baqeer ba amma da yake ɗan gayu ne shi sosai mai kuɗi a haka sai kaga ya fishi, sai saje daya tara a fuskarshi dake ƙara mishi kyau, girman ido ya ɗan rage irin yanda yake jan hankalin mata yace “Zeey you just look different, sai nake jin kamar yau na soma saninki.”
Ido ta ɗan juya kaɗan tace “Junaid please kada ka sakani dariya ba wani different kawai dai ka ganni ne bayan shekara of course dole kaga na canza.”
Mota ta tada tana cewa “Ni dai Allah yasa baka ma Mamy magana ta ba.”
“Guess?”
Harararshi tayi tace “Ya Allah ban san ya zan yi da kai ba.”
“Amincewa kawai zaki yi muyi aure shikenan komai yayi daidai.”
Murmushi tayi tace “Me nace maka?”
“Sai wanda in kika ganshi zuciyarki bata nutsuwa, sai kinji butterflies na yawo a cikinki in ya matso kusa dake bla-bla-bla ba dai har yanzu yarintar na nan ba?”
Kafaɗa ta ɗaga tace “Call it whatever you want ni dai haka nake ra’ayi.”
Idanunshi na kanta yace “Kin san in na matso kusa dake you will definitely feel it?”
“Problem ɗin shine ni bazan bari ka matso ɗin ba sannan inka matso ma abotar ta ƙare daga yanzu.”
Dariya yayi abinda yasa yake son Zeey kenan bata shakka ba kuma ta magana don kaji dadi abinda ke ranta kawai take faɗa.

*****
Baqeer wannan karon shine karo na biyar daya duba agogon hannunshi, tun  jiya Dada ke cewa zata zo bai kulata ba gashi har huɗu da rabi babu ita ba labarinta, ba dai haushi taji ba akan rannan ya tafi ya nuna bai san nemanshi taje yi ba? To lokacin ai ba laifinshi bane tunda shi bai san me zai ce mata ba? Ko dai ta fahimci bata buƙatar su a rayuwa ne shi yasa ta cire su? To shi menene nashi? Sumar kanshi ya shafa yana tunani duk ya rasa me yasa hankalinshi da tunaninshi suke kan yarinyar, yana jiyo Dada tana hira da yaran dake yawan shigo mata shi sam wannan ba shine a gabanshi ba, rayuwarshi duk ta zama babu daɗi haka kawai ya fara jan kekenshi yana gyara ɗakin, kallon agogo ya sake yi biyar saura minti goma yanzu kam ya tabbatar ba zuwa zata yi ba hakan yasa ya ɗauki wayarshi kawai ya kunna karatun  Qur’ani yana saurare idanunshi a lumshe.
Kamar daga mafarki yaji Dada tace “Lale lale tun ɗazu nake jiranki ashe kina tafe.”
Sautin karatun ya rage sosai tare da nutsuwa don yaji ko itan ce tazo.
Zeey ce ta rungume Dada tace “Hajiya Dada kwana biyu ne fa baki ganni ba amma duk kin yi rashina.”
Kunnenta ta ɗan jaa kaɗan wanda yasa Zeey yin ƙara tace “Dole inje gidanku na roƙa a bar mini ke ko a bani ke na bawa jikana.”
Ido Zeey ta buɗe tace “Wa? Ba dai ni ba?”
“Akwai jikokina sai dai ba a Kano suke ba.”
Dariya kawai tasa tace “Dada kin yi mishi maganar kuwa?’
“A’a yana ɗaki kin san halinshi ai tambayata zai yi wanene, kawai dai nace mishi zaki zo yau.”
“Hmm shiru yayi ko?”
Dada tana murmushi tace “Kin san hali ai.”
Dada ce tayi gaba ta kamo hannun Zeey suka shiga ciki, ƙofar ɗakin ta ƙwanƙwasa sannan tace “Baqeeru?Idonka biyu?”
Idanunshi ya sake runtsewa sannan ya buɗe yace “Umm!”
Ƙofar Dada ta buɗe, Zeey tana jingine da bango ta juya baya, ƙamshin turarenta ne ya shiga hancinshi, kallonta yayi kaɗan yayi saurin mayar da kanshi gefe, Dada tace “Ko zaka ɗan fito akwai wanda yake son ganinka ne.”
Kamar zai tambayi waye sai kuma yaji bai son yin magana saboda yadda take tsaye daga waje, Dada ta juya tana saka tabarma a tsakiyar falon dake ɗauke da kujeru biyu.
Keken ya turo da kanshi har yazo inda Zeey ke tsaye, kasa cigaba da tafiyar yayi ita ma bata motsa ba, a hankali ta waigo shima ya ɗago suka kalli juna, da sauri suka ɗauke kai, Zeey tace “Yau baka je yawo ba?”
“Dama kullum nake zuwa?”
“Au ashe fa ba kullum kake zuwa ba.”
Kallonta yayi itama ta kalleshi sai kuma yaga tayi murmushi ta wuce wurin Dada, Baqeer da kallo ya bita.
Chapter 54 · 0% Book details