Sashe 35
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
******
Maryam ce ta kalli mai gidan nata dake zaune a ɗaki tana yi mishi tausa cike da sanyin murya tace "D don Allah kaji? Ba dadewa zai yi ba yana kai shi zai dawo."
Kallonta yayi takaicin yadda take fifita ƴan uwanta sama dashi na damunshi don jiya ko bata faɗa ba yasan kuɗin cefanen daya bata su taje ta kashewa, sai dai ya zai yi? Yana sonta iya so shi yasa yake haƙuri da waɗannan abubuwan nata.
Zare ƙafar shi yayi yace "To shi kenan ni bari na fita." Sumbatarshi tayi a saman leɓe tare da tsotsan kasan leɓen nashi kaɗan tace "Love you."
Murmushi ya sakar mata sannan ya fito, ta rakashi har mota sannan ta dawo ɗaki, kayan da bai saka ba wanda ta ciro mishi ta mayar cikin drawer. Waya suka sake yi da Salim akan yana waje zai turo mai gadi ya amsar mishi key ɗin motar.
Tace to tare da fitowa falo dan ɗauka me zata gani? Babu key ɗin motar a wurin, cike da mamaki ta hau dubawa sai dai babu shi babu alamarshi, ganin haka yasa ta kira mai gidan nata din tana tunanin faɗan da suka yi jiya watakila yasa ya manta ya ajiye a wani wurin.
Bayan ya ɗauka take sanar dashi bata ga key ɗin motar ba, buɗar bakinshi sai ce mata yayi Baffanshi ya amsa zai je wani wuri daga nan zai taho da Areef.
Gaba ɗaya mamaki ne ya rufeta tace "D me kake cewa? Na ɗauka mun yi magana da kai akan zan bawa Salim ya kai Ya Baqeer asibiti?"
"Ohh haka ne fa ki cewa Salim ya nemi adaidaita sai ki bashi 1k duk da nasan ba zai wuce 500 ba kinga ai babu laifi, kin dai san ba zai yiwu Baffa ya hau adaidaita ba bayan ga mota a gida, sannan don motarshi na wurin gyara bazan ce mishi kada ya fita da motar dana sayawa jikanshi ba."
Kasa magana tayi saboda tsananin mamakin kalamanshi, duk da ba yau suka saba guma mata takaici ba amma na yau yayi mata zafi fiye da ƙima, yanzu duk soyayyar da suka sha daren jiya har ya manta ya koma gidan jiya? Kasa magana tayi sam bata ma san shi ya kashe wayarshi ba sai ringing taji a kunnenta, kallon wayar tayi Salim ne ta ɗauka cikin dakushashiyar murya taji yace "Nayi mishi magana zai zo ya amsa nima yanzu na iso, ƙawarki ce ma ta ajiyeni."
Hawaye taji sun gangaro mata, ta sharesu tana cewa "Wacece?"
"Zainab dai Zeeyn Baqeer, nayi mamakin ganinta wallahi data cemin Zeey ce nayi ta mamaki har muka iso mamaki bai bar kaina ba."
Murmushin yaƙe tayi tace "Don Allah taimaka ka bata." Shi kanshi yadda ta amsa yasan da wani abun sai dai bai tambaya ba ya miƙawa Zainab, ta kara wayar tana cewa "Umma ce ta bani saƙo wurin Salim ashe ma wurinki zaizo, ban yi plan da shigowa gidanki ba shi yasa bazan leƙo ba."
Maimakon taji ta bata amsar maganar data yi sai ji tayi tace "Zeey don Allah ki taimaka ki bada motarki akai Baqeer asibiti na rasa ya zan yi....." ta ƙarasa maganar cikin rawar murya "Okay, amma kin tabbatar babu wani abu?"
Ta sauke ajiyar zuciya tace "Nagode sosai babu komai wannan ma da kika yi mana kin biya mana, Allah ya saka miki da alkhairi."
Kashe wayar Zeey tayi don daga yanayin maganar Maryam tasan babu lafiya gashi bata so taga mutum cikin damuwar da ba zata iya tallafa mishi ba.
Da murmushi ta kalli Salim ta miƙa mishi key ɗin motar tace "Kaje da tawa ashe ta manta akwai abinda zata yi kuma uzurin na dole ne."
Ya amsa tare da godiya, kallonta yayi yace "In ajiyeki kafin na wuce?"
Tunowa data yi in har tsautsayi yasa aka ganta akwai tashin hankali hakan yasa tace "No kawai kaje inka gama ka kirani na fito nazo inda kake na amsa."
Da mamakin kalamanta yake kallonta to taya zata koma gida? Ƴar gayu kamar ta? Sai dai yasan a yanayin yanda Zeey take magana da isa bai isa ya sake tambayarta ba, bata ko tanka shi ba ta fito yana kallonta ta tari adaidaita kai daga gani kasan bata san ya ake tarar su bama, ta sanar dashi inda zataje yace 700 ga mamakinshi yaga ta shiga bayan shi jan magana yayi ya tsuga mata kuɗi, zaune take a ciki tana kallon yadda ake gwajab-gwajab da ita a hanya gaba ɗaya mamakin kanta ya isheta wai anya itace dai Zainab? Zainab Sulaiman Karaye? Anya kuwa a cikin hankalinta take abubuwa? Tun ɗazu take kallon kiran da Nabeela keyi mata amma taƙi ɗauka, kanta kawai ta shafa tana mamakin yadda ta manta abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi sannan har ta ke manta kanta wurin ganin ta taimaka mishi. Gefen titi ta kalla daidai nan mai adaidaita ya sake jijiga tace "Ai ba don shi nake yi ba don su Umma nake yi." Ta ƙarasa maganar tana sauke ajiyar zuciya.
A gefen gidansu ta sauka ta bashi 1k tana neman wucewa, daga nesa ta hango yarinyar nan tsaye da saurayin rannan da alama kyauta ma ya kawo mata don ga abu nan a hannunta sai smiling take yi, shi kuma yana jingine a jikin mota, wani kallo tayi musu na takaici kawai ta shiga gida, shi kam mai adaidaita daɗi ne ya kamashi don ya kula bama tasan nawa ta bashi ba saboda hankalinta baya wurin, cikin sauri yaja adaidaitarshi yayi gaba don ma kada ta dawo tace ya biyata, mamaki ne ya rufe mai gadi daya buɗe mata ƙofa ta shiga, kai tsaye ɗakinta tayi ta faɗa kan gado tayi ruf da ciki tana ƙullawa da kwancewa.
*****
Bello dake tsaye kusa da Asiya wata irin gigitaciyar soyayya ce take taso mishi, ji yake yi kamar yafi kowa dace a duniyar nan, ya mata alama data shiga cikin mota ta buɗe gift din, shiga tayi shima ya shiga ya zauna ta buɗe jakar sannan ta dauko box din dake ciki, kwalin jaka ne set ɗinshi da takalmi, wani sanyayyen murmushi ta sakar mishi tace "Bae ka bar sakaltani da yawa fa, kullum ne sai an kawo mun gift?"
Hannunta ya riko yace "My love kin dai san kin fi ƙarfin komai a wurina, nayi miki alkawari zan jiyar dake soyayyar da ko sunan Baqeer baza ki tuna ba nan gaba."
Murmushi ta sakar mishi tace "Yanzun ma kana yi"
"Tukunna ki jira na samu fita ƙaro karatun don ƙafata ƙafar ki gwara muyi aure na tafi dake."
Wani sanyi ne ya ratsata tabbas Bello zai cika mata burinta, har yanzu ba wai tana sonshi bane amma future ɗinta ta tabbatar a wadace take in har ta aureshi.