← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 168

Sashe 22

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“To ka fita dani daga ɗakin mana kowa ya huta? Zaka iya kaini waje ka yasar ai.” Baqeer ya samu kanshi da faɗan haka.
Da mamaki Kamalu ya kalleshi don ko sanda Baba yake ji dashi bai iya mayar mishi da magana sai dai kawai ya tafi ba tare da ya kulashi ba.
“Ni kake faɗawa haka?”
Baqeer bai tanka shi ba ya ɗan harɗe hannunsa a kirji kawai ya lumshe ido, shi da Kamalun ma zai fita dashi ƙila da hakan yafi mishi sauƙi don rayuwar ta isheshi.
Kamalu dama da fitarshi ya ɗan sha ƙwayar da suka saba sha, nan da nan idanunshi suka yi jaa ya miƙe ya janyo keken Baqeer ya fara neman saka shi akai, yana tunanin Baqeer zai bashi hakuri yaga ko kulashi bai yi ba, Kamalu na haki haka ya saka shi a kan wheelchair hankalin Baqeer a kwance yake babu alamun dana sani ko bada hakuri.
Da yake a soro suke kai tsaye ya fita dashi waje ya fara turashi a keke cikin ƙarfi yana cewa “Ka nemi yafiyar abubuwan daka aikata mana ni da ƙanne na.”
Sam Baqeer bai da ma niyyar yin magana, takaici ne ya rufe Kamalu kawai ya ajiye keken nashi daga can gefe tare da ja baya yana cewa “Kasan Allah yau zan nuna maka ni mahaukaci ne in dai baka bani haƙurin abubuwan da aka yita yi mini a gida saboda kai ba, Baqeer bai ko kalleshi ba sai addu’a kawai da yake yi a cikin ranshi.
Wani irin birki da aka taka da ƙarfi ne yasa hankalinsu ya tashi, Baqeer abinda ya faru dashi ne ya dawo mishi nan da nan zufa ta shiga keto mishi ta wanke mishi jiki, shi kanshi Kamalu tsoro ne ya rufeshi don gabanshi sai dukan uku-uku yake yi.
Zainab dake cikin mota tana ta sauri saboda wayar gaggawa da Nabeela tayi mata itace ta ɗago kanta daga sityarin motar cikin wani irin ɓacin rai ta fito, kan Kamalu tayi wanda yake kallonta hankali a mugun tashe, bai yi auni ba yaji ta zabga mishi wani irin mari.
A fusace yana haki yake kallonta yace “Ke? Baki da hankali ne?”
Cikin faɗa take kallonshi ita ma kafin ta kalli mutumin dake kan wheelchair, ba dai yaron jiya bane? Kauda tunanin tayi daga ranta sannan ta matsa inda yake ta janyeshi daga kan titi ta ajiyeshi a gefe cikin ɗan duhun farkon dare take kallonshi tace “Me yasa kai baka rabo da haɗuwa da mutanen banza? In kasan wanda kake tare dasu basu da hankali me yasa ba zaka zauna a gida ba? Ko kana tunanin kai ba mutum bane dan baka da ƙafa? Ko kuwa kana tunanin kai kaɗai ne ke cikin mummunar ƙaddara da har kake yarda ana juyaka duk yadda aka so? Rannan ba kai bane mai bin mace tana wulaƙanta ka? Sannan yau ka ɗauko wanda yake son yin ajalinka ma gaba ɗaya? To ka sani in har ka bari rayuwarka ta salwanta ko ka mutu ba lallai irin waɗannan mutanen suyi maka addu’a ba, in ma zaka buɗe ido ka buɗe akwai mutanen dake cikin wani hali sama da kai.”
Bata ko jira amsarshi ba ta fara ƙoƙarin shiga mota, a fusace Kamalu ya nufota yana shirin fizgota, waigowa tayi cikin tsananin ɓacin rai ta nunashi da yatsa tace “Don’t you dare! Wallahi ni ba sa’arka bace sannan daga ganinka ma ba a hayyacinka kake ba, useless kawai.” Ta shige mota tana jan wani tsaki.
Kamalu ji yayi ya kasa motsi don motar kaɗai daya gani yasan ba sa’ar yinshi bace, haka yaja Baqeer sam babu wanda ya sake cewa uffan har suka koma gida.
Duk yadda Baqeer yaso ya cire kalaman yarinyar daga cikin ranshi ya kasa, duk wani motsi da zai yi kalamanta ne suke sake taso mishi, tabbas gaskiya ce tsagwaronta ta faɗa mishi, bazai yiwu ya maida kanshi nakasashe ba don kawai Allah ya ɗauke wani sashi na jikinshi don ya jarabce shi, in har bazai warke ba to fa dole ne ya koyi rayuwa da ƙaddarar data same shi…..

Me kuke tunanin zai faru? Ga dai Zeey ta tafi gida ana mata kiran gaggawa, ga kuma Baqeer ya fara tunanin canza rayuwarshi, Bello fa? Kuna ganin zaiyi nasara?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#Shalele
#Zeey
#MBB
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SHA HUƊU*

https://www.tiktok.com/@maims_kiddies
"Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta.
https://Wa.me//08101378616

{14}

Wani irin ihu Kamalu ya saki tare da durowa daga kan gadonshi wanda hakan yasa Baqeer kallan inda yake, cike da mamaki yake yi mishi kallon zararre. Kamalu ya sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu gefen fuskarshi ya ƙara faɗawa kan gado a fili yace "Dole na nemoki Roshni ɗi ta ai bansan soyayyar lokaci ɗaya tana yiwuwa ba amma gaba ɗaya kin gigitani, nasan marin nan ke kanki yayi miki zafi." Yasa hannu ya finciko pillow ya ƙanƙame yana juyi, kai kawai Baqeer ya girgiza don shi abinda ke gabanshi yafi shirmen nan.
Wayar da Hadiza ta bashi ya ɗauka ya saka number Asiya kawai yana kallo, wani abu ne yaji ya taso mishi hakan yasa ya mayar da wayar ya ajiye tare da runtse idanunshi, Bello yake jira yazo ya faɗa mishi abinda Asiya tayi mishi don har yanzu ƙwaƙwalwarshi ta kasa ɗaukar abinda ke faruwa.
Yana kallan Kamalu na ta ƙara kankame pillow yana mannawa pillow kiss lalai yau ya tabbatar kanshi ba ɗaya ba, takaici ne ya rufeshi kawai ya juya kai gefe.
Chapter 22 · 0% Book details