Sashe 37
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai kuwa ba ƙaramin kunna Kamalu yayi ba don haka yasa hannu ya janyo rigarshi yace "don ubanka kai har ka isa ma ka buɗe baki ka zagi Roshni bayan ta gama yi maka rana har tana ɗaukar motarta ta baka aro shine kake kiranta mara kamun kai? Kai har ka isa ma kace zaka faɗi wata maganar banza akan Roshni ɗita na ƙyaleka" don ganin nan fa da yayi wa Salim a cikin motar Roshni gashi kuma wai har ta bashi aro ya tuƙa ba ƙaramin zafi yayi mishi a rai ba don gani ma yake yi kawai shima Salim ɗin son Roshni yake yi shi yasa ma har ta ɗauki motarta ta bashi ita ta dawo a napep.
Sai lokacin Salim yasan akan wacce yake magana don haka ya ƙara kwashewa da dariya, cikin dariyar yace "au wai dama Zainab ce Roshni ɗin da kake magana akai, lallai kuwa na yarda abar da kasha tayi maka karo har tana faɗa maka ƙarya tunda gashi ka hau kai ka zauna". Kaucewa yayi ya wuce ya bar Kamalu a wurin yana nanata suna ZAINAB, ashe sunan Roshni ɗin shi kenan Zainab suna mai daɗi sai kuma aka yi dace irin sunan Innarshi gareta wato Abu. Ji yayi kamar ya ƙarasa ƙofar gidan yasa ayi mishi sallama da ita tunda dai yau Allah ya taimake shi yasan sunanta sai kuma ya kalli kayan jikinshi yaji ina ai basu dace da zuwa zance wajen Roshni ba don haka ya juya ya koma gida da nufin canjo kaya sannan ya dawo wurin Zainab ɗin.
*****
Tunda dai ta samu tabbaci daga Salim cewa ya kaiwa Baqeer kuɗaɗen har ma sun je asibiti an kunce ɗaurin sai taji hankalinta ya kwanta, godiya tayi ta mishi tana saka mishi albarka don tasan ba don shi ba da bata san yadda za'a yi saƙonta ya iske Baqeer ɗin ba bare da aka ƙara samun tazara mai yawa a tsakaninsu. Tashi tayi ta koma ɗakinta tana ƙarewa ɗakin kallo ko ta samu wani abu mai muhimmanci da zata ɗaga ta sayar ko ta samu taja jari don zama haka bai ganta ba ita da take da ɗa mai larura ga Hadiza da take da wani irin mugun miji da yake ƙyashin abincin da zai basu suci ma bare sauran buƙatu na rayuwa, dama Baqeer ɗin ne mai taimaka mata to shima yanzu ga yadda Allah yayi dashi. Kallon tsaf ta ƙarewa ɗakin ta rasa abu guda ɗaya mai daraja da zata ɗaga ta sayar idan dai kuma ba kujerunta zata saka a kasuwa ba, zama tayi akan doguwar kujerar tana shafata tare da tuna lokacin da Baqeer yayi mata su sababbi fil a leda haka aka shigo dasu ɗakinta aka jera, a waccan ranar taga tashin hankali don muraran su Jamila suka kasa ɓoye hassada da baƙin cikinsu don a cewarsu ma Mallam ne yayi mata aka fake da wai Baqeer ne yayi duk don a raina musu hankali, to ina ma yaga kuɗin da zai iya yin waɗannan kujerun masu daraja banda dai ana so a raina musu wayo, a cewar Abu kenan data kasa ɓoye hassadarta a wannan ranar saboda ita tafi Jamila wayo ba komai take fitowa ta nuna ba sai dai tayi ta mata ingiza mai kantu ruwa ana ganin laifinta.
Zuciyarta babu daɗi saboda duk ta kalli kujerun ta tuna Bqeer ne ya saya mata ba ƙaramin daɗi take ji ba gashi yanzu halin rayuwa yasa dole zata ciresu ta sayar tayi jari ko ta samu abinda zata rufawa kanta da iyalinta asiri. Wayarta ta ɗauko ta kira makwabciyarsu da suke hulɗar arziƙi sosai da ita tace mata ko zata taimaka ta samo mata masu sayen kujerunta, ba tare da bin ba'asi ba tace ai ko itama sai ta saya don kujerunta nata babu abinda suka yi. Haka dai suka ajiye akan zata shigo ta ƙara ganinsu sai suyi ciniki.
*****
Tana shigowa cikin gidan ɗakinta kawai ta wuce ta kwanta, sai ma tayi sa'a bata haɗu da kowa ba don bata so Mummy tayi mata magana akan tafiya da tayi ta bar Nabila a kantin da suka je da sai keke napep ta hau ta dawo gida don bata san wani uzurin zata bayar ba kuma duk kuwa da tasan Mummy bata cika yawan matsanta mata ba to amma fa bata so tana yawan ɓata mata rai. Tana shiga ta sakawa ƙofar ɗakinta makulli ta rufe don bata so kowa yazo ya dameta, tana jin lokacin da Nabila tazo tana buga ƙofar ɗakin amma tayi shiru ta rabu da ita kamar bata jinta, a haka har bacci ya ɗauke ta inda bata farka ba sai ana wajen ƙarfe biyu da rabi, tana tashi bathroom ta faɗa tayi alwala tazo ta tada sallah, sai data idar sannan ta tashi ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta fita. Akan dining table ta tarar dasu Mummy suna cin abinci. Mummy na ganinta tace "baby har kin tashi?"
A shagwaɓe ta ƙaraso wajen tana ɗagawa Mummyn kai ba tare data buɗe baki ta amsa ba. Kujera kusa da Mummyn taja ta zauna, da kanta Mummyn tayi serving ɗinta su dai Kabir da Nabila suna kallonsu sai ma taɓe baki da Kabir yayi yace "wallahi Mummy ke kike daɗa shagwaɓa yarinyar nan shi yasa take tsula iskancinta son ranta don tasan babu abinda za'a yi mata".
Harararshi Mummy tayi haɗe da cewa "to ina ruwanka? Ko kuwa dai sa ido". Gwalo Zeey tayi mishi tana dariya ƙasa-ƙasa. Ƙwafa Kabir yayi yace "wallahi idan na damƙeki sai kin gane ke ƙaramar mara kunya ce, na lahira sai yafi ki jin daɗi".
"Mummy kin ganshi ko" tayi maganar kamar zata saki kuka.
"Mummy kin ganshi ko" shima ya kwaikwayeta da irin muryarta. Anan suka hau cacar baki kamar wasu ƙananun yara, dama kuma sabon su ne don babu yadda za'a yi su zauna a waje ɗaya basu takali junansu sun yi faɗa ba. Sai da Mummy ta tsawatar musu sannan suka bari sai dai suna ta hararar junansu ƙasa-ƙasa ba tare da sun bari Mummyn ta gani ba. Sai da suka gama cin abincin har ma ta tashi zata bar wurin Mummy ta kira sunanta tare da bata umarnin ta koma ta zauna magana zasu yi. Zama tayi gabanta yana faɗuwa don tasan akan abinda ta aikatawa Nabila ne Mummy zata yi maganar.
Ai kuwa dai tana zama Mummyn ta fara magana cikin tausasawa kamar mai gudun ɓacin ran Zeey ɗin tace "wai ni kuwa Zeey meke damun ki ne kwana biyun nan duk kin canja idan kuma an tambayeki sai kice babu komai?"
Shiru Zeey tayi ba tare data amsa mata ba. Kallonta Mummyn ke yi tana jiran jin amsa daga bakinta sai dai har wucewar wasu mintuna Zeey bata ce komai ba don haka Mummy tace "baki da lafiya ne?" Girgiza kai tayi alamar a'a. "To meke damunki?" Mummyn ta ƙara tambayarta nan ma tayi shiru. "Shikenan to tunda ba zaki amsa ba amma ina kike yawan zuwa da kullum sai kin fita bayan kin san Daddynku ba cika son yawan fitarki yayi ba, kuma ina kika je yau da kika bar Nabila a inda kuka je kika tafi da motar sannan kuma kika dawo a napep kamar yadda maigadi yace sai daga baya kika fita kika amso motar kika shigo da ita? Wama kika bawa aron motar ke kika hayo napep Zeey ba kya gudun wani abu ya faru dake a hanya?"
Kawai sai ta sakawa Mummy kuka abinda ya dakatar da Mummy daga jerin tambayoyin da take yi mata kenan. Tuni hankalin Mummy ya tashi ta koma lallashinta, su Kabir da Nabila dai takaici kamar ya kashe su, su dama sun sani Mummy ba zata iya yiwa Zeey faɗa ba don a wurinta komai Zeey tayi daidai ne sai tace ai yarinta ce tasa wata rana ko ance tayi ba zata yi ba. Tashi suka yi suka bar musu wurin, sai da Zeey tayi kukanta ya isheta Mummy nata aikin lallashi sannan ta iya cewa "kiyi haƙuri Mummy wallahi ni kaina na rasa meke damuna, abun haushi abun takaici kuma na kasa cire abun daga raina".
Ajiyar zuciya Mummy tayi tace "ke kuwa wane irin abu ne wannan daya dameki haka kuma baza ki iya buɗe baki ki faɗa ba ko kya ji daɗi, fatana dai ba akan saurayi bane don kin san fa akwai wanda Daddynku yake son haɗaki dashi, don Allah kada kije kiyi abinda zaki janyo mana ɓacin rai daga ni har ke".
Sai da gabanta ya faɗi da jin wai za'a haɗata da wani duk kuwa data tsinci zancen a parlourn Daddyn ranar da yayi baƙi amma bata wani ɗauke shi da muhimmanci ba. "Ba akan saurayi bane Mummy, ke dai ki tayani da addu'a Allah ya yaye mini damuwar dake raina" kawai ta iya cewa Mummyn ta tashi ta koma ɗakinta, binta Mummy tayi da kallo tana tunanin to me yake damun yarinyar nan ne wai? Gaba ɗaya ta canja kamar ba Zeey ɗinnan ba ƴar hayaniya don in dai tana wuri baka taɓa jin shi tsit.
*****
Sai da ya nufi gidansu da zumuɗin son ya shirya ya koma wajen Roshni ɗin shi sannan ya tuna ashe fa an samu wani ɗan shegiyar ya ɗauke mishi babur ɗin shi, kamar shi kuwa ai yawa ne ya tafi zance wajen Roshni a ƙafa don haka ya fasa shiga ɗakin shi yayi shirin tafiya wajen Roshni ɗin sai ya shiga cikin gida wajen Abu yasan dai ba zai rasa na sayen wani babur ɗin ba a wajenta don a yadda take da zafin neman nan ko mota yace ta saya mishi yasan tsaf zata saya.
Tana zaune a tsakar ɗakinta tana ɗura tsumi a jarkoki saboda masu zuwa saye. Zama yayi daga bakin gadonta yana cika yana batsewa. Kallonshi tayi ta mayar da kofin da take ɗibar tsumin cikin robar tsumin ta ajiye. "Kai kuma lafiyarka ka shigo sai faman kumburi kake yi? Ko kuwa dai wani abu aka yi maka a wajen ka shigo ka huce a kaina?"
Sai da yaci serious irin maganar da zai yi mai matuƙar muhimmanci ce kafin yace mata "babur ɗina fa aka sace".