← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 168

Sashe 28

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ga mamakinta ko musu Zainab bata yi mata ba ta tashi ta nufi wajen da suke cin abincin taja kujera ta zauna, Mummyn ce tayi serving ɗinta don dama ita ta sabar mata da komai take so sai anyi mata gashi yanzu har girmanta bata iya tsinanawa kanta komai. Juya cokali kawai take yi a cikin abincin ta kasa kai ko loma ɗaya bakinta, haka nan sai ganin abinda ya faru tsakaninshi da buduwarshi take yi da kuma lokacin da wannan marar kan gadon ya ajiye shi akan titi. Wane irin canji ne ya samu rayuwarshi haka a ɗan taƙaitaccen lokacin data ɗauka bata sanya shi a ido ba? Tunanikan sun kasa barin zuciyarta har ma ta kasa cin abincin duk kuwa da tarin yunwar da take ji tun ma kafin ta fita ta bar gidan, tashi kawai tayi ta bar abincin ba tare da ko ɗanɗanawa tayi ba.

Kallonta Mummy tayi ta kalli plate ɗin da yake cike taf da abinci yadda ta zuba haka Zeey ta bar mata shi. "Meke damunki ne Zeey? Tun dawowarki na lura kamar akwai abinda ke damunki, ba dai wani mummuna abu aka yi miki a inda kika je ba ko?"
Kallon Mummyn tayi ta girgiza kai alamun babu komai sai kuma tace "Babu komai Mummy kawai dai na gaji ne.”

"Allah ya kyauta," kawai Mummy tace ba don ta yarda da amsar da Zeey ɗin ta bata ba sai don bata fiye son matsanta mata ba amma a yadda take da surutu da rawar kai tasan tabbas akwai abinda take ɓoye mata don haka nan Zeey bata iya shiru in dai har tana wuri to sai ta addabi kowa da karaɗinta. Juyawa tayi zata bar wurin ta koma ɗakinta Daddy ya shigo, yana ganinta kuwa ya fara faɗa ko sannu da zuwan da take yi mishi bai amsa ba.

"Wato Zainab har abada ke ba za'a faɗa miki magana ki ji ba ko, shine don ki nuna ban isa dake ba kika sake wulaƙanta yaron nan Najib bayan cewa da nayi ki bashi haƙuri?” Faɗa kawai yake yi irin wanda bai taɓa sakata a gaba yayi mata ba sai dai ko kusa hankalinta baya wajenshi bare ta tanka mishi irin yadda a mafi yawan lokuta take yi idan yana yi mata faɗa tana ƙoƙarin defending kanta, a yau zuciyarta tayi nisan kiwo ba saurarenshi take yi ba, tunaninta na wajen Baqeer da alhinin abinda ya sameshi, to wai ma shin yaushe ne yaji ciwon da ya nakastashi haka?

Mummy ce tace "Zainab" da ɗan ƙarfi lura da tayi sam hankalinta baya wajen, sai cewa tayi "Eh naji" kawai alhalin bata ma san maganar da ake yi ba. A halinta na rashin barin abinda ke cikinta sai ta samu kanta da kasa furtawa kowa damuwar halin da taga Baqeer ɗin, tana mamakin wai dama wannan gurgun da take yawan gani a mabanbanta lokuta Baqeer ne.

*****

Mamaki ne ya kama Umma data fito bata ga Zainab ba, leƙawa tayi ƙofar gida ko zata ganta sai dai ko alamunta bata gani ba, haka ta juyo tana cewa "Kenan tafiya tayi?” Komawa tayi ta kama aikin taliyar da maƙwabtansu suka kawo mata, tana yi tana share ƙwallar tausayin Baqeer. Wai kenan haka zasu cigaba da rayuwa baya da mataimaki? Salim ɗin da suka dogara a kanshi Mallam yayi sanadin da yayi fushi ya daina zuwa alhalin shi ba tausaya mishi zai yi ba bare ya tallafe shi. Dole ta tashi tsaye ta kama sana'a ta yadda zata samu ta ɗaukar wa Baqeer mataimaki ko almajiri ne da zai ke taimaka mishi tana biyanshi. Ta gama aikin taliyar ta shanya akan igiyar data ɗaura a kusa da ɗakinta, tattare wajen da tayi aikin ta hau yi tana kawar da kayayyakin data ɓata.

Abu dake zaune a ƙofar ɗakinta tana zuzzuba garin dakan da take sayarwa a ƙananun robobi ta kalleta ta taɓe baki kafin ta saki shewa tace "Ahayye nanaye, duniya rawar ƴan mata na gaba ya koma baya, yau ga uwar shalele, mowa a cikin ƴaƴa na sana'ar hannu, ai na ɗauka neman kuɗi sai mu irin ku sun girmi sana'a sai dai ƴaƴan ku su fita su nemo su kawo muku kuna daga kwance, ashe dai duk abun bogi ne,” ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya har da kama hanci ta saki guɗa. Har Jamila dake aikin abincin rana na tayata tace "Yo ba dole ta tashi ta nema ba tunda mai kawowar ya zama gurgu, zaman gida kuma ya aureshi? Kin manta sanda ɗan kanzagi ya ɗauke injin taliyarta ya ajiye wai ta huta?”
Dariya suka sheke dashi duka su biyun wannan abu na basu dariya.
Ran nan na Abu fari ƙal da farin ciki don a yanzu ji take yi tamkar tafi kowa, ƙiris ya rage gida ya dawo hannunta tunda ma gashi ta fara samun Mallam a hannu. A wulaƙance ta kalli Umma da ko ɗaga kai bata yi ta kallesu ba duk kuwa da yadda zuciyarta ke tafarfasa da wannan cin kashin da suke yi mata tace "Dama sakin wannan aikin taliyar kika yi kika tura shi bakin titi kuka yi bara sai kiga kun samo kuɗi fiye ma da abinda yake samu a harkar zanen don yanzu almajirai ai sune da kuɗi tunda su kullum cikin karɓa suke basu san su bayar ba.” Sai wannan lokacin Umma ta kalleta har zata yi magana sai kuma ta fasa ta shige ɗakinta ta barsu anan suna cigaba da sakin baƙaƙen maganganu duk dai akan fifikon da Baba ya dinga nunawa Baqeer akan ƴaƴan su. Zama tayi a bakin gado tana kukan tausayin kansu daga ita har Baqeer ɗin ganin yadda aka mayar da larurarshi abun gori har ana cewa ta turashi su fita bara kamar shi ya ɗorawa kan shi.

Yana daga ɗakinsu yana jiyo duk abinda ke faruwa a cikin gidan da duk gore-goren da suke yiwa Umman. Wani irin ƙunci da baƙin ciki yake ji a cikin ranshi, yadda kowa ya juya mishi baya nayi mishi ciwo. Kallon ƙafafun shi yayi da ko kaɗan baya jin alamun su a jikin shi, ya kalli hannunshi dake naɗe a cikin bandage yace "Shikenan yanzu ni a haka zan yi ta zama ba zan morawa kaina komai ba?” Ƙoƙarin motsa ƙafafun yayi tayi yaga ko zai iya tashi ya kasa, haka nan ya haƙura ya buɗe drawer dake ajiye a gefen katifarshi ya ciro takarda da pencil ya hau ƙoƙarin yin zane sai dai hannunshi baya da ƙwarin da zai iya riƙe pencil dole ya haƙura yayi watsi da kayan a tsakar ɗakin yana sakin huci kamar wanda yayi tseren gudu. Gabaki ɗaya rayuwar bata yi mishi daɗi ji yake yi ina ma ya mutu ya huta, duk ya juya ya kalli ƙafafun shi naɗe a waje ɗaya basa iya ko motsi ya ɗaga hannunshi ya ganshi a naɗe a cikin bandage sai yaji to shi miye amfaninshi ma tunda ba zai iya amfanar kanshi da komai ba. Ƙarfin imani ne kawai ke hanashi ɗaukar mummunar shawarar da zuciyarshi take kitsa mishi don wasu lokutan sai yaji kamar ya datse rayuwarshi ya huta gaba ɗaya da waɗannan matsaltsalun da suka dabaibaye rayuwarshi.

*****
Kamalu kuwa yana fita ya burga babur ɗin shi yabi kwatance tiryan-tiryan kamar yadda aka yi mishi sai gashi a ƙofar gidan su Zeey. Kallon ƙatuwar katangar gidan yayi yana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarshi, yau dai gashi a ƙofar gidansu Roshni ɗin shi fatanshi dai tayi na'am dashi ta amshi tayin soyayyar shi, kallon rigarshi yayi yana ƙara kakkaɗeta yana tabbatar da shigarshi tayi ko gaban gwamna zai iya zuwa a haka. Sauka yayi ya ajiye babur ɗin a gefe ya ƙarasa gaban gate ɗin gidan yasa hannu ya ƙwanƙwasa. Daga ciki mai gadi ya taso ya buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ya leƙo da kanshi waje.
Chapter 28 · 0% Book details