Sashe 45
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Zama Zeey tayi tana kallon Mummy dake haɗa wasu kaya a ɗakinta, miƙewa tayi ta sake nufar ɗakin Nabila, kwana biyu yanayin data samu kanta a ciki yasa ko zama basa yi suyi hira, ita komai ma daina yi mata daɗi yayi shi yasa ta gwammaci ta killace kanta wuri ɗaya inda ba za'a dameta da hayaniya ba. Shiga tayi tana ƙwala kiran small Aunt sai dai ta iske ɗakin wayam Nabila bata ciki yanzun ma, hankalinta ne ya kai yanda ɗakin ya ɗan ragu, gashi babu wasu daga cikin kayayyakinta a ɗakin kamar ma dai tayi tafiya ne. Fita tayi ta koma ɗakin Mummy tana tambayarta inda Nabilan taje. Taɓe baki tayi tace "Share ta fushi tayi akan nayi mata faɗa shine ta haɗa kayanta ta koma gida, kin dai santa ai bata so ana faɗa mata gaskiya ni kuwa tana zaune a gidana ba zan kawo ido na zuba mata sai abinda take so zata yi ba.”
A shagwaɓe tace "Kai Mummy don Allah, wai me Aunty Nabila take yi miki ne da kullum sai kin yi mata faɗa, duk ƙoƙarinta nata burge ki ba kya gani? Yanzu har wani laifi ma take yi da za’a dinga yi mata faɗa?”
"Au haka ma zaki ce bayan duk abinda nake yi saboda ke nake yi, har wani ƙoƙari take yi ta burgeni daga neman suna kawai, tana dai yi don ta burge waɗanda take son burgewa amma bani ba.”
"Ni dai Mummy don Allah ki daina abinda kike yi mata wallahi bana jin daɗi kamar ba ƴar uwarki ba, kefa kike yi mana faɗa akan rashin jituwarmu da Kabir amma gashi ke kuma kina yiwa ƙanwarki hakan.” Kallon Zeey tayi baki buɗe tama kasa ce mata komai, da bata san halin Zeey ba da ta mata faɗar rashin kunya.
Tashi tayi ta fita daga ɗakin tana cewa "Ni gashi sam bana jin daɗin zaman gidan nan idan bata nan gashi yanzu kinsa tayi fushi tayi tafiyarta gidan Inna, dole ne ma naje nayi bikonta gaskiya ko kuma na bita can mu zauna tare amma bazan zauna wancan Kabir ɗin nayi mini jaye-jayen tarkacen abokanshi ba.”
Tayi maganar a shagwaɓe tana fita daga ɗakin
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI*
{27}
Zeey na shiga ɗaki ta kira wayar Nabeela sai dai harta katse bata ɗauka ba, takaici ya kamata ta cilla wayar gefe, mamakin kanta take yiwai har da jan faɗa akan faɗan da bai shafeta ba, so take ta samu yiwa wani magana amma bata san wa ba.
Ƙofar ɗakinta aka buɗe hakan yasa ta kalli wurin don tasan Mummy ce. Shigowa tayi tana kallon ɗakin kamar ba yanzu da suka tashi tace ta ɗan gyara ba amma yafda ta tafi haka ta dawo ta sake samun ɗakin babu alamun gyaran, sai ma ƙara ɗan batashi data yi,
Mummy ce ta kalleshi wanda gaba ɗaya hankalinshi baya maganar da take, cike da mamaki tace "Senate ni kam lafiya dai ko? Tunda ka shigo hankalinka ba a jikinka yake ba."
Ƙaramar iska ya furzar daga bakinshi yace "Yau zamu yi taron manyan unguwar nan, zan ji ƙorafe-ƙorafensu na kuma taimaka musu tare da yardar su kuma zasu taimakeni har kar siyasa ta."
Ajiyar zuciya tayi tace "Ah Alhamdulillah, ba dama abinda muka zo zama anan din kenan ba?"
Kai ya jinjina yace "Haka ne amma ba kya tunanin mutumin can zai iya ruguza mana shirin mu?"
Ajiyar zuciya tayi don ta gane Badaru yake magana tace "Da wannan kuma, amma shi don neman masifa shikenan taron ma ba zai bari ayi lafiya ba? In ba zai zo ba kawai ya zauna a gidanshi mana."
“Taya zan hanashi zuwa bayan kina ganin yana daga cikin dattijan unguwa.”
Kai ta girgiza tana riƙe hannunshi tare da cewa “Mantawa kayi wanene Badaru? Ai bana ji zai zo in har yasan taron naka ne, ko ka manta ko ganinka yayi a hanya canzata yake yi? Bayan kuma dama an riga anyi muku tsakani dashi.”
Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke yace “Har kinsa naji hankalina ya kwanta, sam yanzu bana son abinda ya faru tsakaninmu shekarun baya ya sake faruwa.”
Tana murmushi tana cewa “Ba zai faru ba in Sha Allah! Muna hawa kujerar zamu bar Kano mu koma Abuja daga nan kuma ka fara plans ɗin ka da cikar burinka na zama govenor.”
Rungumeta yayi tabbas shi kam har mamaki yake yi yadda manyan mutane ke yawan complain akan matansu don shi dai kam sai hamdalla, kanshi ta shafa tace “Allah ya kare mini kai Senate.”
Nan yace Ameen yana miƙewa daga kan gadon.
******
Baqeer ne ya turo kekenshi zuwa falo inda Dada take, wanka yake son yi amma bai san ta yadda zai yi yace mata yana son ruwan ɗumi ba, sam tausayi take bashi, sau da dama in zai yi wanka kafin ya nema ma zata ce ta kai mishi ruwan banɗaki amma yau zuwan baƙuwar nan yasa ta sha’afa, dariyarta ya jiyo ta bayanshi tana cewa “Ka huce ka gama fushin da takardar?”
Fuskarshi sam babu fara’a ya ɗan kawar da kai kaɗan, plate ɗin hannunta ta miƙa mishi wanda ke ɗauke da yankakkun kayan marmarin da Zeey ta kawo.
Bai amsa ba sai dai yanayin kallonshi da ya canza jiki a sanyaye yace “Dada daga ina kika samu fruits?”
Murmushi tayi tace “Aiko mana aka yi.”
Cike da kokwanton kalamanta yake kallonta ko me ya tuna sai kuma fuskarshi ta canza sosai yace “Ba dai yarinyar ɗazu bace ta kawo?”
Dada tayi saurin waskewa tana cewa “Ruwan wanka kake so hala? Don dama ɗazu nake tunanin ɗora maka.”
“Itace ko?” Ya ƙara jifanta da tambayar.
Kallonshi tayi tace “Wai Baqeer ni kam fitinar me kake ji da ita ne? Nace aiko mun aka yi ba shikenan ba?”
Ajiye plate ɗin yayi ya gara kekenshi zuwa ɗaki, rufewa yayi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, me kenan take yi haka? Yaji ta bada motar da bai san tata bace ko ta aro ce amma banda ta dinga kawo abu cikin gida, ba zai lamunci wannan ba tunda ba saninta suka yi ba.
Waya ya ɗauka ya kira Salim, ringing uku ya ɗauka yace “Baqeer inzo ne?”
Kai ya girgiza tare da yin shiru to wai ma taya zai ce a bashi number ta? Bayan ko sunanta bai san yadda zai yi ya tambaya ba? Sumar kanshi ya shafa yace “No babu komai kawai dai tambayarka zan yi ya kasuwa?”
Cike da jin dadi Salim yace “Alhamdulillahi gashi nan muna fama.”
“Don Allah ko zaka leka Umma kaga ya take? Mun yi waya amma hankalina ya kasa kwanciya.”
Ba tare da wani dogon nazari ba yace yana tashi zai biya, shiru suka yi ya ɗan yi gyaran murya kaɗan yace “Ranar da muka je asibiti da motar wa ka kaini ne ni kam? Ina taso na tambayeka.”
Salim yayi shiru yana nazarin abinda zai ce, Baqeer ne yayi saurin cewa “Kar kayi mini ƙarya Salim please, motar ƙawar Maryam ce ko?”
Yawun bakinshi ya haɗiya yace “Eh! Am really sorry da ban sanar da kai ba, Maryam ce tace nayi using ɗinta tata bata ga key din ba.”
Kai ya jinjina kenan har hancinshi yasan ƙamshin ta? Nan da nan yaji hankalinshi ya tashi, lallai Baqeer “Don Allah number fa? Kana da shi? Ina son nayi mata godiya.”
Cikin jin daɗi Salim yace “Yanzu kuwa zan turo maka.”
Nan suka yi sallama ya kashe wayar.
Muryar Dada ya jiyo tana buga kofa tana yan mita “Ni kam hala dai halinka gaba ɗaya aka canza? Yanzu ko itan ce ta kawo sai kace ba zaka sha ba? Kyautatawa ce ai ba roko ba, maimakon ka amsa kayi godiya sai ka hau fushi kaƙi amsa?”
Hannu biyu yasa ya shafi fuskarshi ba wai bai gode bane haka kawai yake ji wani sashin na zuciyarshi na tunanin rayuwar yanzu, mahaifinshi ma ya banzatar dashi taya wata da bashi da haɗi da ita zata dinga kula dashi kamar yadda take yi? Dole zai yi mata magana akan abinda tayi.