Sashe 133
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daddy wanda shigowarshi kenan yake jiyo kukan Zainab, hankalinshi a tashe ya nufi ɗakin don ya tabbatar dangin mamanta ne suka sakata wannan kukan, kuma tabbas ba zai ƙyalesu ba har Ɗambattan zai je duk sai ya ci mutuncinsu, dama shi yasa ko da wasa baya son taje yanzu gashinan abinda ta jawowa kanta, ƙofar ɗakinta ya ƙwanƙwasa bai jira ta amsa ba ya tura ƙofar don zuciyarshi har wani azalzala yake.
Rai a ɓace yace “Da da nake hanaki zuwa ai baki yarda ba yanzu da alama kin san amfanin abinda nake yi miki tunda gashi kema da kike tasu sun gwada miki halinsu.” Kallonshi tayi ta ajiye kayan sannan tace “Ni ba saboda su nake kuka ba.” Da mamaki yace “Saboda wa kike kuka to? Ko akan waccan shashashar Nabilan ne?”
Kai ta girgiza tace “Ba’a kanta bane sannan Dady kada dai ka manta ƴar Mummy ce kake kiran ta shashasha.” Tsaki yayi ta sauko ta tako gabanshi, kallonta yayi da son jin me ya faru don sai yaga gaba ɗaya ta canza, anya ma sun kular mishi da yarinyarshi kuwa? Tsugunawa tayi tace “Daddy surukinka nake so yazo ya gaisheka shine nake jira ka sanar dani lokacin da kake nan.”
Wani wulaƙantaccen kallo yayi mata yace “Ina da wani suruki ne bayan Junaid? Kin dai san bana son shirme ko?”
Ta dake tace “Junaid ba surukinka bane sai dai in wata ƴar kake dashi daban da zaka bashi.”
Fuska a tamke yake kallonta, ɓacin ranshi ya fito bayyane a fuskarshi yace “Ke sam baki da kunya ko? Ni kike yiwa magana haka?”
Dakewa tayi tace “Daddy yaushe kake gida? Zai zo ku gaisa?” Yatsa ya nuna ta dashi yace “Kin san Allah ranki kike so ya ɓaci, ki kawo mini wani ɗan iska gida ki gani.”
Mummy ce ta katseshi da cewa “Senate please! Ka tambayeta wanene? Ko kuwa ka ganshi bai yi maka ba ne? Ka jira kaga wanene mana in bai maka ba sai ka sanar da ita ra’ayinka.”
Tsaki yayi yace “Ke har kina tunanin zata kawo saurayin da zai kwanta mini? Har yaushe ma tasan mutane ta zauna dasu balle tasan abinda ya kamata?”
Zee ce tace “Ban sani ba amma nasan abinda nake so, Daddy kasan bazan auri Junaid ba kuma babu wanda ya isa ya rabani da wanda nake so, abu mafi sauƙi shine ka amsheshi hannu bibi……” hannu ya ɗaga kamar zai kai mata mari, ko me ya tuna sai kuma ya fasa, ya dunƙule hannu tare da nunata yana fitar da iskar ɓacin rai yana cewa “ɗan gidan uban waye? Ko shima zaki ce baki sani ba?”
Kai ta kauda tace “Na sani amma ba wannan bane a gabana.” Rigarshi kawai ya kaɗa yayi ciki, zuciyarshi na azalzala, Mummy ce ta kalleta sannan ta jinjina mata kai alamun tayi daidai ita kuma tabi bayan Daddy. Ɗaki ya shiga ya zauna tare da buɗe ƙafa yana huci kamar zakanya, zama tayi kusa dashi tana shafa gefen kafaɗarshi tana cewa “Senate calm down, yarinya ce bata san meke faruwa ba, sai dai inaga don Allah kayi haƙuri ka bari yazo kaga wanene, in har bai yi maka ba kace bai maka ba, itama a lokacin na tabbatar bata da uzurin da zata ce a’a.” Kallonta yayi yace “Sam ban san ya zanyi da yarinyar nan ba gaba ɗaya bata jin magana.” Ta kwantar da kanta akan kafaɗarshi tana cewa “Yarinya ce kayi mata uzuri don Allah.” Da ƙyar ya sauke wata ajiyar zuciya yace “Kice yazo kuma maganarta da Junaid yana nan har sai na gamsu da shirmenta na watsa mata ƙasa a ido, na tabbatar bata isa ta ƙara yi mini musu ba.”
Mummy ta fito ta shiga wurin Zee ta sanar da ita saƙon Daddy, sai dai duk da haka babu walwala a fuskar Zee, kwanciya tayi kawai tana ji zazzabin na sake rufeta, ya zata yi? Ta san Baqeer ko da ƙafar shi ba zai taɓa yiwa Daddy ba, balle in yasan ɗan wanene, tasan duk kuɗinshi yana ji ance ɗan Badaru ne to fa an rabu kenan balle ga babu kudi ga kuma babu ƙafa, pillow kawai ta janyo ta kwantar da kanta tana tunanin abinda zata yi.
*****
Baqeer yana jiyo Dada nata mita akan tunda ya shiga ɗaki alwala kawai taga ya fito yayi bata ƙara ganinshi ba, sannan ga abinci ta bashi yaƙi ci, shi kam yana jinta don ko magana baya son yi, takaicinshi ɗaya rashin ƙafafuwan nan, haka yasa ƙafar a gaba yana ta ƙoƙarin takawa, sai dai daga ya tsaya a kanta sai yaji ya faɗi, yanzun ma sake gwadawa yayi ya faɗi, kanshi ya jinginar a jikin gado yana haɗiyar wani takaici da ɓacin rai, shi yanzu ko zai daki kirji yace yana son Zainab yayi yaya da ita? Hannu kawai yasa yana dukan saman ƙirjinshi da yake ji kamar wani abu ya tsaya mishi a wurin yaƙi wucewa, can ya janyo wayarshi ya kunna, saƙon Zainab ne ya shigo _Daddy yace kazo gobe da yamma ya ganka_ sake maimaita saƙon yayi, lallai Zainab da gaske take yi, shi yanzu ta ina zai iya zuwa? Wai anya ta tuno abubuwan da suka faru a baya kuwa? A dalilinsu? Abinda yasa har ƴan sanda suka shiga maganar? Badaru kuwa a ranar yayi mata iyaka da shiga gidanshi? Shima aka yi mishi iyaka da ko ganinta yayi kar ya sake yi mata magana? Dama can akwai ƴar tsama tsakanin iyayensu sai dai case ɗin nan shine ya kawo ƙarshen gaisawar da ake yi don kuwa tun daga nan komai ya wargaje, ashe Maryam sun cigaba da ƙawancensu saboda makarantarsu ɗaya, abinda yake so ta sani shi zai iya bijirewa Badaru amma ita fa? Inta bijire me auransu zai tsinana? Aure babu albarkar iyaye? Wai ma ta ina da kujerar guragu zai nufi Alhaji Sulaiman?
******
Abu ce ta kalli Kamalu tace “Ban gane lefe ka haɗa ba?”
Dariya yayi yana shan robar kunun ayan daya siyo yace “Ai ke na kula baki fahimceni bane, aure zan yi don komai ya kammala kayan kwalliya ne ban siya ba sai abayoyi da jaka da takalmi.” Katseshi tayi da cewa “Ba dai ka gama haɗawa ba dai zaka ce, wannan dogon lissafin da kayi ai yaci rabin kuɗin aikin.”
Kamalu ya ajiye robar kunun ayan yace “Ni dai don Allah ki bani ajiyar nan taki na saida na ƙarasa haɗa lefe na, kin dai ga suruka zaki yi sannan wannan surukar manya ce don haka kar ki wani damu da yawan kuɗin da kika kashe.”
Wani kallo tayi mishi tace “Ba dai wai zoben dana siya da gadon da aka raba mana kake cewa na baka ka saida ba?”
Kai tsaye yace “Shi mana, to menene amfaninshi dama idan ba kadara ba?”
Wani mugun kallo tayi mishi tace “Kaga bana son shirme, in zaka yi aure to fa ka haɗa komanka da kanka.” Tana kaiwa nan ta shige ciki tana mitar rainin wayon da yazo mata dashi.
*****
Bello kam gidan duk yayi mishi zafi bai isa ko falo ya fito ba Asiya zata haushi da masifa, duk ya rame ya jeme, abun takaici ta ƙi bashi key ɗin motarshi daya bata kafin ya tafi, don ya bar mata ne akan tayi amfani dashi tunda baya nan to yayi yayi ta bashi taƙi, sannan shi kunyar ma fita waje yake ji mutane su ganshi ga gida kullum datti, abinci wannan sai kame-kame yake ci, kallon mutunci ma taƙi yi mishi, gashi irin masifaffun matan nan ne da idonsu rufewa yake yi in suna bala’i. Yau kam ya gama gajiya da rainin wayonta dole ne ya taka mata birki, fitowa yayi a fusace ya shiga ɗakinta……..
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
*Da Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BIYU*
{82}