← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 168

Sashe 41

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sauraren Maryam kawai Umma take yi tana girgiza kai, dama tana yawan ji Maryam ɗin na kuka da uban mijin nata sai dai bata taɓa zama ta bayyana mata halin da suke ciki ba sai dai taji suna maganar yawanci ita da Baqeer ita kuwa bata saka musu baki. Hannu tasa ta ɗauke ƙwallar da suka taru a cikin idonta tace "Kiyi haƙuri Maryam, kowanne aure da kike gani da irin ƙalubalen da ma'auaratan ke fuskanta ba kuma zai yiwu kowane lokaci ace akan mahaifinshi kuke samun saɓani ba, ai shi ubanshi ne kuma dolen shi ne yayi mishi biyayya. Saboda Allah ta yaya ubanshi zai ce ga yadda za'a yi ke kuma kice ba haka ba ya yarda, kenan sai ya ɗauki maganarki sama data ubanshi saboda kawai baya son ɓacin ranki, ai ba haka ake zaman duniya ba abinda haƙuri bai baka ba kuma rashin shi ba zai taɓa baka ba. Kici gaba da haƙuri don Allah duk abinda kika san yana janyo matsala a tsakaninku ki dinga ƙoƙarin kiyayewa, ni ranar dana san baki faɗa mishi zaki zo ba ai da ban bari kin ɗauki Baqeer kin kai shi har mariri ba da sai nasa a nemo motar haya na tafi na kai shi duk ba wani abun damuwa bane.”
Haka dai tayi ta mata nasiha tana tausar zuciyarta kafin suka yi sallama ta ajiye wayar tana jin ƙarin damuwa akan wacce take ciki. Gaba ɗaya ƴaƴanta babu wacce ke jin daɗin zaman gidan miji, dama Baqeer ne tsaye akan al'amuransu to shima ga yadda rayuwarshi ta koma dole yana buƙatar matallafi kafin suga yadda rayuwa zata yi dashi, watakila idan hannunshi ya warke ya koma kan harkokin zanen shi komai zai warware musu tunda ai dama rashin yin zanen ne ya saka su a cikin halin da suke ciki, rashin yin zanen ne yasa Mallam ya juya mishi baya ya fitar da hannunshi daga al'amuranshi, tasan daga ranar da ya warke ya komawa harkokinshi komai zai gyaru, daga wannan ranar Mallam zai janye korar da yayi mishi daga gidanshi don zai ga nakasar data sameshi bata hanashi cigaba da al'amuran rayuwarshi kamar da ba, sai dai kuma yaushe ne zasu ga zuwan wannan ranar? Dole ta tashi ta tsaya da ƙafafunta har zuwa lokacin da Baqeer zai samu lafiya ya koma kan harkokin nashi, kafin nan dole ne ta zama jaruma jajirtacciyar mace mai tsayawa ta nemi na kanta ba tare data jira sai wani yayi mata ba. Zata tashi ta kama sana'a komai runtsi komai wahala don ta tallafi rayuwarta data iyalinta.

*****
Zainab na ƙoƙarin shiga gida ta hango samari tsaye a gate din gidansu, da mamaki ta karasa wurin, mai gadi ne ke ta mata alama da karta ƙaraso sarai ta gane sai dai bata bi ta kanshi ba ta nufo gadan-gadan zata shiga.
Jikin motarta suka nufo hakan yasa ta gane Najib dake ɗaya daga cikinsu. Kai ta girgiza tare da furzar da iskar bakinta, wato dai yau mutane neman kaita bango suke yi da shirmensu na sunan soyayya?
Knocking din glass ɗinta yayi, ta zuge tana yi mishi wani irin kallo na takaici, ya ɗan jingina da ƙofar motar yace “My Zeey mun zo wurin Kb ne zamu fita su kuma abokaina ganinki suke son yi.”
Kallansu tayi tace “Hi!” tana ɗaga ƴan yatsunta guda biyu.
Matsowa suka yi suna murmushi, tana kallon Najib tace “Babu laifi ai, hope ka faɗa musu mun yi north-west?”
Kallonshi suka yi tana ɗan murmushi tace “Kada ku damu ya samu wata ne, so ba wani issue bane, J bye sai munzo biki.”
Tana kaiwa nan ta shiga cikin gida zuciyarta na sake tafasa don sam ba wannan shirmen bane a gabanta, ita tunanin yadda zata taimaki Baqeer kawai take yi, ko yaci abincin? Fuskarta ta shafa tare da takaicin halin da ta shiga.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#Zeey
#Kamalu
#Sanyin Zuciya
#Rayuwata

*Na Umm Asghar*
*Da*  
*Ayusher Muhd🏌🏻‍♀️
*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR*

{25}

  Nabeela ce ta kalli Kabir wanda ke ta watso da kaya ƙasa a cikin ɗakin shi cike da kulawa tace “Ya Kabir me kale nema ne?”
Kallonta yayi yace “Please ki fita, ko me nake nema ba ɗaki na bane?”
Jikinta ne yayi sanyi ta fara neman barin ɗakin sai kuma yasa hannu ya riƙo rigarta yace “Sorry raina ne a ɓace ba wai wulaƙanci bane takardu na shigo dasu jiya kuma ban gansu ba.”
Ajiyar zuciya tayi cike da damuwa tace “Takardun menene? Akwai dai wanda Zainab ta kai ɗakinta jiya amma su na mota ne.”
Sakinta yayi ya fito daga ɗakin cikin sauri ya shiga ɗakin Zeey, akan dressing mirror ya gansu, ƙwafa yayi ya sake dubawa ganin komai yadda ya ajiye yasa ya ɗauka ya fito fuskarshi sam babu alamar walwala.
Zeey ce ta shigo ranta duk a ɓace ama barta da damuwar Baqeer wannan mahaukacin da wannan yaron na neman ƙona mata rai, takardun ya nuna mata bayan ya tare ƙofar shiga yace “Uban wa yace ki ɗaukar mini takardun motar nan?”
Kallon takardun tayi a wulaƙance sannan ta kalleshi tace “Kaga don Allah banda lokacin wasu takardun motarka, na shiga ɗakinka na gansu na ɗauka motar da aka ce za’a saya mini ne ka shigo da takardun, shine na ɗauka don na duba.”
“Kawai daga ganin abu a ɗakina sai ki ɗauka ko kin tambayeni ne?”
Saman goshinta ta shafa tace “Please! Ya isa haka ba gashi ka ɗauka ba sai ka sakasu a abinci kaci…….”
Cikin ɗaga murya yace “Malama ni kike yiwa magana haka?”
Mummy ce ta fito da sauri da alama ma sallah take yi don sanye take da hijab, kallonsu taiy tace “Zaku fara ko?”
Zeey ce ta fara neman wucewa ciki don bata da lokacin Kabir balle shirmen da yake yi.
Kallon Mumy yayi yace “Wallahi wata rana sai na fasawa yarinyar nan baki in dai ni zata dinga yiwa magana a haka.”
Zeey ko kulashi bata yi ba ta wuce cikin falo, tana jiyoshi ya fita wurin abokanshi tare da bugo ƙofar da ƙarfi.
Kallon Nabeela tayi tace “Meya faru?”
Nan ta sanar da ita abinda ya faru cike da ɓacin rai tace “To ke menene naki na sanar dashi? Sai ki zo ki faɗa mini gashi nan yanzu a dalilinki kin janyo musu sun samu matsala?”
Zeey dake falo tana jiyosu ta dawo tace “Mummy menene laifinta a ciki? Gaskiya ta faɗa ni fa bani da lokacin Ya Kabir neman faɗa kawai yake ji, sannan idan ya dawo ki sanar dashi kada ya ƙara janyo ruɓaɓɓun abokanshi gidan nan su tare mutum suna yi mishi shirme inba haka ba wata rana sai na faɗa musu magana.”
Yadda Mummy take kallonta ne yasa ta shagwaɓewa ta shiga ɗaki cikin jin haushin kanta yanda takaici da damuwat halin da Baqeer ke ciki yasa duk hankalinta yaƙi kwanciya.
Nabeela ta sake kalla fuskarta a ɗaure tamau tace “Kin dai san nace a’a ko? To wallahi bana son hauka in ba haka ba ki tattara ki koma gida.”
Wani abu ne ya tokare mata maƙoshinta sai dai bata iya cewa komai ba sai juyawa data yi idanuwanta na sake ciccikowa da ƙwalla ta bar wurin.

******
Kamalu daya biyo Zee a mota ashe yana ganin sanda Najib ya jingina da mota wanda hakan ya sake tunzuro shi, nan da nan kishi ya turnuƙeshi, Roshni ɗin tashi wani soko zai tare? Bayan shi ya gama shirya rayuwar love da ita? Ko kallon ƙauna data yi mishi ɗazu kaɗai ya tabbatar mishi ta gama amsar soyayyarshi.
Tsayawa yayi a gefe har saida yaga sun shiga mota sannan shima yabi bayansu, a wani restaurant suka yi parking da motocinsu uku suna shiga ciki ya fito da ƙusoshi ya jera a ƙasan tayoyin yana yi yana waige-waige wai kada a ganshi, daya gama yayi wani murmushin jin daɗi ya shige motarshi yayi tafiyarshi ko banza dai ai ya rama.
Haka ya dinga yawo a gari yana nunawa abokanshi motar babanshi wai shima yau gashi nan an bashi, wani wurin ma nuna musu yake yi kamar motarshi ce.

Su Kabir da Najib suna fitowa suka yi reverse suka bar wurin wanda shirmen ƙusoshin da Kamalu yasa bai yi musu komai ba.
Chapter 41 · 0% Book details