Sashe 31
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
{19}
Tana shiga soron gidan ta ganshi daga bakin ƙofa ya ƙurawa ƙofar shigowa gidan ido sai dai idan ka lura sosai zaka gane hankalinshi ba'a wajen yake ba yayi nisa sosai wajen tafiya duniyar tunani. Tsayawa tayi tana kallonshi ta ƙara tabbatarwa da kanta lallai fa shine dai Baqeer ɗin data sani ba wani daban ba, kafin taja jiki ta shige cikin gidan tana jin wani irin tausayin shi yana ratsa ta. A tsakar gidan ta tsaya tana sallama, Umma da ɗakinta ke a kusa da ƙofar shigowa ta fito tana amsa sallamar. Ganinta a tsaye yasa ta washe baki tana cewa "Ah ah Zainab kece? Lale lale sannu da zuwa, shigo daga ciki.” Bin bayanta tayi itama tana murmushin, kujera ta nuna mata ta zauna ita kuma ta koma bakin gado. Ɗan russunawa Zeey tayi ta gaisheta, da fara'arta ta amsa mata tace "Jiya kuma sai kika tafi ba tare da kin jirani ba, har waje na leƙa ban ganki ba.”
Sai ta samu kanta da jin kunyar Umman kada tayi tunanin ko guduwa tayi saboda ganin halin da Baqeer ɗin yake ciki. Kanta a ƙasa tace "Kiyi haƙuri Umma wai fa zuwa nayi na gaisheki na kuma ƙarbi number wayar Maryam ranar mun haɗu har muka rabu kuma ban samu na ƙarba ba, sai dai ruɗewar da nayi da yadda naga Yaya Baqeer ya koma yasa na fice ba tare da ko sallama na tsaya yi miki ba.” Ta ɗan ja numfashi kaɗan tana murza tafin hannunta a saman cinyarta, kafin ta cigaba “Umma ni kam meya faru dashi haka na ganshi a wani hali daban saɓanin yadda na sanshi ada?”Hawaye ne ya sulmiyo daga idanunta tasa gefen rigarta ta share. "Kin dai ga yadda Allah ya mayar da Baqeer, ƙaddara ce ta afko mishi wacce bawa bai isa ya kauce mata ba tunda haka Allah ya hukunta, wani ne ya kaɗeshi da mota sanadin hakan ya rasa ƙafafunshi likitocin sun ce sun tashi daga aiki baza su ƙara moruwa ba,” ta ƙarashe maganar kukan da take riƙewa a cikin ranta na ƙwace mata, damuwar data yini a ciki ce ta taso mata lokaci guda har ta kasa riƙe kanta a gaban Zainab ɗin.
Duk sai Zainab taji babu daɗi ganin yadda Umman ke kuka kashirɓan gaba ɗaya tausayinta ya lulluɓeta, tashi tayi ta koma kusa da ita ta zauna ta kamo hannayenta ta riƙe cikin tausasa murya tace "kiyi haƙuri Umma, ƙaddararshi ce tazo a hakan kamar yadda kika ce kuma bawa bai isa ya kauce mata ba, Allah ya sauƙaƙa mishi ya bashi ikon cinye jarrabawar da yayi mishi".
Da ƙyar ta iya tsayar da kukan tana jin kunyar yadda ta tasa yarinya a gaba tana yi mata kuka sai dai kuma damuwar dake danƙare a cikin ranta ce ta taso mata lokaci guda tafi ƙarfinta, a halin da ake ciki yanzu bata san ya zata yi ta kai Baqeer asibiti ba gashi ita bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba bare ta samu abinda zata yi hidimar kula dashi, dama shine ya ɗauke mata dukkanin wasu buƙatunta to ga kuma ajin da rayuwa ta kai shi shima a yanzu neman mai taimaka mishi yake yi. Sun jima shiru babu wanda ya ƙara magana sai zuwa can Zainab tace "Umma zan tafi Mummy tace kada na daɗe".
"To Zainab nagode kin ji, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.”
"Ameen Umma" tace tana nufar ƙofar ɗakin sai kuma Umma tace “Yau ma zaki tafi baki karɓi lambar Maryam ɗin ba?” Juyowa tayi tana dariya tace "Wallahi na sha'afa bayan kuma abinda ya fito dani kenan.”
Dariya itama Umman tayi ta ɗauko wayarta ta lalubo number Maryam sannan ta miƙa mata wayar ta kwafa. A daidai wannan lokacin Mallam Badaru daya kasa zaman kasuwa saboda ɓacin rai ya shigo yana ƙwalawa Umma kiran da duk wanda yaji yasan bana lafiya bane. A take jikinta ya hau ɓari ta fita daga ɗakin jiki na rawa har zanin jikinta yana kuncewa tsabar ruɗewar da tayi. Tana fita tsakar gidan taga ya janyo Baqeer ya dangwarar da keken nashi a tsakar gidan, komawa yayi ɗakin yana watsi da duk wani kaya da yasan na Baqeer ɗin ne. Sai daya gama fitowa dasu tas sannan ya fito, nunata ya hau yi da ɗan yatsa yana cewa "Wallahi na gaji, na gaji da zaman nakasashen ɗan nan naki a gidana, na gaji da zunɗena da nunani da mutane suke yi duk lokacin dana fita waje ana yi mini dariya saboda kawai naso ɗanki na fifita shi a cikin ƴaƴa gashi yanzu da abinda yazo ya saka mini, duk wani ƙoƙarina na ganin ci gabanshi a rayuwa ya tashi a banza, to bazan iya ba gashi nan ki fitar mini shi daga gidana don na tsani na buɗe ido na ganshi, yaje can yayi rayuwarshi inda bazan dinga ganinshi ba bare ya saka mini cutar hawan jini.”