Sashe 11
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai kawai Baqeer ya kauda daga inda Salim yake zaune yana ƙoƙarin kai mishi abinci bakinshi, hannu yasa ya amshi cokalin da hanunshi na dama, faɗuwa cokalin yayi saboda karayar dake hannun, sake ɗauka yayi nan ma spoon ɗin ya faɗi, gaba ɗaya Baqeer tsoron abinda ke faruwa dashi ne ya sake kamashi, nan da nan yasa hannun hagunshi ya ɗauki cokalin yana jin wani irin zafi da raɗaɗi na sake dabaibaye mishi zuciya, shi kanshi Salim tausayinshi ne duk ya rufeshi, nan Baqeer yayi spoon ɗaya wanda yake jin abincin ya koma mishi tamkar maɗaci saboda ɗaci, da ƙyar ya haɗiye na bakinshi sannan ya maida cokalin ya ajiye kafin ya rufe ido. Addu'a kawai ya samu kanshi dayi akan Allah yasa duka waɗannan abubuwan dake faruwa dashi su kasance mafarki ne ba gaskiya ba.
Sallamar Bello ce tasa ya sake runtse idanunshi, yana ji Bello na yiwa Salim magana akan halin da Baqeer ɗin ke ciki yace "Salim ashe abinda ke faruwa kenan? Ni ina can Kaduna ban san aminina na cikin wannan halin ba? Wallahi ranar da muka kawoshi asibiti washegari na tafi Kaduna akan akwai wani aikin zane da wani yake so za ayi wai na decoration ne za'a saka a hotel din daya buɗe, Baqeer ne ya haɗani da mutumin saboda shi ya fara nema shi kuma sunata shirin tafiya Baba baya so yayi nesa da gida, sam zuciyata bata kawo abin ya kai girman haka ba."
Cike da jimami Salim yace "Ayya!"
"Amma dai ba da gaske bane kafafun Baqeer sun samu matsala ko?” Bello yayi tambayar cike da tsoro, Salim gaba ɗaya kasa amsa mishi yayi sai dai kawai ya girgiza mishi kai alamun babu magana “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Kawai Bello yake faɗa gaba ɗaya ya kasa iya cewa komai, meke faruwa da aminin nashi haka? Mutumin da future ɗinshi a shirye take taya wannan mummunar ƙaddarar zata afka mishi? Da ƙyar ya jinginar da kanshi jikin bango yana maida ajiyar zuciya, ya daɗe a haka kafin yace “Amma dai babu abinda ya samu hannunshi ko?”
Salim ya sake girgiza kai yace “Wannan karaya ce kawai sai dai matsalar warkewar ba yanzu ba.”
Hankali a tashe Bello ya matso kusa da Baqeer cike da wani irin mugun tausayi, zuciyarshi na wani irin harbawa na tsantar tausayin abinda ke faruwa da abokin nashi.
A hankali Baqeer ya buɗe ido ya zubawa Bello dake tsugune kusa dashi, idanunshi sun yi jaa sosai, da ƙyar ya iya ƙaƙalo wani wahalallen murmushi wanda iyakacin sa leɓensahi cike da jimami yace “Baqeer wannan wani ibtila’i ne ya samemu?”
Kai kawai Baqeer ya girgiza dan baya jin ma bakinshi zai iya furta wani abun. Bello ya cigaba “Ɗazu Yallaɓai ya kirani ina hanya akan yana ta nemanka bai sameka ba idan ya kira Baba kuma sai yace mishi baka gida, wai yana sin ku haɗu gobe akan maganar tafiyarka, yanzu ya zamu yi da wannan ƙaddarar?”
Idanun Baqeer ne suka cigaba da kara kaɗawa suna yin jaa sosai, babu shakka shidai kam rayuwarshi ta ƙare, da ace babu karayar hannun nan ma da watakila abun yazo mishi da sauƙi, ina zai kai burin daya ɗauka akan gasar nan? Auren da zai yi fa? Ƙannenshi daya yiwa alƙawari zai taimakawa su samu jarinsu mai ƙarfi fa? Mahaifinshi da yake jira ya faranta mishi da kyautar daya samu fa? Nan da nan ya shiga jin wani abu na harbawa a saman ƙirjinshi, nan ya fara fitarda numfashi da ɗan sauri da sauri, da sauri Bello ya riƙeshi yace “Baqeer ya isa haka nan, dan Allah ka rufa mana asiri kar wani abu ya sake samunka.”
“Allah gani nan a hanunka, ka ɗauki raina kowa ma ya huta da wannan wahalar da nake shirin ɗaura musu, ni ban faranta musu na sauƙaƙa musu ba gashi ina ƙoƙarin sanyasu cikin uƙuba.” Abinda Baqeer kawai ke faɗa a cikin ranshi kenan, cike da tausayi Bello ya ajiye ledar dake hannunshi ya kalli Salim yace “Bazan iya zama anan ba zuciyata sai ta buga saboda tausayin Baqeer inda wani abin ka taimaka ka kıranı ka sanar min zan dawo gobe In Allah ya kaimu.” Yana kaiwa nan ya fita da sauri bai tsaya ba sai a cikin motarshi, shiru yayi yana nazari dan ko motar ya kasa kunnawa, can ya ɗauki waya ya kira Asiya.
A lokacin tana kwance akan gado ranta duk a ɓace, Habi na zaune a ɗakin tana gugar kayansu da suka bushe dan tun sassafe tayi wanki, Asiya sam bata wankin kayanta in har Habi na gida a ganinta ita babbar yarinyace mai karatun degree wacce tasan ƴan dabarun daɗin bakin da take tasa Habi tayi mata komai.
Habi ce ta kalleta tace “Asiya kin kira kinji ya jikin Baqeer ɗin kuwa?”
Tsaki tayi tace “Habi dan Allah ki bar maganar nan, kema kin san bazan kira ba kin san taurin kaina.”
Ajiyar zuciya tayi dan tasan halin yayar tata, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka ganin Bello ne bata san me zai ce mata ba saboda har yanzu a ƙasan ranta tana skn Baqeer.
Tana ɗauka suka gaisa yace “Asiya kin je duba Baqeer kuwa?”
“Naje amma ban shiga ba.” Ta faɗa tana kauda kai, cike da zargi yace “Me yasa? Ko tausayi?”
“Umm” kawai tace tana ƙoƙarin kauda maganar da cewa “Kaje Kadunan?”
Daɗi ne ya kamashi ganin yau ta tambayeshi abinda ya shafeshi yace “Naje, kuma Alhamdulillah na samu kuɗi sosai sannan sun ce zasu sake kirana saboda sunji da ɗinaikin da nayi musu.”
Kai ta jinjina tace “Congrats Allah ya ƙara buɗi ni zan kwanta.”
Da sauri yace “Baqeer har da hannunshi suka karye fa?”
Cikin sanyin murya tace “Na sani, sai da safe.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar, Bello ne ya dafa kanshi yana jin wasu tunanuwa na ɗarsar mai a zuciya, waya ce ta shigo wayarshi, ganin sunan Yallabai yasa yayi ajiyar zuciya ya ɗauka cikin fara’a suka gaisa sosai Yallabai ne yace “Wai ku haka ake abu? Taya zan yita neman amininka wayarshi a kashe? Ko wayarce ta lalace ai zai iya kirana ta wurinka ko ta wurin Babanshi, menene kuke yi haka ne? Bayan kun san jibi zamu je ganin Deputy Gomna akan tafiyar mu.”
Bello yayi ajiyar zuciya ya kasa magana, ran Yallabai a ɓace yace “Bana son iskanci fa, wani abun kuke ɓoye mini ne?”
Bello ya sake ajiyar zuciya yace “Yallabai ka kira Baba ka tambayeshi ni tsoron yin magana nake yi.”
A fusace yace “Kenan dai wani abun ya faru? Da kaina zan je gidan gobe.”
Bello yace “To Yallabai in dai da taimakon da kuke buƙata ku sanarmin.”
Kashe wayar yayi ya fara wani tunani kafin ya tada motar ya bar wurin.
******
Washegari da safe Baba da kanshi yazo yace sai an sallami Baqeer, duk yanda ake lallaɓashi akan yayi haƙuri ya barsji ya ƙara samun sauƙin bai yarda ba, haka nan suka sakashi a keken guragun da Baban ya siyo suka turashi zuwa mota shi kuma ya tsaya ya amshi magungunan da aka rubutawa Baqeer ɗin ya fito don shi dai ba zai bari su ruguza mishi shirin da suka daɗe suna yi ba. Da ƙyar Bashir da Salim suka cicciɓeshi sakashi a cikin motar.
Salim ya kalli Baba yana son yace zai bisu amma yasan halin faɗan Baba da rashin son yaga Baqeer da abokai.
Baba har yaje zai shiga mota sai yace “Kai da mota kazo?”
Da sauri yace “A’a adaidaita na shigo.” Ya sani sarai magana Baban ya faɗa mishi tunda shi dai ba motar nan ce dashi ba, alamu Baba yayi mishi da kanshi akan ya shiga baya kusa da Baqeer, hakan yasa Salim shiga, duk wannan abinda ake yi Baqeer na zaune idanunshi na kallon window yana hango satin daya gabata fa yazo duba Auntyn Asiya asibitin nan ta haihu suka zo tare suna tafe suna ƴar soyayyarsu, cike da farin ciki da annashuwa, wai yau gashi sai dai ya kalli waje ta window amma babu damar ma ya taka? Yana jin Salim ya shigo har suka fara tafiya babu mai magana a cikin motar, can Baba ya kalli Bashir yace “Kai kuma yaushe zaku koma makaranta?”
Da mamaki Bashir ɗin ya kalli Baban dan tun wancan wata aka koma ya sanar da mahaifin nasu amma yace bashi da kudi ya jira in an biyasu kuɗin tafiyar Baqeer zai bashi yayi registeration ɗin, da aka turo kuɗin ya sake yi mishi magana sai Baban cewa yayi ya jinkirta yaga nawa Baqeer ɗin zai bukata sai ya duba ragowar in zai isa a bashi yayi registration, shima tun daga nan bai sake bin Baban da maganar makarantarshi ba, a rayuwa har mamakin Baba suke yanda bai damu da kowa ba a cikinsu banda Baqeer din, bai damu da rayuwar da suke yi ba sai ta Baqeer wanda hakan yasa kiyayyar Baqeer ta gama shiga zuciyoyinsu kaf ɗin su babu mai sonshi har kuma wannan lokacin babu mai tausaya mishi, su ganin hakan ma suke yi da Allah ne yayi musu sakayya.
Yawun bakinshi ya haɗiya yace “Baba ka manta nayi maka maganar tun kwanaki?”
“Ka shirya gobe ka sake yi mini magana sai kaje ka biya, dan naga kai har yanzu ba hankali kayi ba baka san abinda ya kamata ba, karatun nan shine gatanka.”
“Toh” kawai ya iya cewa don bai ma san me zaice ba kuma, a ƙofar gida suka sauka, haka suka kinkimeshi da ƙyar aka saka shi a keke sannan suka turashi ciki.