Sashe 87
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Baqeer yanzu abubuwa sun kankama, dan yankan ɗinki inya maka sai ka riƙe baki, sai dai baya dinkawa sai dai Tanimi ya haɗe mai, shi kuma in da na wuta ne yake yi, kafafunsa Alhamdulila yana jin canji sosai a tattare dasu, duk bayan sati biyu yake zuwa asibitin Junaid, wanda tunda yaga ya daina zuwa da Zainab ya haɗa shi da wani physiotherapist ɗin dan sama shi saboda Zee ya nace da zuwan Baqeer ɗin. Shi kuwa Baqeer ko a jikinshi hakan ma da ɗi yamai ko banza dai yanzu baya ganin Zee. Kamar yanda suka saba yau haka sukaje makaranta sun gama kenan suka shiga adaidaita suka dawo gida, a hanya Baqeer ya tsaya ya saiwa Dada lemo da ayaba, yana tafe yana kallan gari da yanda kowa ke ta hada-hada, har suka isa gida nan Tanimu ya fito da keken shi kuma ya hau yana mai godiya, hannu yakai zai fara turawa sai yaji an fara turashi, da mamaki yace "Tanimu karka...." Sai kuma yaga Tanimu a gabanshi, sai a lokacin yajuyo kamshin turaren da yake sai mata wanda yanzu ta daina ma kamshin turarenta ta koma na wanda yake sai mata, baice komai ba itama batace komai ba ta tura keken suka shiga soron gidan shi kuma Tanimu yai musu sallama ya tafi, a soron ta tsaya ta kalleshi tace "Are you okay?"
Sai a lokacin ya kalleta, idanuwansu ne suka haɗu da juna wanda a wannan lokacin sukejin kaunar da sukewa juna ta wuce duk tunanin mutum sai dai ita bazata fara cewa tana sanshi ba alhalin bata san matsayinta a cikin ranshi ba, shi kuma bazai iya cewa yana santa ba saboda ajinta ya wuce ace tayi soyayya ko ya auri gurgu, ya tabbatar tausayi ne kawai take mai shima da kunya ya dubeta yace yanaso.
"Da me kenan?" Yai tambayar idanunsa cikin nata, kallan shigarta yai riga ce ta ɗan wuce mazaunanta kaɗan sai pencil jeans sai kuma kanta datai rolling da mayafi, yanayinsa ne ya canza nan danan kishi ya turnikeshi taya zata fita a haka? Zee kuwa sam ta manta da shigar da tazo dan hankalinta sam ya tafi da jin auren Asiya. Katse mai tunani tai da cewa "Your Ex itace tai aure ko?"
Kallanta yai yace "Oh I thought wani abin ne, yeah na gani." Ta ɗan mai wani kallo tace "Na ɗauka zan ganka kana zazzabin aureta da akai."
"In akwai so da matsayi kenan a zuciyar mutum ko?"
Kai ta jinjina tace "Yanzu babu?" Tai tambayar cike da san jin amsarsa, wani shanyayen kallo ya mata wanda yasa taji duk komai na jikinta ya sage yace "A haka kike yawo?" Kallan jikinta tai nan taji shakuwa tazo mata, mai makon ta amsa mai tai saurin shigewa ciki tana ƙiran sunan Dada.
Dada kuwa tana jinta ta fito tace "Lale da Abu na ai saura kaɗan na sa cigiyarki gidan radio nidai bana iya jure rashin zuwanki dayawa." Rungume Dada tai tace "Allah sarki Dada ta bana san zuwa ne akai-akai kar wasu su fara tunanin gunsu nake sintiri." Tai maganar tana kallan Baqeer, wanda ke zaune ya harɗe hannu yana kallansu, Dada ta kalleshi itama tace "Tab to ba sai suyi tunaninsu su gama ba ni dai nasan guna kike zuwa dan kuwa bazaki zo gun Baqeeru ba yo wannan ma me zai kawoki gunshi? Yaran da magana ma sai ya dinga shan kamshi kafin yai?" Kallansa tai tana guntse dariya ta tace "Ah to Dada kema kinsani ai," cike da zolaya take maganar, lemon ya ajiye yai hanyar ɗakin shi sai dayazo daf dasu yace "Da ɗinta ma nasan ba guna ake zuwan ba." Dada tai caraf tace "Yadai fi maka, ah to tun kafin ka hanamin ita zuwa gwara da ka sani." Har ya shiga ɗaki tana satar kallanshi shima sai dayaje ƙofa ya waigo, da sauri ta ɗauke kai tace "Dada wallahi aikena akai na gudo ganinki bari naje zan dawo."
"Kai nidai bangaji da ganinki ba amma bakomai ki taimaka ki dawo." To tace sannan ta juya, Baqeer kasa shiga ɗaki yai har sai da ta bar gidan, idanu ya lumshe inama ba a kujerar guragu yake ba ya sanar da ita abinda ke ranshi? Ya zaiyi da wannan san dake cika mai zuciya? Zeey kuwa gun aiken da Mumy ta musu ta nufa ga mamakinta Nabila bata nan, waya ta mata sai jitai wai tana gida batajin da ɗi, kai Zeey ta girgiza a fili tace "Itadai Aunty Nabs batasan zuwa gun in ba dani ba, na rasa wace irin kunya gareta." Nan ta nufi gida tana mamakin kunya da kara irinta Nabila sam bata hayaniya ko faɗa bakaji tanayi, itafa sam bazata iya irin wannan abubuwan ba dan ko yanda bata iya faɗar abu in ranta ya ɓaci mamaki take bata.
****
Asiya Amarya da Bello an tare an kuma sha roman soyayya, ya kashe kudi dan duk kudin da aka bashi na tafiya ya juyesu a bikin nan, Abuja sukaje ya kama musu hotel sukai kwana biyu sannan ya wuce ƙasar Germany inda anan zasuyi jarabawar shiga, duk wanda suka ɗauka zasu ɗau ki nauyin iyalinshi da karatunshi har na tsawon shekara biyar. Asiya haka suka zo airport babu abinda take sai ɗaukan selfie tana sawa a IG kwanan nan da ɗi takeji, ji take kamar tafi kowace mace gata, shiyasa yanzu ba kowa ma take kulawa ba, Habi ma in tana mata magana kamar wata ƴar aikinta haka take mata, shima Bello duniya tai da ɗi matsalarshi ɗaya mahaifansa da suke neman takura mai, shiyasa yanzu yakejin da ɗi zasu bar kasar ma su huta, sunyi akan in yaje yai wata ɗaya zaizo ya ɗau keta dan itama tay applying visa, haka ya wuce ita kuma ta hau jirgi ta dawo Kano tawa Habi waya akan tazo su zauna saboda batasan zama ita kaɗai, taso kin zuwa sai dai mahaifinsu ya sata taje a ganinshi bai dace a barta ita kaɗai ba.
****
Wace irin shakuwa ce mai ƙarfi ke ƙara shiga tsakanin Baqeer da Zainab, a koda yaushe yana bata mahimmanci a ranshi saboda yanaji Allah ne ya kawota cikin rayuwarshi dan ta daidai ta mai ita, a yanzu yafi da farinciki duk kuwa da bashi da ƙafa a kalla yasan me yakeso yasan yai abinda zai kwantar mai da hankali, ba kamar da wanda Badaru ke kula da duk wani motsinshi ba, komai nashi sai da izinin Badaru gashi yai ta wulakanta ragowar kanensa saboda shi, wannan abu ya dade yana damunshi.
Yau Baqeer ne zaune yana yanka shadar da ya siya zai dinkawa Hassan da Husaini da kuma Areef, yanajin da ɗin yanda a yanzu baya taɓa rasa kuɗi kuma haryanzu kuɗin filinshi bai cinye ba, ya tanada ragowar ne dan siyan keken wuta na electric da kuma shirin buɗe shago da yake san yi, wayarsa ce ta fara ƙara alamar an mai waya, kallanta yai ganin wata number yasashi jinkiri kafin ya ɗaga bayan sun gaisa ne mutumin yake sanar dashi akan shine wanda watanin baya ya nemeshi akan zanen da zai dinga musu. Baqeer ranshi ne ya ɓaci ganin sunzo da rainin wayau, taya tun nemenshi da sukai a baya basu sake nemanshi ba sai yanzu? Yanzun ma yasan daga wayar ba wani abu dazai faru. Katse mai tunani yai da cewa "Kayi hakuri matata tace Allah ya mata rasuwa sai abubuwan duk suka tsaya min komai ya fita daga kaina." Nan danan kuma sai jikin Baqeer yai sanyi yace "Allah ya mata rahama." Ya amsa da ameen sannan yace "Na shigo Kano inaso mu haɗu in ba damuwa gobe." Ya jinjina kai yace "Allah ya kaimu, ka turomin lokacin sai nazo." Nan suka tsara inda zasu hadu sukai sallama, sai dai haryanzu baije farinciki ko doki ba aganinsa sai yaga komai ya tabbata zai kwantar da hankalinsa, sam bai yadda da mutane ba yanzu.
*****
Kamalu kam duniya tamai zafi shiyasa yanzu in ba ɗau ki dadai da yake a shagon Baba ba babu abinda ke rage mai zafi, gani yake gwara ya ɗauka ya fara tara lefe a dabarance, ya tabbatar Roshini intaga akwatinan laifi goma sha biyu to fa tabbas yasan zata sara ma kaunar da yake mata, za kuma tasan lalai shi ɗin saurayi ne da a ke yayi ake kuma sha'awar aura.
*****
A zabure Kabir ya ture Nabila ganin aika-aikar da sukai, nan da nan kanshi yaji yayi wani irin sarawa, me ya aikata? Abinda ya faru daren jiya ne ya fara dawo mai..........
(😑😑Gaba daya Umm Asghar kasa motsi tai, Kabir da Nabila, Ayusher ce ta kalleta jikinsu gaba daya ya kame .)
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
DA
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA HAMSIN DA HUƊU
{54}