Sashe 38
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta hau cewa tana tafa hannaye, "kai kuwa garin yaya aka yi haka?"
Kasa faɗa mata yadda aka yi yayi sai ce mata yayi wai ya ajiye shi ya shiga shago sayen abu kafin ya fito har anyi gaba dashi. "Yanzu dai Inna ɗan wani abu zaki bani naje na sayi wani don wallahi yadda na saba da babur ɗinnan bazan iya komawa yawo a ƙafa ba".
Dariya ta saki haɗe da shewa tace "to kai in banda abinka baga motar Mallam nan ba don me kaima baza ka riƙa karɓa kana tuƙawa ba".
"Hmm Inna kenan, Baban ne zai yarda ya bani motarshi?"
Da sauri tace "yo me zai hana bayan a yanzu gida ya dawo hannunmu, dama ai saboda wancan gurgun yasa yaƙi kowa amma yanzu da idanunshi suka buɗe ya gane ashe shayi ruwa ne ai dole ya dawo wajenmu mu ɗin dai daya watsar, kada ka samu wata damuwa duk lokacin da kake da buƙatar motar ka faɗa mini kawai ni nasan yadda zan bi dashi na karɓar maka makullin daga haka wata rana ma har sai kaga ya bar maka motar gaba ɗaya in yaso shi ya sayi wata",
Suka saka shewa harda tafawa kamar wasu abokai, Kamalu dai daɗi fal ranshi don yana ganin kamar Roshni taso shi an gama ne in dai har yayi dace da samun motar nan....
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA UKU*
{23}
Zeey tana jin isowar mahaifinsu ta fito daga ɗaki suna gaisawa bata jira wani abu ba tace "Daddy don Allah gobe ina son zuwa Ɗambatta." Ai kafin ta ƙarasa maganarta ya tsuke fuska tamau kai kace saƙon mutuwa aka kawo mishi, fuskar nan babu alamar wargi yace "Kina sake yi mini maganar Ɗambatta wallahi ranki in yayi dubu sai ya ɓaci."
Sosai itama ta canza yanayin fuskarta tace "Daddy wai haka ake rayuwa?"
"Haka ake rayuwa? Ni kike yiwa magana haka?" Yayi maganar cikin ɗaga murya da tsawa, da sauri Mummy ta ajiye abinda take yi a kitchen ta taho wurinsu tace “Senate ya isa haka nan don Allah, ke kuma wuce ɗaki.”
A fusace yace “Bata isa ta tashi ba sai ta faɗa mini dalilin da yasa ba’a isa ayi mata magana ba sai ta mayar da martani, akwai sa’anta anan ne ko kuwa don mun kashe kuɗi mun kaita waje karatu shine take neman juye mana abubuwan banzan data koyo a can?”
Kasa tayi da kanta ranta na sake ɓaci, daga maganar Ɗambatta sai ya hau faɗa? Menene laifinta anan saboda Allah?
Mummy ce ta dafashi tace “Senate please ya isa haka kasan yarinya ce ba komai take ganewa ba.”
“Yarinya ce amma ta iya zabgawa Najib rashin mutunci ko? To wallahi wannan karon in har kika kori Junaid ki shirya auren duk wanda naga dama don kuwa baza ki janyo mini magana ba.”
Murmushi tayi ta kalleshi tace “Daddy in dai maganar Ɗambatta ne na daina amma please kai ma ka bar maganar Junaid, yaron nan fa sa’a nane kuma hatta ƴan matan da yayi da na sani.”
“Wannan damuwarki ce ko cewa aka yi don kin san ƴan matanshi shi kenan bazaki iya aurenshi ba?” Fahimta da tayi ran Daddy ya gama ɓaci yasa ta ɗan dafa kanta kawai sai gani suka yi tayi baya ta kwanta, a rikice Mummy ta taso Daddy ma haka duk ya rikice don Zeey ce sanyin idaniyarahi dauriya kawai yake yi yana yi mata faɗa don ya lura rashin tsawatar mata na nema yasa ta kangare, ɗagota Mummy tayi tana kiran sunanta cikin ƙarfi, a hankali ta fara buɗe idanunta tana lumshesu tace “Mummy ki bawa Daddy haƙuri….”ta sake maida idanunta ta rufe, hankali a tashe ya ƙaraso suka hau ƙoƙarin maidata kan kujera, Mummy ta kwallawa Kabir da Nabeela kira.
A kusan tare suka shigo falon, Kabir daga gefe yaja ya tsaya ranshi na sake ɓaci yace “Wallahi in baki tashi ba zaneki zan yi da belt ɗin jikina.”
Shareshi tayi tana ji Mummy nayi mishi faɗa ai kuwa Kabir ya nufota yana ɗan ware belt ɗin shi, ido ta buɗe kaɗan ganin yadda ya nufota yasa tayi saurin miƙewa ta ɓoye a bayan Daddy wanda mamaki duk yasa sun kasa magana, hararar Kabir tayi tace “Bro wallahi ka canza rayuwa.”
Ta kalli Daddy tace “Sorry Dad just joking.” Tana kaiwa nan ta ruga tayi ciki tana dariya.
Takaici ne yasa su dariya wanda Kabir yace “Daddy ka gani ko? Shi yasa nace ka barni da ita na gyara mata zama.
Zainab kuwa kwanciya tayi akan gado har yanzu dariya take yi, can ta tsaya da dariyar tunowa da halin da Baqeer yake ciki da tayi. Ko ya yake yanzu?
*****
Washegari…….
Umma tana kallon Baba yadda ko kallon ɓangarenta bai yi ba yake ƙoƙarin fita daga gidan, gaisuwar ma da take yi mishi bai amsa ba, cike da dauriya tace “Mallam nace nasa kujeru na a kasuwa saboda magungunan Baqeer tun jiya nake so na sanar da kai.”
Cak ya tsaya sannan ya waigo ya zabga mata wani kallo yace “Ya aka yi baki haɗa dake kanki ba?” Yayi maganar tare da ƙarasawa waje, ajiyar zuciya tayi sai kuwa ji tayi Abu na guda, fitowa tayi tana taku ɗaɗai ta wani turo ɗaurin ɗankwali gaba tana tauna chewing gum, Jamila ce ta fito sa sauri tace “Abu lafiya?”
Girgiza jiki ta ɗanyi tana wani yauƙi tace “Wallahi Mallam ne da wasan shiririta jiya goyani yayi a ɗaki shine yanzu nayi mishi maganar ya arawa Kamalu mota ya bani key babu ko musu.”
Jamila nan da nan ta ɗaure fuska tamau tace “Bayan Bashir ne zai shiga da motar makaranta yau kuma jiya ya faɗa mishi sai ya bawa Kamalu?”
Ta ɗan murmusa tace “To kinga ai bashi da laifi abinka da wanda so yake ɗawainiya dashi, mantawa yake yi da wasu abubuwan balle abu in ya shafi wanda suke zaune kara zube…..” ai kafin ta karasa magana Jamila ta cakumota rai a mugun ɓace, Abu tayi murmushi tace “To kin dai san hannunki in ya kai jikina za’a iya sallamarki.”
Jamila ta hankadata baya a fusace ta koma ɗaki, Fatima dake wanke-wanke ko kallonsu bata yi ba bare susa ran zasu ji ta tanka musu.
Abu ta sake yin dariya tace “To borori asha aikin gida da kyau.