Sashe 42
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
****
Umma yau haka ta wuni sukuku saboda tunanin halin da Maryam take ciki a gidan mijinta, ita kaɗai ke da mata biyu dake zaune anan garin, ƴaƴan Abu mata da suka yi aure su biyu ba’a Kano suke ba, daga Hadiza har Maryam babu wacce tayi dace a gidan aurenta, wannan abu na bala’in ɗaga mata hankali, tana nan a kishingiɗe hankalinta duk ya tafi kan tunanin ƴaƴanta sam bata kula da shigowar Baba ɗakin ba kawai sai ji tayi ance “Kefa yanzu gaba ɗaya kin zama mara mutunci ko? Har kin isa na shigo gidan baki ko ɗago kai kin kalleni ba bare nasa rai da gaisuwa?”
Da sauri ta miƙe zaune tace “Mallam sam ban ji shigowarka ba wallahi.”
Kallon ɗakin yayi ranshi na sake ɓaci yace “Au na ɗauka ai kin bi titi kema.”
Kallon mamaki tayi mishi don bata gama gane me inda kalamanshi suka nufa ba.”
Ya zabga mata wata muguwar harara yace “Bani.”
“Me zan baka?”
“Kuɗin kujerun ko da ke a naki haukar bar miki kuɗina zan yi? Ko ba da kuɗina kika sayi kujerun ba?”
Mamaki ya gama rufeta tace “Mallam kujerun nan fa Baqeer ne ya saya mini kuma kuɗin shi zan samu na tallafawa dasu.”
“Inyee? Fatima ni kike yiwa magana haka? Ni kike cewa Baqeer ne ya saya miki kujeru? To wallahi na saka ƙafar wando ɗaya dake a gidan nan, zanga in gurgun ɗan naki zai iya tallafa miki, ni zuciyata fari tas tunda ba shi kaɗai gareni ba sannan ina da lafiyayun ƴaƴa zan kuma nuna muku dukkanku a tafin hannuna kuke.”
Idanunta ne taji sun cicciko duk haƙurinta sai data ji ta kasa jurewa don haka tace “To Mallam tunda haka ka zaɓa mu bamu da ikon hanaka, sai dai shima ƙaddarace ta faɗo mishi ba yin kanshi bane.”
Ƙwafa yayi ya fice daga ɗakin ranshi a mugun ɓace, Jamila wacce dama take gadi a ƙofar ta sam bata so ya wuce bata tare shi ba tayi saurin fitowa tana lanƙwasa jiki da yanga tace “Mallam ashe ka dawo?”
Wani kallo yayi mata yace “Ke kuma meye hakan kike yi kamar wata mai ciwon haƙarƙari?”
Abu ce ta kwashe da dariya wacce fitowarta kenan tace “Kai Mallam yanga fa ake yi maka irin ta jan hankali.”
Tsaki yayi yace “Yanga ko hauka, ni bani wuri na wuce don Allah.”
Yayi maganar yana tureta ya wuce bangaren Abu, nan da nan zuciyar Jamila ta sake zafi ta dinga ji kamar zata yi hauka, kai tsaye ɗakin Fatima tayi wacce ke zaune tana tunanin yadda Mallam ya juya mata baya kamar ba ita ce ƴar lelenshin nan ba.
Tana shiga tace “Fatima wai haka zamu zauna Abu ta mallake Mallam muna kallo ba zamu ɗauki wani mataki ba?”
Ko kallonta bata yi ba tace “Ku mallaka ta dama ni dai don Allah kuje can ku karata.”
Jamila nan da nan takaici ya ƙara rufeta a fusace ta banko mata ƙofa ta fito, har ga Allah ita bazata taɓa yarda Abu ta ƙwace musu miji tana ji tana gani ba.
*****
Dada tayi mamaki da Baqeer bai musa ba data kawo mishi abincin dare, kuma banɗaki da kanshi yake gungura kekenshi yake zuwa, hakan ya sake tabbatar mata zuwan yarinyar nan ne yayi tasiri sosai a tare dashi, to wacece ita? Dole ta tambayi Maryam alakarsu don bata san me tace mishi ba amma tabbas tun bayan tafiyarta ya canza, washegari haka kawai ya samu kanshi da tunanin ko zata zo sai dai babu ita ba labarinta, murmushin takaicin kanshi yayi, iyayenshi ma suka gujeshi bare yarinyar da har yanzu ko sunanta bai sani ba, yarinyar da kawai ganinta yayi amma wai har wani sashi na zuciyarshi ke kwaɗaita jin muryarta, wanda ya tabbatar ko a hanya ya ganta ba lallai ya iya ganeta ba, to wai wacece? Wannan tambayar ita ce ke sake ƙona mishi rai, wayarshi ya ɗauka abinda tunda ya fara ciwo bai taɓa yi ba, dubawa yayi yaga Maryam ta saka mishi kati kawai ya gwada siyan data na kwana ɗaya, facebook ya leƙa inda ya dinga ganin hotunan Bello na tayashi murna da ake yi da kyaututtukan da aka bashi, har ya canza sunanshi ma zuwa MBB, wani murmushin takaici yayi ya sake duba wani hoto inda yaga Bellon riƙe da hannun mace wanda ko ba’a faɗa ba yasan Asiya ce, nan yayi deleting account dinshi ya ajiye wayar kawai.