← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 168

Sashe 75

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Tun safe yau gidan babu kowa, Abu ta fice kasuwa sayen kayan magungunanta ita kuma Jamila ƴar ƙanwarta ce ta haihu yau suna don haka ta fita da sassafe. Ita kaɗai ce a gidan tana zaune tana hutawa bayan gama dukkan wasu ƴan hidindimunta, Baqeer ne ya faɗo a ranta tana jin daɗin yadda rayuwarshi ta fara samun saiti, duk wannan ƙuncin da rashin walwalar ya tafi duk kuwa da bata je ta ganshi ba har yau tun bayan barinshi gidan amma tasan daga yanayin yadda take jin muryarshi a waya al'amuranshi sun fara daidaita. Tunaninta ne ya ƙara komawa kan takardun filinshi da suke hannun Mallam da tasan ko sama da ƙasa zata haɗe ba bayarwa zai yi ba, idan tace zata tambayeshi ma tasan ranta ne kawai zai ɓaci ya kuma zo bai bata ba. Kallon ƙofar ɗakinshi tayi sai taga ɗakin a buɗe ga alama mantawa yayi ya fita bai rufe ba don ba sabonshi bane barin ƙofar a buɗe saboda rashin yarda. Wani tunani ne ya ɗarsu a cikin ranta ai kuwa zuruf ta miƙe ta nufi ɗakin, tura ƙofar tayi ta shiga ta janyo akwatin data san yana ajiye dukkanin wasu muhimman abubuwa nashi. Buɗe akwatin tayi ta fara fitar da kayan ciki tana duba duk wata takarda da hannunta zai kai akai, cikin sauri take komai don bata so wani ya dawo ya isketa a ɗakin so take yi tayi abinda zata yi ta fita ba tare da wani mahaluki ya ganta ba. Sai da ta kusa gama fitar da kayan cikin akwatin Allah ya bata sa'a taga takardar da take nema. Hannunta har rawa yake yi data warware takardar taga itace dai wadda take nema, haka ta ajiye ta a gefe sannan ta mayar da sauran kayan data fitar cikin akwatin har ta gama ta ɗauke ta mayar dashi inda yake kamar bata yi komai ba ta fita ta janyo ƙofar ta rufe kamar dai yadda ta ganta, tana shiga ɗakinta ta samu wuri tayi mata kyakkyawan ɓoyo sai ranar da zata je ganin Baqeer zata tafi mishi da ita ta bashi tasan idan ya sayar da filin ba ƙaramin taimako kuɗin zai yi mishi ba, sai sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar da bata san tana riƙe da ita ba don fa har ta shiga ɗakin Badaru ta fito zuciyarta na bugawa don tsoro kasada kawai tayi ta shiga ɗakinshi ta ɗauko takardar nan amma tunda Allah yasa har tayi ta gama babu wanda ya ganta ta godewa Allah. Da yake yau ita ce da girki sai ta tashi ta cigaba da ƴan kujiba-kujibarta, ta ɗora sanwar abincin rana har ta gama babu wacce ta dawo. Har yaran ma yau babu wanda ya shigo, haka ta gama ta rarraba ta ajiyewa kowa nashi sannan ta gyara wurin, Fatima ba dai tsafta ba, duk cikin matan Mallam Badaru ita kaɗai ce bata barin wuri da datti ko tace sai tayi aikin yamma zata haɗa ta gyara, tana gama girki zaku samu ta gyare wurin tsaf kamar ba a nan aka yi aiki ba. Sai wuraren la'asar sannan Abu ta dawo niƙi-niƙi da buhun kayayyakin da take haɗa magunguna dasu, anan tsakar gidan ta dire buhun ta zauna tana sauke numfashi don sosai ta kwaso gajiya. Sannu da zuwa Fatima tayi mata, kai kawai ta iya ɗagawa sai faman haki take yi. Ita dai Fatima bata ƙara bi ta kanta ba sai ma cigaba tayi da aikin girkinta, dama can babu wani sakewa a tsakaninsu saboda haɗe mata kan da suka yi suka wareta a cikinsu shi yasa itama ta fita sabgarsu ta kama ƴaƴanta kawai take hidimarta dasu. Sai da ta gama hutawa sannan ta tashi ta shiga kitchen ɗin ta ɗauko kwanon abincinta na rana. Anan tsakar gidan ta zauna taci sai da ta ƙoshi tayi hani'an sannan ta kora da ruwa ta tashi tayi alwala ta shige ɗakinta don ko sallar azahar bata yi ba tana can tana bulayi wajen masu haɗa mata maganin mata.

*****
Baqeer yayi nasarar ɗora sketches ɗin shi akan sabon page ɗin daya buɗe akan IG da facebook har ma da tiktok da twitter. Cikin hukuncin Allah cikin kwanaki biyu da ɗorawa akan shafukan nashi sai gashi yaci karo da saƙonnin mutane  masu son designs ɗin nashi, godiya yayi wa Allah domin kuwa ba iyawarshi bace ko dabararshi tasa mutane suka nuna sha'awarsu ga kayan nashi. Tuni ya fara neman makarantar koyon ɗinki mai kyau inda yake so ya fara cikin ƙanƙanin lokaci. Da taimakon Salim ya nemi makarantar har ya sayi form ya cike ya mayar, a yanzu matsalarahi kawai kuɗin makaranta da zai biya, yana da kuɗaɗe a account ɗin shi amma ba wasu masu yawa bane ga baya son ya faɗawa Umma tunda yasan ba shi gareta ba kawai zai ɗaga mata hankali ne, gaba ɗaya ya damu don bai san yadda zai yi ya samu kuɗin ba, dama ya saka rai ne da samun kuɗi saboda wasu da suka ce suna son zai yi musu designing wasu kaya amma su zasu bayar da description na kayan sai ya zana to ya basu address ɗin gidan Dada akan zasu zo tun kwanaki biyu da suka wuce har yanzu shiru kake ji kuma basu ƙara nemanshi ba.
Shigowar Dada ce ta katse shi daga tunanin da yake yi tace "Tanimu yazo fa tun ɗazu kai yake jira.” Ajiyar zuciya ya sauke ya gunguro wheelchair ɗin tashi ya fito, anan tsakar gidan yaga Tanimun ya tambayeahi ko ya samo musu mai adaidata sahu? Yace "eh" Sallama yayi wa Dada suka fice daga gidan Tanimu yana tura shi. A ƙofar gida mai adaidaitan ya tsaya Baqeer ya faɗa mishi inda zai kai su ya kuwa yanka musu kuɗi, babu wani jaa Baqeer ya amince suka taimaka mishi ya shiga ciki sannan Tanimu ya naɗe wheelchair ɗin ya shiga suka tafi. Suna tafe Tanimu nayi mishi hira yawanci labarin garinsu ne da Innarshi sai ƙannenshi mata guda huɗu, mahaifin shi ya rasu shine wan uban ya kawo shi almajiranta wai a rage mishi nauyi. Jefi-jefi yake amsawa don hankalinshi ya kasu kashi biyu, ɗaya yana tunanin yadda zai yi mutane su san shi da sabuwar sana'arshi ɗayan kuma yana wajen tunanin Zeey da a ƴan kwanakin nan ta koyi shariya don ko gidan tazo sai tayi ta wani sha mishi ƙamshi tana basar dashi sosai hakan ke damunshi kawai dai yana dannewa ne kada ya nuna mata don bai cika son ya zura jiki ba kada yaje yayi nisan da zai kasa dawowa alhalin tafi ƙarfinshi ba iya samunta zai yi ba. Har cikin asibitin mai adaidaitan ya shigar dasu, da taimakon Tanimu ya zauna akan wheelchair, sai da ya sallami mai adaidaitan sannan suka shiga cikin asibitin. A reception ya faɗi number folder shi da kuma wurin wanda suka zo. "I know" kawai tace don tasan duk zuwan da suke yi Junaid ɗin suke gani. Sai da ta miƙa mishi folder sannan ta basu izinin shiga.
Shi kuwa Junaid yana ganin folder Baqeer wani farin ciki ya lulluɓeshi nan ya fara gyara zaman rigarshi yana murmushi don ya kwana biyu bai ga Zeey ba kuma ko a waya ba sosai suke magana ba sai dai suna shiga sai yaga wani saurayin yaro ne ya rakoshi babu ma abokinshi da suka saba zuwa bare Zeey da ita yake sa ran fara gani. Fara'ar fuskarshi ce ta ɗan ragu yace "ina kuma Zeey ɗin yau baku zo da ita ba?"
Wani malalacin murmushi Baqeer ya saki don haka yaji daɗi da Junaid ya zama disappointed da rashin ganin Zeey. Yaga murmushin da yayi sai kawai ya basar cikin ranshi yace "Wannan gurgun fa na lura har wani gani-gani yake yi mini akan Zeey sai dai kuma duk abun shi bai isa na bar mishi ita ba ko yana da lafiya kuwa bare a yadda yake da disability.” Haka dai aka yi session ɗin ranar zuciyar Junaid a cunkushe shi kuwa Baqeer sai daɗi yake ji, har da haka yasa ya hana Zeey yi mishi rakiya kamar yadda taso ta cigaba da kawo shi.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
       *Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
        *DA*
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA BAKWAI*

{47}

  Suna fita Junaid ya cillar da file ɗin Baqeer ƙasa, yau yaci burin ganin Zeey da soyayyar da zasu ci amma sai gashi komai bai tafi daidai ba, secretary ɗinshi ce ta shigo tace “In kawo tea ɗin?” Rai a ɓace yace “Mai tea ɗin zaki kawo.”
Yayi maganar tare da cigaba da aikinshi a computer cike da ɓacin rai, fitowa tayi tai shiru tana tunanin ina zata ga mai tea, da sauri ta fito bakin gate ta sanar da mai gadin rehab centre ɗin nasu akan ya kira mai shayin dake ƙasan layinsu tana tunanin ko yunwa yake ji yana son a bashi wani abun.
Babu dadewa kuwa sai ga mai shayi nan tace ya biyota, office ɗin Junaid suka nufa, yana zaune yana rubuce-rubuce, izini ya bata ta shiga shi kuma yabi bayanta, wani kallo Junaid yayi mishi yace “Waye?”
Hankali a kwance tace “Mai shayin ne don bansan me kake so ba.”
“Shayin me kuma?” Ya tambaya cike da mamaki, ta ɗan kalli mutumin dake tsaye sannan tace “Ɗazu kace in kira mai shayin?”
Wani kallo yayi mata yace “Nafisa ni kam hausa ce ba kya ganewa?” Da yake yoruba ce zaman Kano ne yasa ta iya hausa yasa tace “Ba haka kake nufi ba?”
Kai kawai ya girgiza ya sallamesu ya cigaba da aikinshi.
Chapter 75 · 0% Book details