Sashe 102
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Hanyar ƙofa tayi da sauri ya riƙo hannunta, kallonshi tayi kawai taji hawaye ya soma taruwa a idanunta, saman goshinta ta shafa sannan ta fizge hannunta tana cewa "Haba Yaya wannan wani irin son zuciya ne, taya zaka yiwa Mummy haka? How?" Kuka ne ya nemi k6wace mata kawai tasa hannu ta sake turashi baya, jikin ƙofa ya jingina ya sa hannu saman fuskarshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, ya zai yi da rayuwar nan? Kallonta yayi kamar zai yi kuka shima yace "Zeey sam nima ban san meya faru ba, ban tuna ba sam akan abinda ya faru kin dai san ba shaye-shaye nake yi ba."
Wani mugun kallo tayi mishi tace "Ranar da ta taimaka maka ka dawo ɗaki hope dai ba ranar bane?"
Kallonta yayi cike da rashin fahimta yace "Yaushe kenan? Don ni dai ban taɓa rasa hanyar ɗakina ba tunda dai kin san ba shaye-shaye nake yi ba."
Hannu ta ɗaga mishi tace "Ta ina zan sani tunda ba ganinka nake yi ba, sau nawa ake neman ka a gida ba'a ganinka? Sannan ranar am sure abinda ta fara ce mini kenan da yake bata son aga laifinka sai ta wayance."
Yanayinshi ɗauke da mamaki yace "Ban dai san me ya faru ba amma ni dai ba dai ni ta kawo ba sannan da kike magana haka ke kin san ma wacece Nabila ne?"
Tsaki tayi tace "Malam bani hanya na wuce don wallahi baka isa ka tozarta Mummy ina raye ba, kai ko tausayinta ma baka yi? Ko duba yadda ta riƙe mu da amana baka yi ba? Kana gani abubuwan da take fuskanta akan mu a dalilin mahaifiyar mu da danginta, sannan kana ganin yadda suke faɗa da Inna akan mu, wannan wani irin rashin imani ne......." Ta ƙarasa maganar cikin tsananin takaici wanda kana ganin takaici a idanunta, taya zai yi haka? Shi kanshi kalamanta sun saka yaji jikinshi ya ƙara sanyi shi yasa duk wani abu da zai yi yayi ƙoƙarin yi ganin ya janye jikinshi daga kanta, amma yanzu yasan ba mai ganewa babu wanda zai fahimceshi.
Ƙofa ta kama tana neman buɗewa da sauri ya ƙara maida ƙofar ya rufe yace "Ni kaɗai ne ɗan uwanki a duniyar nan, ki taimaki rayuwata ki jira na samu nutsuwa ni da kaina zan sanar in kuma har na wuce kwana biyu ban sanar ba na baki dama ki sanar wa Daddy ɗin, kiyi mini wannan alfarmar don Allah," ya ƙarashe maganar yana haɗe hannayenshi bibbiyu alamar roƙo.
Hawaye ne ya zubo mata tace "Kwana biyu kaɗai Yaya don ba zai yiwu mu mata ace kullum muke ɗaukan laifi ba." Tana kaiwa nan ta fita, kasa ko motsi yayi saboda takaicin abinda ya aikata, tsanar kanshi na sake ratsa ko ina na jikinshi, taya zai yiwa Mumy haka?
Nabeela da tun jin motsin Zee ta biyota duk abinda ya faru a ɗakin tana waje tana saurarensu, jin kalmar Zee na karshe yasa tayi saurin barin wurin tayi ɗaki tana shiga ta shige bargo ta fara kuka har da shesheƙa yadda za'a iya jiyowa daga waje.
Ita kuwa Zeey tana fitowa jikin ɗakin ta tsaya tana jiyo kukan Nabeela, tabbas ba zata iya haɗa ido da ita ba, haka ta koma ɗaki kawai ta kwanta ruf da ciki, takaici duk ya isheta sai take gani kamar ma abinda ya faru laifinta ne tunda da bata dage sai Nabila ta zauna anan ba tabbas da bai haiƙe mata ba. Waya ta ɗauko tana son yiwa Baqeer magana amma bata son ɗaga mishi hankali don ta tabbatar dazu ta sanya shi cikin damuwa. Duk yadda Zee take da dauriya akan abu amma yau ji tayi ta kasa bacci haka tayi ta juyi sai wajen asuba bacci ya ɗauketa.
*****
Habi ce ta kalli Asiya tace "Kinga tashi zan yi na koma gidan mu ba zai yiwu ki dinga yi mini abu kamar wata uwata ba."
Cike da gadara tayi tsaki tace "Aikin banza gidan naku menene a ciki banda kunu? Ƙosai wannan ba kullum ake samu ba, amma nan kin samu banza sai ki dafa indomie ki soya kwai da dankali gashi nan duk kin cinye kayan abincin da My love ya siyo."
Baki kawai Habi ta saki kafin ta tuntsire da dariya tace "Malama tashi daga baccin da kike yi, ke ɗin ƴar wacece? Kema ai ƴar kunun ce da shi aka raineki da shi kika girma."
Yatsa ta nunata dashi cike da ɓacin rai tace "Wallahi ki shiga hankalinki dani, wai ni sa'arki ce ko kuwa don kinga na ɗaukeki kamar kawa kike son ki mayar dani marainiyar wayonki?" Harara itama ta zabga mata tace "Kinga kafin ma ki sallameni gidan kunu zan koma, gidan shayi asha da madara lafiya." Tana kaiwa nan ta miƙe ta fara haɗa kayanta a cikin jaka, takaici yasa Asiya jan tsaki ta koma ɗakinta tana cewa "Kiyi ki gama nasan dawowa zaki yi don yadda kika saba da cin mai maiƙo ba iya zaman gidan naku zaki yi ba, ta kalli wayarta cike da takaici don wallahi sai ta yiwa Bello wulakanci in har bai turo mata kudi yau ba, gaba ɗaya account dinta dubu biyar kacal take dashi ga kayan abinci da yawa babu, ita dai yayi sauri yazo ya dauketa su tafi don ba zata iya wannan rayuwar ba, rayuwar talauci da jiran sai an bata. Gara itama ta tafi daga can ko ta wataya ta ƙara zama babbar yarinya.