Sashe 112
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*****
Umma cikin baccinta taji kamar ana ƙwala mata kira, ita ba yara ƴan makaranta ba balle ta tashi da safen nan, ga sanyi da ake a gari, abin mamakin ma daga waje ake kiran nata ba ciki ba. Fitowa tayi da sauri tana cewa “Malam lafiya? Allah dai yasa ba wani abun ne ya faru ba?” Wani banzan kallo yayi mata yace “Yau wai ba girkinki bane?” Mamaki ya kamata wanda ya bayyana a fuskarta tace “Girki nane amma kiran na menene?” Da hannu ya nunata yace “Kinga bana son shirmen banza da wofi ki fito yanzu kisa a siyo wake da mai don ƙosai nake son ci da kunu.” Baki ta ɗan buɗe kaɗan tace “Malam haka kawai da safe kace ƙosai zaka ci da kunu? Ina ma masu shagon suka buɗe?” “Eh lallai wuyanki ya isa yanka, to a cikin kuɗina na kujeru da kika cinye ki ciro kisa a siyo wake da mai, sannan ayi mini kunu wallahi in lokacin fita ta yayi ba ayi ba za’a gamu da ɓacin rai na.” Kallonshi tayi jiki a sanyaye tace “Malam kaji tsoron Allah rabona da in ganka ma a ɗakina har na manta balle kuɗin cefane da zaka bani ranar girki na, kana son cewa har wannan lokacin kuɗin kujeru muke ci?”
“To in ma ba na kujeru bane da alama kuɗin sata ko haram kike ci tunda ke dai ba kudi gareki ba ba kuma sana’ace dake ba, ni dai na faɗa miki in fito inga abincin da nake so,” yana kaiwa nan ya shiga ɗakin Jamila yana cewa “Zan koya miki hankali da kaina, ina zaune zaki ɗauki jakarki ki bar mini gida.”
****
Ƙarfe bakwai Mummy ta haɗa breakfast a kan dining, Daddy ne ya fito fuskarshi sam babu walwala wanda kana gani kasan ba wani baccin kirki ya samu ba, zama yayi sannan ya kalleta yace “Bani wayata na kira Kabir.” Miƙa mishi tayi tana cewa “Senate ka saki ranka please kaga dai akwai important meeting da zaka yi yau.” Murmushi kawai yayi baice komai ba, sai kiran Kabir da yayi yana zama ya kira Zeey itama. Kallonsu yayi yana cin haɗin soyayyen dankali da kayan ciki wanda yasha attarugu da tattasai da albasa sai ƙamshi ke tashi, fuskar nan tashi babu walwala yake cin abincinshi, babu alamun zasu ci don dukkansu da alama cikin ɓacin rai suke, Daddy ne ya kalli Zeey yace “Jiya kin dai ji me nace miki ko?”
Kanta tsaye tace “Naji amma ba abinda zai sa na aureshi bayan tun farko na faɗa maka ni bana son shi.” Wani kallo yayi mata sannan ya kalli Kabir yace “Ka shirya anjima kaje gidan Alhaji Nafi’u kaga yarinyarshi mun riga mun gama magana auren ku zan haɗa nayi ƙarshen wani watan kuma wallahi duk wanda yaƙi bin umarnina zai gamu dani.”
“Daddy me kake cewa? Taya zan yi aure a cikin wannan yanayin? Ana wannan case ɗin?” Kallonshi yayi yace “Wani case kenan?” Da mamaki Zeey da Kabir suka kalleshi, ya cigaba da cin abincinshi yana cewa “Oh wai tsautsayin daya afka kan Nabila? Baiwar Allah ƙaddara ce ta afku mata amma da zarar yayarta ta fita da ita komai zai dawo daidai.” Zeey bata san sanda tayi wani murmushin takaici ba tace “Na ɗauka ma daka kira shi haƙurin dukan daka yi mishi ka farfasa mishi jiki zaka bashi sai ma kazo da wani zance? Taya ma zaka ce yayi aure? Ita kuma Nabila fa”
Tamke fuska yayi sosai ya tashi yana kallon Kabir wanda shima kallonshi yake yi, babu tsoro yanzu ko shakkar Daddy da yake dashi a da, yace “Na dai faɗa maka,” yana kaiwa nan ya fita daga falon, shima Kabir fita yayi ya bar gidan ma gaba ɗaya.
Mummy ce ta kalli Zeey wanda gaba ɗaya suma yanayinsu babu daɗi sai dai basu da ta cewa, haka ta fito ita da Nabila suka shiga mota suka bar gidan suma.
A hanya Nabila tace “Saukeni.”
Mummy ta kalleta tace “Kema kin san baki isa ba, tun kafin ki ja mana matsala gwara ki kwantar da hankalinki aje a cire cikin nan, kafin ma ki lalata rayuwarki don Kabir ma aure zai yi.”
Gabanta ne yayi wani irin faduwa tace “Aure?”
Mummy bata kulata ba sai cigaba da jan mota da take yi, Nabila ta fara sakin wani irin ihu tana jijiga ƙofa kai kace zararriya ce tana ihu tana cewa “Buɗe ni, buɗe ni ko wallahi na ce satoni kika yi.” Tsoron abinda Nabila ke yi yasa Mummy yin parking ai kafin ta gama daidaita motar ma Nabila ta fita, adaidaita ta shiga ta wuce gidan Inna tana tafe tana kuka kai kace wani ne ya mutu. Tana shiga gida tun a tsakar gida ta ƙara buɗe maƙogwaro tana zabga ihu, Inna daga ciki ta jiyo ihu cike da tsoro ta fito, mamaki ne ya kamata ganin Nabila nan ta rungumeta tace “Nabila? Menene?” Kuka sosai take yi kamar ranta zai fita a cikin kukan tace “Inna na shiga uku, Kabir yayi mini ciki ta ƙarfi sannan yanzu mahaifinshi yace aure zai yi mishi da wata bani ba.” Jikin Inna ne ya fara rawa da sauri tayi baya tana maimaita kalmar ciki? Ciki? Ina zan sa kaina da wannan abun kunya a karo na biyu? Baya tayi saboda jin wani duhu ya mamaye mata idanuwanta, jikinta har rawa yake yi take cewa “Kaini gidan wallahi ba zai yiwu ba, kaini gidan yanzun nan Nabila.”
Da yake abinda take so kenan da sauri ta fito dama tace mai adaidaita ya jirata tunda tasan Inna dama dole taje gidan, haka suka juya gidan Inna sam ta kasa nutsuwa zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, kanta na wani irin zafi. A falo suka samu Mummy don dama tunda Nabila ta gudu ta dawo gida, ta zauna a falo tana tunanin abun yi ko dai ta tashi taje wurin Inna ne tayi mata bayani? Ai kafin ma ta bawa zuciyarta amsa taji ance “Shashashar banza shashashar wofi wallahi kin yi asara ke dai kam baki ji daɗin halinki ba, ki sadaukar da komai naki kiƙi haihuwa dashi amma ƴarki ƙwaya ɗaya baza ki iya amsar mata hakkinta ba? Jininki guda ɗaya dake duniya shine ba zai iya kula miki da ita ba?” Mummy a zabure ta ɗago ta kalli Inna waigawa tayi da sauri tana fatan babu wanda ke wurin sai dai me? Daddy ta gani tsaye a bakin ƙofa don har yayi nisa ya tuna ya bar wasu takardu ya kuma kira number Mummy bata ɗauka ba, jikinta ne ya fara rawa, me zata gani Zeey na tsaye a jikin ƙofar ɗakinta don jin hayaniya yasa ta fito, wasu zafafan ƙwalla ne suka zubowa Mummy shikenan rayuwarta ta ƙare……..
(Baki a sake muka kalli juna, meke faruwa? Me Inna ke nufi da kalamanta? Tana son cewa Nabila ƴar Mummy ce ko kuwa dai kuskuren harshe ne tayi?)
ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA TAKWAS*
{68}