Sashe 113
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba ɗaya parlourn ya ɗauki wani irin shiru na wasu ƴan mintuna, sai a sannan Inna ta ankara da ɓaramɓaramar da tayi. Hankali a tashe Mummy ke kallon Daddy, wani irin kallo yake yi mata daya ƙara sawa jikinta yin sanyi. Baki ta buɗe zata yi magana sai dai ta rasa ma me zata ce. Ƙarasa shigowa cikin parlourn Daddy yayi yace "Me nake ji Inna tana faɗa Halima?" Jikin Mummy ne ya ɗauki rawa sai girgiza kai take yi ta kasa cewa komai. "Da gaske ne Nabila ƴarki ce da kika haifa ta cikin ki ba ƙanwarki ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar, Mummy dai babu baki sai ido. Wata irin gigitacciyar tsawa yayi mata yace "magana nake yi miki ki buɗe baki ki amsa mini shin Nabila ƴarki ce ko ƙanwarki?" Gaba ɗaya sai ta sake rikicewa don tunda take da Daddy bata taɓa ganin fushin shi irin wannan ba, in banda hawaye babu abinda ke kwarara daga idanunta.
Wani irin kallo Daddy yake yi mata sai ya juya ya kalli Nabila dake tsaye a gefen Inna yana ganin kamanni na zahiri tsakanin Mummyn da Nabila kamannin da bai taɓa tsayawa ya lura dasu a tsakaninsu ba saboda duk lokacin nan a zaman ƙanwarta take a wajenshi. Hannu yasa ya tura hular daje kanshi baya ta faɗi a ƙasa. "Lahaula wala ƙuwwata illa billah,' kawai yaje ambatawa. Tuni ya manta da batun meeting ɗin da zashi da mantuwar da yayi ta dawo dashi gidan har yaji wannan mummunan zancen mai kama da almara.
Ƙara kallonta yayi sai yaga gaba ɗaya baƙinta yake gani, cikin wata irin masifaffiyar murya da duk wanda aka yiwa amfani da ita sai ya ruɗe yace "duk tsawon shekarun da muka ɗauka tare baki yi tunanin akwai wata rana da zata zo ba da zan iya sanin cewa ita ɗin ƴarki ce shi yasa kika zaɓi ki ɓoye mini?"
Cikin rawar murya tace "Senate," hannu ya ɗaga mata alamun baya son jin komai daga bakinta. Juyawa yayi ya kalli Inna yace "kun san cewa Nabila ba ƙanwarta bace ƴarta ce amma kuka rufeni baku taɓa sanar dani ba? Akwai wani abu da kuke ɓoyewa ne?" Gaba ɗayansu suka yi shiru ita kanta Inna a yadda taga Daddy ya birkice musu a yau wani irin mugun tsoronshi ne taji ya kamata.
Wani tunani ne ya ɗarau a ranshi sai ya waiwaya ya ƙara kallon Mummy yace "kun ma je inda na turaku kuwa?" Ɗan shiru tayi tana tunanin to ina ya turasu, aka kuma ta tuna ashe fa asibiti yace suje a zubar da cikin jikin Nabila. Da kai ta amsa mishi don a yadda take jin bakinta yayi mata nauyi baza ta iya furta kowacce kalma ba. A fusace yace "baku je saboda kema kina son Kabir ya auri ƴarki?" Murya ba rawa tace "ba haka bane Senate, wallahi ba haka bane zan kaita."
"Da dai ya fiye muku don na faɗa miki Kabir ba zai auri Nabila ba ba a gidana za'a yi wannan kwamacalar ba ace ɗana yana auren ƴar matata wacce kowa yake yiwa kallon ƙanwarta, mun riga mun gama magana da Alhaji don haka tun wuri gara ku san yadda zaku yi da cikin nan, ba kuma naso maganar ciki ta ɗara parlourn nan kin san idan ta fita ba ƙaramar illah zata yiwa kujerar da nake nema ba don haka ku kiyaye." Nabila na jin abinda Daddy yace ta zube a wurin tana birgima tana ihu akan ita dai a bar mata cikinta kada a zubar tsoro take ji. "Rufe mana baki mutuniyar banza, duk bake kika janyo mana ba da baki je kin bashi kanki ba hakan zai faru ne?" Inna tayi mata tsawa tana jin wani irin ɓacin rai na ƙara taso mata ɓacin ran da bata taɓa nuna tunanin zata ƙara jin kwatankwacin shi ba tun a shekarun baya da wani abu mai kama da wannan ya faru dasu.
Rarrafawa Nabila tayi wajen Daddy tace "Don Allah Daddy kada kuce sai an cire cikin nan wallahi tsoro nake ji ance mutuwa ake yi a wajen zubar da cikin, ka aura mini Kabir ɗin yadda asirinmu zai ƙara rufuwa in yaso sai ka aura mishi waccan ɗin ni na amince." Wani irin kallo yayi nata yace "Zancen banza kenan ko ki amince ko kada ki amince Kabir aure zai yi, maganar aure a tsakaninku kuma na haramta shi, ki tashi kuje a zubar da cikin kamar yadda na ce, ni zan samo miki miji daidai ke amma ba Kabir ba."
Haushin Nabila ne Inna taji ya kamata ganin yadda Daddy yake nanata ba zai aurawa ɗan shi ita ba ita kuma sai faman naci take yi kamar shi kaɗai ya rage autan maza. A fusace tace "Tunda yace ba zai aura miki ɗanshi ba ai sai ki haƙura muje a zubar da cikin don ba zan ƙara yin rainon shege ba, na dai yi ɗaya ba zan ƙara yin na biyu." Da wata irin ƙaƙƙarfar murya kamar ba tata ba Mummy tace "Inna!"
Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta, wai ita yau me yake damunta ne da take ta faman fallasa asirin da suka binne cikin ransu shekara da shekaru, asirin daya rabo su da ƙasarsu ta haihuwa duk don su samu su lulluɓeshi ba tare da kowa ya san shi ba.
"Don't tell me cikin shege kika yi kika haifeta Halima? No wonder itama tayi following footsteps ɗinki, tabbas barewa ba zata yi gudu ba ɗanta yayi rarrafe." Daddy yayi maganar ranshi na ƙara ɓaci sai dai kuma bai yi mamaki da jin cewa Nabila shegiya bace don yasan haka nan baza su ɓoye ita wacece ba inba don suna gudun asalinta ba. Zeey da tunda aka fara maganar nan take hawaye ta kalli Kabir fuskarta ƙunshe da mamakin abubuwan da suke taji yau ɗinnan. Ji tayi ba zata iya cigaba da tsayuwar ba don haka ta koma ɗakinta tana kuka, wannan wacce irin kwamacalar rayuwa suke ciki. Ace wai Nabila ƴar Mummy ce ta cikinta ba wai ƙanwarta ba kamar yadda kowa ya ɗauka. To ita kuwa Mummy me zai sa ta ɓoye musu irin wannan sirrin mai girma haka? A ganinta ai ko ta ɓoyewa kowa bai kamata ace su ta kasa faɗa musu ba tunda dai ai sun zama ɗaya yanzu tana ganin babu wani batun ɓoye-ɓoye kuma a tsakaninsu. To amma idan har Nabila ƴar Mummy ce me yasa take yawan kyararta tana yi mata faɗa alhalin ita ba haka take yi mata ba? Sam fa babu wata jituwa tsakanin Mummy da Nabila yadda take yi ma kamar haushinta take ji komai tayi sai tayi mata faɗa har ita tana mamakin yadda aka yi sam babu jituwa a tsakaninsu kamar ba ƴan uwa ba to ashe ma uwa ne da ƴarta sune basu sani ba. To ko dai haka duk iyaye mata suke idan ta duba taga yadda tasu mahaifiyar tayi watsi dasu tunda ta bar gidansu bata ƙara waiwayarsu ba sai ma ƴan uwanta dake yawan zuwa suna ɗagawa Mummy hankali duk don akan ta riƙesu kamar ƴaƴanta bayan ita data haifesu tayi watsi dasu ta manta ma tana da wasu ƴaƴa data fita ta bari.
Kwanciya tayi tama rasa abun dake damunta, ta rasa tunani guda ɗaya da zata yi a cikin kanta. Har yanzu ganin abubuwan da suka faru take yi kamar almara ko a cikin shirin film. Wayarta ta ɗauka ta rubutawa Baqeer text. "Komai ya kwance min Ya Baqeer na rasa ya zan yi." Ko minti biyu bata yi da ajiye wayar ba reply ɗin shi ya shigo yace "Are you okay? Me ya faru?"
Hawaye ne ya zubo mata don ganin reply ɗin shi ya sata jin wani irin rauni ya lulluɓeta. "Nothing was as it seems Ya Baqeer. Rayuwar nan gaba ɗaya ƙarya ce mutanen duniya mayaudara ne."
Hankalinshi ne yaji ya tashi don haka yayi saurin kiranta, tana ganin shine ta ɗauka sai ta fashe mishi da kuka. Tashin hankalin shi ne ya ƙaru sai cewa yake yi "Zainab menene? What happened? Are you okay?" Ita kuma kuka kawai take yi don a yanzu tana buƙatar yin kuka a inda za'a rarrasheta, ga matsalar rashin sanin matsayinta a wajen Baqeer ga matsalar auren da Daddy yake son ya ƙaƙaba mata na dole gashi Mummyn data kasance mata abar jingina a duk lokacin da take cikin damuwa ta sameta da ɓoye musu sirri mafi girma a rayuwarta a yanzu bata san wane matsayi zata ajiye ta ba kuma. Sai data yi kukanta ya isheta sannan tayi shiru, shima tun yana rarrashinta har yayi ahiru ya ƙyaleta tayi kukan sosai don ya lura kamar akwai abinda yake damunta. Sai data tsagaita da kukan sannan yace "Are you okay?"
Ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa sai kuma ta tuna ashe fa baya ganinta don haka ta buɗe baki tace "Eh," cikin dakusashiyar murya.
"Me ya faru kike irin wannan kukan Zainab?" Ya ƙara tambayarta. "Ashe mutanen duniya maƙaryata ne mayaudara Ya Baqeer? Ashe zaka iya zama da mutum na tsawon wani lokaci ba tare da kasan gaskiya guda ɗaya a kanshi ba?"
"Me ya faru? Waye ya yaudareki? Is it Junaid" Ya ƙara tambayarta muryarshi a cunkushe yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarshi, shi yasan dama Zainab tafi ƙarfinshi zai yi wuya ta iya son shi ko yana da lafiyar ƙafafu bare kuma a yadda yake ɗinnan.
"No, its not him," tace tana girgiza kai sai kuma tace "Thank you for lending me your shoulders to cry on," ƙit ta kashe wayarta ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya. Duk da ta yarda dashi tana ganin kamar bai kamata ta kwashe abinda yake faruwa a cikin gidan su ta faɗa mishi ba, tana ganin kamar wannan wani sirrinsu ne da ba kowa ya kamata yaji ba,