Sashe 107
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ta ƙarasa wurin da sauri tace “Daddy please!”
Wani kallo ya watsa mata yace “Ban taɓa tunanin har dake za’a haɗu a tozartani ba, a cikin gidana? No way!” Ya sake maganar yana ƙara zubawa Kabir bulala, yana zaune duk uban azabar da yake ji na zafin dukan bai sa ya tashi ba don dama tunda Daddy yaji yasan abinda zai biyo baya sai ya wuce haka, kallon Nabila yayi wacce tayi ƙasa da kai tana share ƙwalla, tana cewa “Daddy don Allah kayi haƙuri na tabbatar shima yayi dana sani, don Allah Daddy…..” kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata iya cigaba da abinda zata faɗa, ganin jini ta gefen wuyan Kabir yasa Mummy tace “Senate please ya isa haka.” Hannu ya ɗaga mata tare da cewa, “Tashi ki koma ɗaki wannafatan umarni ne na baki.” Mummy haka ta miƙe kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tayi ɗaki, ya sake ɗaga bulalan zai doki Kabir, Zeey tayi saurin tsayawa a gabanshi zuciyarta baza ta iya bari a cigaba da fasawa Kabir jiki haka ba, kallon Daddy tayi hawaye suka zubo mata tace “Daddy kar ka illatashi a zauna asan solution ɗin da za’a nema tunda mai afkuwa ta riga ta afku.”
“Kin matsa ko kema sai na zuba miki dukan a jiki? Ni zaku maida shashasha a gidana? To wallahi ba a gidan nan ba, babu wanda ya isa ya tozartani balle yaja mini mutane su fahimci gidana ma ban gyara ba balle in jagoranci mutane.”
Matsawa yayi daga inda Zeey take ya sake zubawa Kabir wani bulalar, ido ya runtse don shi kaɗai yasan me yake ji, saukar bulalar yaji sai dai ba a jikinshi ba, hakan yasa ya buɗe ido, ganin Zeey yayi a tsaye a daidai inda Daddy ya kai dukan, ya sani duk faɗan da suke yi da ita tana sonshi don kaf duniya su biyu ne a wurin mahaifinsu, kallon juna suka yi idanunta sun cicciko da ƙwalla don rabon da a daketa har ta manta, shi kanshi Daddy ganin Zeey ya daka yasa jikinshi yayi sanyi, kallonshi tayi tace “Daddy na roƙeka da Allah ka bar wannan dukan, sannan bafa abinda ya faru kake shakka ba tsoron siyasarka kake kaga mafita itace.”
Fuskarsa a tamke yace “Ba wani mafita shiryawa zata yi gobe ita da Mummy zasu je a cireshi, da hankalina babu wanda ya isa ya kawo min ɗan shege sannan ko an zubar bazan iya aura mata shi ba zan dai nemo mata wani ta aura, kai kuma wallahi in baka yi wasa ba gidan mari zan kaika aje can a rufe soko don wallahi baka isa ka lalatamin tafiyar nan ba.” Kai kawai Kabir ya saukar ƙasa yana jin wani irin ƙunci a zuciyarshi.
“Daddy zubarwa kuma?” Zee tayi tambayar cike da shakkun kalamanshi, wani kallo yayi mata ya yarda bulalar yace “ƙwarai kuwa don ba dai ni za’a haifawa cikin shege ba.”
Yana kaiwa nan yayi ciki yana sababi, wani kallo tayi wa Kabir wanda kana gani kasan na bacin rai ne sannan ta kamo Nabila suka bar wurin.
Tun a hanyar ɗaki Nabila ke kuka har suka shiga ɗaki ta kamo hannun Zeey tace “Zeey tsoro nake ji don Allah kar a zubar ba gwara muyi aure a huta ba?”
Kallonta tayi cike da tausayi kafin tace “Kin san Daddy ba zai yarda ba, ki kwanta ki huta In Sha Allahu komai zai tafi daidai.
Nabila tana riƙe da ciki tana cewa “Ni dai bazan zubar ba sai dai na shiga duniya, Zeey ki taimaka min don Allah, akwai aure tsakanina dashi me yasa kuke haramta auren bayan ya halarta?”
Tausayinta ne ya ƙara kama Zeey hakan yasa tayi ɗakinta jiki a sanyaye tana shiga ta kwanta akan gado tana jin kanta na wani irin sarawa, ga bayanta inda aka daketa har yanzu zugi yake yi mata, tashi tayi ta kalli madubi ta yaye rigarta ta baya sai ga shatin duka har ya fara tashi, nan da nan taji zuciyarta ta karaya, waya ta ɗauka ta kira Baqeer don muryarshi kawai take son ji.
Har sai data kusa katsewa don yanata yankan ɗinki sam bai ji kiran ba wayar tana silent, da sauri ya ɗauka sanda idanunshi suka kai kan sunanta na motsi a jikin wayar, karawa yayi a kunnenshi yace “Assalamu Alaikum!”
Cikin sanyin murya tace “Wa’alaikasalam da na ɗauka baka kusa.”
“Me ya sameki?” Tambayar daya jefeta dashi kenan, cike da mamaki tace “Me ka gani?”
“Yanayin muryarki ya canja, meya faru?”
Kwanciyarta ta gyara taja bargon duvet da aka yi gyaran gadon dashi tace “Abubuwa da yawa, ɗazu ma ganinka dana yi abu ne ya faru yasa na bar gidan, sai dai na yanzu yafi na ɗazu.”
Ɗan ajiyar zuciya ya sauke kaɗan yana cewa “Zancen ranan nan ne?”
Tana ƙifta ido gun dauriya tace “Eh!”
“Kenan solutions ɗin bai samu ba?”
Ta kara cewa “Eh sannan yanzu abubuwan ma sunfi lalacewa zance ya ƙarasa kunnen Daddy.”
“How?” Ya tambayeta yana ajiye scissors ɗin hannunshi, ita kanta tambayar data yiwa kanta kenan how? Taya aka yi ya sani bayan lokacin da ta fita baya gidan? Sannan ta tabbatar Kabir ba shi zai sanar dashi ba to meya faru? Muryar Baqeer ce ta katseta da cewa “Baki san ya aka yi ba?” Miƙewa zaune tayi tace “Ya Baqeer bye zan kiraka anjima.” Kai ya jinjina ga mamakinta ji tayi yace “Please ki kula da kanki.” Cak ta tsaya saboda kalamanshi sun shiga jikinta, shi kanshi jin abinda bakinshi ya furta yasa yayi saurin kashe wayar don tabbas abinda ke zuciyarshi ne ya fito fili ba tare da ya shiryawa hakan ba, shafar sumar kanshi yayi sannan ya ɗan maida hankali kan wayar yana cewa “Allah ya warware muku abinda ke faruwa.”