← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 168

Sashe 103

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

******
Cike da jin daɗi Baqeer ya kalli wayarshi, dubu dari hudu cif aka turo mishi. Wasu zafafan ƙwalla ne suka zubo mishi yana jin wani yanayi a cikin zuciyarshi na nutsuwa da salama, ya zai yi da wannan jin dadin? Sujudush shukr yayi wa Allah na godiya tabbas Allah shine maji daɗin bawa, in har yaso ya tasheka babu mai durƙusar da kai, miƙewa yayi ya dinga exercise ɗin ƙafar shi kafin ya sake kallon wayarshi, sunan Zainab ya fara dubowa sai kuma ya saki murmushi ya kira number Salim nan ya sanar dashi an biya kuɗin sannan yace suzo da yamma suje a dubo shagon da suka ce zasu kama, sai suga abubuwan da suke buƙata tunda yana da ragowar naira miliyab ɗaya da rabi na kuɗin filinshi da aka sayar, cike da jin daɗi Salim yace ai gani nan ma zuwa wannan ai ba abun jira bane.
Sallama suka yi cike da jin dadi dukkansu, anan ya turawa Umma dubu arba'in ya turawa Hadiza dubu ashirin ita da Maryam su raba sannan ya turo kekenshi ya fito falo wurin Dada.
Tana ganinshi tace "A'a cukumi an fito?"
Murmushi kawai yayi ya hau danna wayarshi, yana son kiran Zainab sai dai yafi so sai ya kama shagon har an zuba kekunan ɗinki kafin ya kaita taga wajen. Kallon Dada yayi yace "Dada menene bamu dashi a gidan nan yanzu Salim zai zo zamu fita sai mu sayo daga can." Ƙwalla ce taji ta taru a idonta, tunda Baqeer ya samu abun yi bai ƙara bari ta rasa wani abu ba a cikin gidan don kafin ƴaƴanta su kawo mata ya cire kuɗi ya sayo duk abinda yasan suna da buƙata, ita kuwa me zata cewa Baqeeru bayan ta cigaba da yi mishi addu'ar fatan alkhairi. "Shikenan daga tambaya sai kuka Dada, idan ba kya buƙatar komai ai sai ki faɗa ba wai ki zauna kina share hawaye ba." Maficin da take fifita dashi ta ɗauka ta jefa mishi sai dai yayi saurin kaucewa yana dariya, itama dariyar tayi tace "babu abinda muke buƙata Baqeeru, ka wadata mu da komai Alhamdulillah, Allah yayi maka albarka ya baka masu yi maka kaima." Murmushi yayi, sosai yaji daɗin addu'ar da tayi mishi har yana hango kanshi da Zainab a matsayin ma'aurata har ma ga ƴan ƴaƴansu data haifa mishi, wani irin farin ciki ne yaji ya kamashi cikin ranshi yana raya inama wata rana mafarkin shi ya tabbata ya zama gaskiya yana ganin da babu wanda zai kai shi farin ciki a duniya.
A daidai wannan lokacin Salim ya shigo yana sallama, ganin Baqeer a zaune yana murmushi shi kaɗai don tuni Dada ta tashi ta bar shi a wurin. Zama yayi akan shimfiɗar Dada yace "mutumina irin wannan farin ciki haka, halan wasu kuɗaɗen aka sake turo maka."
Tsaki yayi still murmushin bai bar fuskarshi ba yace "tun ɗazu nake zaune a wurin nan ina zaman jiranka, a ina ka tsaya?"
"Kasan lokacin da ka kirani ina kasuwa to sai da na sallami wasu customers kafin na rufe shagon na taho. Ina dai ka shirya mu tafi?"
Ɗaga mishi kai yayi kafin yace "eh, bari na ɗauko atm card ɗina. Sai dai a ina kake ganin ya dace mu nemi shagon? Da a tunanina ko nan unguwar sai kuma na duba naga nan ɗin yayi wajen gari da yawa ba kowa ne zai iya biyo mu nan ba shine nace bari dai na jira kazo sai muyi shawarar inda kake ganin yafi dacewa mu buɗe shagon, idan zai yiwu dai mu nemi wurin da yake center kasuwanci inda ko address muka bayar ba zai yi wahalar zuwa ba ba cikin lungu ko cikin unguwa ba, koya ka gani?"
"Hakan shawara ce mai kyau, In Sha Allah ina barin nan zan yi mana survey zan kuma bada cigiya a wasu wuraren da nake ganin za'a samu wuri mai kyau, ko kuwa yanzu kake ganin zamu fita neman wurin?"
"Eh akwai wasu shaguna da wani da muke koyin ɗinki tare ya faɗa mini su nake so muje mu gani daga nan zaka rakani shopping zan je nayi mana ƴan tsince-tsince." Komawa yayi ɗaki ya canja kaya sannan ya ɗauki atm card ɗin ya saka a aljihu ya fito, kallonshi kawai Salim ya tsaya yana yi domin sai yaga Baqeer ɗin gaba ɗaya ya canja mishi kamar wanda ake yiwa wankan inji, fatarshi sai sheƙi take yi tana glowing kamar ta jarirai ga wata ƴar ƙiba da yayi alamun ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali fiye da daa. Kantin da yake zuwa idan zai yi sayayya suka je, suna tafe suna ƴar hirar su duk akan yadda suke so shagon da zasu buɗe ya kasance. Sayayya yayi musu kamar yadda ya saba sai turaren Zeey da baya fashin saya mata duk lokacin da zai je sayayya irin wannan sai dai wannan karon ya haɗa mata da wata doguwar rigar abaya daya gani tayi mishi kyau, yasan idan ta saka a jikinta tabbas zata yi mata kyau shi yasa bai ji ƙyashin saya mata ba duk kuwa da cewa rigar tana da tsada don da yaga kuɗinta sai da ya jinjina kai amma Zainab is worth every penny he has, zai iya kashe mata ko nawa ne don yaga farin ciki a fuskarta.

*****
Umma na zaune a tsakar gida wajen da suke yin girki tana ƴan aikace-aikacen ta, Abu da Jamila na zaune kowacce a ƙofar ɗakinta, ita dai Abu ƙulle-ƙullen magungunan matan da take sayarwa tana yi suna zunɗen Fatima dake ta kaiwa tana kawowa ba tare data kula da me suke yi ba, tana cikin aikin Hadiza ta kirata ta sanar mata da saƙon da Baqeer ya tura musu ta account ɗinta ita da Maryam, bata san lokacin da ta saki wani murmushin farin ciki ba tana godewa Allah daya kyautata rayuwar yaronta bai bar shi ya shiga garari ba bayan da iftila'in rayuwa ya afka mishi, faɗa mata tayi ai itama ya turo mata kuɗin, nan dai suka taya juna murna domun basu yi zaton rayuwar Baqeer ɗin zata inganta har haka ba a yadda suka ga ya cire rai da rayuwa a lokacin da ya samu accident sai gashi yanzu komai ya wuce ya fara zama tarihi. Murya ƙasa-ƙasa Jamila tace "ita kuma wannan lafiyarta ƙalau dai ko naga tana dariya ita kaɗai." Kallonta Abu tayi ta yatsina fuska sannan ta ɗaga murya don Fatima ta jiyota ba kamar yadda Jamila ta saukar da tata ba tace "kika sani ko albishir ta samu nakasashen ɗanta ya warke." Suka kwashe da dariya gaba ɗaya harda tafawa, kallonsu Umma tayi tace "Abu kenan, nakasa ai ba kasawa bace jarrabawar rayuwa ce kuma mun karɓeta a yadda tazo mana muna kuma fatan Allah yasa mun cinyeta sannan kuma fata nagari lamiri idan akwai rabon zai taka a gaba sai kuga ya warke tunda abun duk yin Allah ne amma ko a haka Alhamdulillah tunda ya tsira da ranshi da lafiyarshi. Ina kuma baki shawara ki rage yawan izgili don baki san me gobe zata haifar ba sai Allah tunda dukkanmu rayuwar ba a hannunmu take ba bare muce mun san yadda ƙarshenmu zai kasance."
Miƙewa Abu tayi a fusace tace "aniyarki ta biki, wato tunda ɗanki ya zama nakasashe shine kike yi mana mugun fata to ta Allah ba taki ba."
"Ameen Ya Rabbi, aniyar kowa ta bi shi," Umma ta mayar mata itama don taga alama matan nan na neman ƙure haƙurinta, duk kawaicin da take yi musu basa gani har sai sun sa ta tanka musu sannan hankalin su yake kwanciya.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA UKU*

{63}
Chapter 103 · 0% Book details