Sashe 96
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kaikaice ya kalleta yaga yadda ta mayar da hankalinta gaba ɗaya a kanshi ya kawar da kai sannan yace "wacce irin magana kenan? Wai don Allah Nabila me yasa ba zaki sama mini lafiya bane? Nace miki ba zai yiwu mu gina wata alaƙa a tsakaninmu ba bayan mun san dangantakar dake tsakaninmu saboda Allah me yasa ba zaki fahimta bane?" Wani malalacin murmushi ta saki irin na takaici, sai da tasa hannu ta ɗauke wasu sirararan hawaye da suka biyo kuncinta sannan ta juyo ta kalleshi muryarta na rawa tace "ni na daɗe da sanin baka ɗaukeni a yadda ni na ɗauke ka ba Kb to amma ya zanyi? Bani na ɗaurawa kaina ba Allah ne ya ɗaura mini sai dai ni ba abinda ya kawoni wajenka ba kenan abinda ya kawoni daban da wanda kake tunani." Kallonshi tayi sosai taga hankalinshi ya dawo kanta kafin tace "banga period ɗina ba wannan watan abinda yasa nake zaton ciki ne dani." Wani irin sanyi ne Kabir yaji yana ratsa shi kamar wanda aka yiwa wanka da ruwan ƙanƙara, me Nabila take so ta faɗa mishi? Anya kuwa ba mafarki yake yi ba don shi dai ba zai iya tuna wani abu ya shiga tsakaninsu ba duk da dai ita ta musanta amma ta yaya za'a yi ace yayi abu ba tare da yasan yayi ba, shi ko a cikin bacci bai ji alamar yayi abu makamancin wanda ita tace sun yi ba to ta yaya zata yi ciki bayan shi bai ji wani alamu na wani abu ya faru tsakaninsu ba.
Wani kakkauran yawu ya haɗiya da ƙyar ya iya ƙwato muryarshi yace "Kin kuwa san abinda kike faɗa? Wane irin ciki kuma Nabila? Kin ma tabbatar lokacin period ɗin naki yayi? Nifa har yau ban yarda wani abu makamancin wanda kike faɗa ya faru a tsakaninmu ba don har yau ban iya tuna lokacin da hakan ya faru ba to ta yaya zaki ce wai kina da ciki alhalin ni dai nasan babu wani abu daya shiga tsakaninmu."
Bata san lokacin da ta saki kukan da take riƙewa ba duk yau, kuka tayi mai yawa tana jin wani irin ƙunci a cikin zuciyarta. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan ta ɗago idanun da suka rike suka yi jawur dasu kamar an ɗiga musu barkono tace "Kana nufin ƙarya zan yi maka kenan ko me?"
Murya na rawa don hankalinshi idan yayi dubu ya tashi yace "Nifa ban ce ƙarya kike yi ba kawai dai na kasa tuna lokacin da hakan ya faru a tsakaninmu gashi kuma kina cewa wai ciki ne dake."
"Wai ne ma?" Ta tambayeshi idanunta na ƙara tara ruwan hawaye, hannu tasa ta ɗauke hawayen kafin tace "kasan dai ko ina ƙarya bazan yi irin wannan ba wacce zata janyo mini zubewar mutunci da ƙimata ta ɗiya mace, bana jin daɗi Kb yanzu kwata-kwata ko abinci bana iya ci ba tare dana amayar dashi ba gashi yanzu har Mummy ta fara gane halin da nake ciki, yanzu ya zan yi idan aka gane ciki ne dani Kabir?" Ta ƙarashe maganar tana mai fashewa da wani irin kuka da yake fitowa daga ƙarƙashin zuciyarta. Ita dai soyayya bata yi mata adalci domin kuwa gashi ta kaita ta baro, bata tsinci komai a cikinta ba sai dana sani.
Shi kanshi Kabir ji yayi gaba ɗaya hankalinshi ya tashi, gajiyar daya kwaso ma tuni ya nemeta ya rasa don wannan tashin hankalin yafi gaban gajiyar da yake ji a jikinshi. Komawa yayi ya zauna akan gadonshi suna facing juna, ya rasa wacce irin shawara ya kamata su yanke, tabbas bai kamata su bari wannan maganar ta fito ba don ba mutuncinsu ne kaɗai zai zube ba har da na iyayensu, yasan yanzu idan maganar nan ta fasu a gari haka za'a yi ta yawo dasu a social media bare idan aka ji dangantakar dake tsakaninsu. Sun jima a zaune shiru kowanne da abinda yake saƙawa a cikin ranshi sun kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi bare su tsara wacce zata fishe su. Agogon ɗakin ne ya buga ƙararraar dake alamta ƙarfe ɗayan dare tayi abinda ya dawo da hankulansu jikinsu. Kallon Nabila Kabir yayi yace "to ko zuwa zamu yi a zubar don kin san dai bai kamata mu bari wannan maganar ta fita ba ko?"
Tashi tayi tsaye dafe da ƙirji tace "a zubar kuma? Bayan ance mutuwa ake yi idan anje zubarwa." Shima miƙewar yayi yana jin takaicinta na neman kamashi ganin ita ta janyo musu shiga cikin wannan halin sannan kuma ya samo musu mafitar da yake ganin ita ce daidai tana neman ta kawo mishi tangarɗa. Ɗan ɗaga muryarshi yayi duk kuwa da cewa dare ne baya raina sauti yace "to me kike son ayi yanzu idan ba'a zubar ba?"
A sanyaye tace "ka yiwa Daddy maganar aurenmu tun kafin...."
"What?" Ya katseta a fusace jin maganar da take yi mai kama da a cikin tatsuniya ake yinta.....
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA TARA*
{59}
Hannunshi ta kamo tace “KB tsoro nake yi wallahi, don Allah kazo muje mu yiwa Daddy magana shi zai fahimci soyayya ce ta saka mu….” Fincike hannunshi yayi ranshi na ƙara ɓaci ya shiga jinjina kai yana cewa “Eh lallai na tabbatar kanki ba ƙalau ba, nama gama lura so kike yi mutane su fara nuna mu, sannan kina nufin Daddy shine zai bi bayanki? Shaye-shaye kike yi? To wallahi ki shirya gobe muje asibiti ki zubar da cikin nan, kin ji na faɗa miki, ni ba mahaukaci bane in ke baki da hankali.” Yana kaiwa nan yasa hannu ya jata ya turata waje ya kulle ƙofar shi, hawaye ne suka gangaro kan saman kuncinta a hankali tasa hannu ta share, tana juyawa zata wuce suka yi ido biyu da Zeey wacce ta tashi daga bacci ta nemi charger ɗin wayarta ta rasa, shine tayi tunanin duba ɗakin Nabila, tayi mamaki data shiga taga bata ɗakin don har toilet ɗin ɗakin a buɗe yake bare tayi tunanin ko tana ciki, haka ta fito cike da mamakin inda taje kawai taga Kabir ya buɗe ƙofa kafin tayi wani tunani taga ya turo Nabila, mamaki ne ya ƙara rufeta bayan sun haɗa ido, ta ɗan harɗe hannu tace “Aunty Nabs me kike yi a ɗakin Yaya a daren nan?” Gaban Nabila ne yake wani irin faɗuwa don ko Mummy bata shakkar ta ganta sama da Zeey don tasan bakinta ba shiru yake yi ba. Murmushin yaƙe tayi ta matso inda take da sauri cike da maganar raɗa tace “KB ina ji ya sha wani abu ne a waje ya shigo ciki ba a hayyacinshi ba shine ni kuma na tashi fitsari naji motsi na taimaka na kaishi ɗaki,” ta ƙarasa maganar tana ɗan kauda kai, mamaki ne ya kama Zeey tace “Are you serious? Shaye-shaye ya koma?” Bata jira Nabila ta bata amsa ba ta fara neman yin ɗakin Kabir cikin ɓacin rai, da sauri tasa hannu ta riƙo ta tace “Ina zaki? Bafa nufina shan wani abu na shaye-shaye ba wani abu ya sha shine cikinshi ke yi mishi ciwo.” Tsaki Zeey tayi tace “Karfa ki maidani wata mara wayau please, in naje na tambayeshi zan ji me ke faruwa.”
Hankalin Nabila ne ya tashi ganin da gaske Zee ɗakin zata je, kuma tasan tabbas Kabir yaji harda sharri take yi mishi to fa ita dashi tasan sun ƙara yin hannun riga, ƙafarta ta riƙe da sauri tace “Zeey ƙafata,” kasancewar dare ne yasa tayi maganar a hankali, da sauri Zeey ta dawo ta ɗagota tana cewa “Bigewa kika yi?” Ta ɗaga kai tana alamun shishitu don kar a jiyo su, tare suka koma ɗaki ta kwanta a kan gado tana cewa “Wasa fa nake miki ɗazu dama so nake naga yanda zaki yi ne, saƙo aka bani shine na bashi.” Wata nannauyiyar ajiyar zuciya Zeey ta sauke tace “Allah har hankalina ya tashi, kin san dai na tsani shaye-shaye bare mai yi in har Yayana ya fara hankalina tashi zai yi.” Murmushi tayi tace “Kema kin san ba zai fara ba balle Daddy ne zai barshi?” Wani kallo Zeey ta mata sai suka yi murmushi a tare, fitowa Zeey tayi ta koma ɗaki, idanu ta rufe a hankali tana hango fuskar Baqeer, wayarta ta ɗauka ta zubawa sunanshi ido, ya ɓata mata rai shi yasa ba zata je ta ganshi ba duk da sun shirya gwara ta nuna mishi ita ma tana fushi, amma me ASF take nufi? Abinda yazo mata kenan kawai ta shiga goggle ta dinga searching ana bata wasu ma’anoni da duk ta kasa ganewa, haka ta kwanta duk ranta a ɓace na son tasan me Baqeer yake nufi, juyi tayi sai kuma ta ɗauki waya taga karfe 1 na dare, saƙo ta tura mishi “Ya Baqeer menene *ASF*? Nifa ka sanyani a duhu Allah zan yi kuka.” Tana kaiwa nan ta kifa wayar bayan ta jonata a charge don tasan bacci yake yi.
******