Sashe 73
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau kwana biyu kenan Zee bata zo ba gashi ko waya taƙi yi mishi, sam komai yaji ya fita daga kanshi, haka kawai inya kalli turaren da rose flower ɗin daya siya sai yaji ranshi ya ɓaci, Dada tana lura da duk wani ɓacin ran da yake ji dashi kwanan biyu, don ko waje baya fitowa sai in abu yake so, zanen ma da yake na ɗinki ya ajiye tunda yana jiran a gama sayar da wancan kafin ya sake wani.
Yanzu shine karo na takwas daya ɗauki wayarshi yana ajiyewa, tsaki yayi ya cilla wayar kan gado, sallama yaji daga ciki hakan yasa ya ɗan gunguro kekenshi zuwa jikin ƙofar ɗakin shi. “Talatu kece?” Abinda ya jiyo Dada tana faɗa kenan hakan yasa ya maida kekenshi ciki takaici duk ya ƙara kamashi, exercise na kafarshi ya shiga yi sannan ya ɗauki wani littafi yana karantawa na fashion and design, “Me zai dameshi bayan mahaifinshi ma tunda ya koreshi ko waya bai taɓa yi ba yaji ya yake? Ai duk da bai san inda yake ba ya tabbatar daya tambayi Umma zata sanar mishi.”
Rufe idanuwanshi yayi yana tunanin meke damunshi akan Zainab? Me yasa yake ji kwana biyun nan kamar wata guda? Wayarshi ya janyo ya rubuta ‘Hope kina lafiya?’ Gogewa yayi ya sake rubuta ‘Zaki zo?’ Ido ya zaro yace zamana take yi ashe? Nan ya goge ya rubuta ‘Nace ba?’ Nan ma ya goge cike da takaici ya rufe wayar yana jin haushin kanshi.
A haka yayi sallar azahar, ko da Dada ta bashi abinci ma tsakura yayi ya ajiye yace ya ƙoshi, ita dai bata kulashi ba ta shirya ta fita gidan mai jego inda aka yi haihuwa kusa dasu.
Haka yayi sallar la’asar ya fito waje yana neman fita waje wurin wannan makahon haka kawai yake ji yana son bashi ko dubu biyar ne a cikin kuɗin shi, turus ya tsaya jin ƙamshin turarenta, baya yayi da keken ya koma tsakar gida yana ɗan gyaggyara zaman rigarshi, sallama tayi ya amsa ciki-ciki, da mamaki ta shiga tsakar gidan yi tayi kamar bata ganeshi ba tace “Dada fa?”
Mamakin kalamanta ne ya sakashi waigowa, kallonta yayi sanye take da doguwar rigar abaya sabon yayi, a saman abayar aka yi hula sai ta ɗaura ɗankwali tasa hular a sama, tayi kyau sosai sai yaga ma kyaunta kamar ƙaruwa yayi, kai ta ɗan karkatar tace “Tana ciki?”
“Ban sani ba.” Amsar daya bata kenan ba tare da yasan ya furta ba. Ga mamakinshi sai gani yayi zata juya ta fita da sauri yace “Ina zaki?”
Waigowa tayi tace “Gida.”
“Gida?” Ya tambaya fuskarshi a tamke tace “Eh, ko da wani abun ne?”
Kasa magana yayi sai kallonta da yake tace “Meye amfanin zuwa inda in aka ji kwana biyu kayi shiru ba za’a yi maka waya ko a tambayi lafiya ba ina ganin ba amfanin zuwa.”
Kallon juna suka yi, juyawa tayi zata wuce sai ga Dada ta shigo, dariya suka saki ta gaisheta tana cewa “Haba duk kwana biyu gidan babu daɗi ba kya nan shi kuma o’o sai ƙuncini da cin magani.”
Ta gefen ido ta kalleshi shi dai duk bai jin daɗi yaso yayi mata magana kuma sai ga Dada ta shigo, da alama ma bata ji daɗi bane, duk sai yake jinshi babu dadi.
Wayar Zee ce tayi ƙara kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗaga haka kawai taji zuciyarta na ingizata yin abu, tace “J haba ai ni nayi fushi.”
Kalmar J data furta ne ya sakashi kallonta, nan da nan takaici ya kamashi Junaid fa kenan, shine basu tashi yin wayarsu ba sai da tazo nan gidan?
Junaid yace “A’a fa nine zan yi fushi, sau nawa ina kira baki ɗauka ba.”
“Wai ka kira sam ban kula ba ban ɗan ji daɗi bane kayi hakuri.”
Kallon Baqeer tayi shima kallonta yake yi sai yaji ranshi duk babu daɗi, to wai shi menene nashi? Yasan bai kyauta ba amma wayar da take yi da Junaid haka ji yake yi kamar ya kwace wayar ya hanata magana.
“Allah a’a kaima kasan ba haka bane.” Shagwaɓar da yaji tana yiwa Junaid kenan, wani abu yaji ya sake tokareshi nan ya kauda kai.
“Okay to shikenan zan sanar mishi sai muzo kasan ni na ɗauka kaine zaka bamu appointment ai.”
Sallama suka yi ta kashe wayar sannan ta kalleshi tace “J yace ya kamata ka koma.”
“Na dauka Junaid sunanshi?”
“Eh amma J nake ce mishi.” Wani kallo ya maka mata ta kauda kai tana cin magani.
Bata jira me zai ce ba tace “Yaushe zamu je?”
“Zamu je da Salim.”
Wani kallo tayi mishi ranta ya ƙara ɓaci sai dai shi haka kawai baya son ya dinga sakata wahalar yawon nan sannan baya son ma ya dinga haduwa da Junaid.
Dada ce ta sake dawowa tace “Zo mu shiga ciki kin ji waje akwai ɗan sanyi.”
Zeey wucewa ciki tayi suka barshi a waje takaici duk ya isheshi, shigowa yayi ya kalli jakar turaren daya siyo mata sannan yasa hannu ya ɗauka, fitowa yayi yaga Dada tana waje da alama banɗaki ta shiga, Zeey na zaune tana daddanna waya, kusa da ita ya nufa ya miƙa mata gift bag ɗin, ɗagowa tayi ta kalleshi tace “Na menene?”
“Ki amsa.” Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa tana kallonshi, shagwaɓewa tayi tace “Allah fushi nake yi.”
Wani irin yanayi ya shiga ya ɗan dake yace “Zazzaɓi?”
Kai ta girgiza alamar a’a yace “Ciwon ciki?”
Nan ma kai ta girgiza yace “Me ya sameki?”
“Kawai.”
Maimaita kalmar yayi yana kallonta, ta turo baki kaɗan tace “Kawai babu abinda ke mini daɗi ne.”
Wani murmushi ne yazo mishi wanda shi kanshi bai san yayi ba, kallonshi tayi tace “Allah da gaske nake yi.”
Kai ya ɗaga alamar eh sannan yace “Sai kije saurayinki yayi miki allura.” Yana faɗar haka ya fara tura keken, kallonshi tayi sannan ta buɗe jakar, flower ɗin data gani da turare ne yasa ta miƙe da sauri tace “Ka san mai bada rose flower dai yake nufi ko?”
Kallonta yayi daidai ƙofar shiga ɗaki yace “Me yake nufi?”
Kafaɗa ta ɗaga tace “Ka bani baka san ma’anarshi ba?”
Kai ya kauda yace “Ni dai ban fassara ba.”
Zai rufe ƙofar ɗakin tayi saurin cewa “Thank you!”
Kallonta yayi yace “Nima.”
“Ban ji ba Allah me kace?”
Gyaran murya yayi tace “Yauwa me kake gani in muka nemi wasu masu ɗinkin suma kana musu zanen?”
Kallonta yayi yace “Hmm idea ce mai kyau, zan…..”
Da sauri ta katseshi tana cewa “Zan je na kai ɗinki kamar yadda muka yi wannan am sure zasu zo da kansu gwara suzo da kansu da ace mu muke nemansu.”
Murmushi ya saki yana jin daɗin yadda komai take faɗarshi duk da wani sa’in ya kula bata iya magana ba amma a ƙalla abinda ke ranta take faɗa. Itama murmushi tayi tace “Ya Baqeer yaushe zamu duba school ɗin ɗinkin?”
“Kada ki damu zan duba zan faɗa miki yadda ake ciki.”
“Hmmm sai kayi mini alƙawarin in ka jini shiru zaka dinga kirana Allah bana son a shareni sai naga kamar ba’a damu dani ba.”
A ranshi yace ke kuwa aka damu dake amma a fili murya kawai ya gyara.
Dada ce ta shigo hakan yasa ya rufe ƙofar ɗakin, wayarshi ya tadda tana ƙara ya ɗauka da sauri ganin Umma ce, tambayarshi tayi jiki nan yake sanar da ita makarantar da yake son shiga, tayi farinciki sosai sai dai tunda makaranta mai tsada ce sannan kafin ya gama ya buɗe shago tasan zai ji jiki nan suka ɗan yi hira sannan ta kashe.
*****
A fusace Badaru ya fara kiran sunan Kamalu kana ji kasan ranshi a ɓace yake, Abu ce ta fito da sauri har zaninta na neman kwancewa, tace “Malam me yayi?”
Yatsa ya nuna mata yace “Wallahi in ba so kike yi nasa a kulle ɗanki ba kice kada ya kuskura ya ƙara zuwa mini shago ya ɗauki abu, don asara da rashin hankali satar ma a shagona zai yi? To daga ke har shi zan iya sallamaku ke kin san ba damuwa ta bane.”
Jiki a sanyaye tace “Mallam anya kuwa shine zai ɗauka duk fa fitinarshi baya halin ɓera kasan wannan Bashir ke yi.”
Salati Jamila tasa tace “Bashir? Ahir ɗinki ko tsinke bai taɓa dauka ba tare da izinin mahaifinshi ba ehe.”
Badaru cike da takaici yace “Ni dai banyi sa’ar ƴaƴa ba kaf cikinsu kowa da ɓacin ran da yake ƙunzuga mini, to wallahi ni daidai nake da kowani ɗan iska kun ji na faɗa muku.”
Ɗakin Fatima ya shiga yana sababi, haushi ne ya ƙara rufeshi da yaga babu kujeru ya wuce ɗakinta ya kwanta akan gado.
Jamila ce ta kalli Abu tace “Kin dai yi asara wallahi a gidan uban wa Bashir ya taɓa sata? Amma Kamalu fa? Sai dai kar ki faɗa amma kowa yasan yana ɗauke ɗauke.”
Harararta Abu tayi ta shiga ciki tana masifa itama.
Ita dai Fatima tana kallonshi don yanzu tunanin yadda zata tunkare shi ya bada filin Baqeer take yi, gani take in aka sayar da filin tabbas zai ishi Baqeer biyan kuɗin makaranta ya kuma buɗe shago sai dai taya zata amshi takardun fili a wurinun Badaru? Sannan inya tambayeta wace ƙaryar zata yi?