Sashe 135
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
*****
Tunda ya tashi da safe yake jin faɗuwar gabanshi na ƙaruwa. Haka ya yini sukuku ko abinci kasa ci yayi haka Dada tayi ta fama dashi akan yaci abincin har ta gaji ta watsar dashi ta cigaba da ƴan sabgoginta. Ita bata san yadda yake ji ba shi yasa ta dameshi da batun wani abinci ko ance mata yana da ntsuwar da zai iya zama yaci abinci ne. Tun bayan azahar ya tashi ya shirya a cikin wata dakakkiyar shadda kalar light brown sai aka yi mata aiki da zare kalar coffee a irin waɗanda ya ɗinka ne, sosai yayi kyau ya fito cikakken namiji tsaf gashi dama tubarkallah Allah yayi mishi siffa irinta cikakken ɗa namiji gashi da wani irin kyau, sai abun ya haɗu da iya gayu da tsafta. Turarukanshi ya ɗauka ya feshe jikinshi dasu, wayarshi ya ɗauka ya fita parlourn Dada yana zaman jiran isowar Salim don ya matsu su bar gidan ko sun je suyi abinda ke gabansu yasan matsayin soyayyarshi da Zainab.
Bai daɗe da zama ba Salim ya iso shima cikin shiga irinta Baqeer. Dada na ganinshi tace "Hala gaisuwar surukai zaku shi yasa kuka yi gayu haka." Murmushi Salim yayi yace "Ashe bai faɗa miki ba, mahaifin Zainab zamu je mu gaisar," shi kuwa Baqeer cewa yayi "da bama kwalliya sai zamu wani wuri." Harararshi tayi tace "Idan nayi magana daga kai har Zainabu kuce ba haka ba ashe ni kuka ninke baibai, to Allah ya tabbatar mana da alkhairi wallahi naji daɗi."
"Ameen," Salim yace. Ƙara kallonsu Dada tayi tace "Ai gara ku hanzarta ku tafi kada suyi ta jiranku, idan kun je ku cewa Zainabu ina gaisheta akwai kuma tamu ni da ita zata zo ta sameni har gida naji dalilin wannan ƙunbiya-ƙunbiyar." Dariya Salim yayi yace "zan kuwa faɗa mata Dada, sai mun dawo."
Tunda suka fito babu wanda yayi magana, shi dai Salim ganin kamar Baqeer baya cikin nutsuwa yasa yayi shiru da bakinshi ya ƙyaleshi yaji da damuwar shi, shi kuwa Baqeer tunanin bai san abinda zasu je su riske ba ne yafi tsaye mishi a rai, yasan zai yi wahala su samu karɓuwa a wajen mahaifin Zainab. Anan cikin unguwar suka tsaya a masallaci suka yi sallar la'asar, haka Baqeer yayi ta gaisawa da mutane suna yi mishi jajen abinda ya faru. Bayan sun fito daga masallaci Salim na turashi suka ƙarasa gidan su Zeey. Ciro wayarshi yayi ya ƙirata, tana ɗauka yace mata "Gamu a ƙofar gida."
"Okay bari nazo na shigo daku," kawai tace ta ajiye wayar. Basu wani daɗe suna jiran ba sai gata ta fito cikin material ɗin daya ɗinka mata. Kallon-kallo suka hau yi zuciyoyinsu cike da bege da ƙaunar juna. Sosai Baqeer yaga ta ƙara yi mishi kyau gashi kayan sun karɓeta kamar yadda yayi hasashe. Salim ne ya katse kallon-kallon da suke yiwa juna yace "Hajiya Zeey barka da yamma." A kunyace tace "barkanmu dai, ku shigo." Tayi gaba suka bita a baya. A parlourn karɓar baƙin Alhaji Suleiman ta sauke su, sai da ta zauna suka ƙara gaisawa da Salim sannan ta kalli Baqeer ta sakar mishi wani ƙayataccen murmushi tace "Ya Baqeer ina yini," cikin wani salon magana da ita kanta bata san ta iya ba kawai dai ta tsinci kanta dayi.
Lumshe ido yayi ya mayar mata da murmushin kwatankwacin irin wanda tayi mishi yace "I'm fine and you?"
Karkata kai tayi tana dariya tace "Lafiya lau, sai dai fa ban yi tunanin da gaske zaka zo ba."
"Me yasa?" Ya tambayeta yana tsatsareta da ido. Ɗan kawar da kanta tayi daga kallonshi da yake neman kassara mata jiki tace "Saboda jiya ka nuna min ba zaka iya pursuing ɗina ba." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ina sonki Zainab har ban san yadda zan kwatanta miki ba amma ina tantama idan mahaifinki zai amince ya bani aurenki, kin dai san komai ba sai na faɗa miki dalili ba."
"Kasancewarka tare dani ne abu mafi muhimmanci da nafi buƙata, ni kai kaɗai nake so kai kaɗai kuma zan iya aure don haka kada kasa damuwar komai a ranka In Sha Allah bazan bari kowa ya rabamu ba." Sun daɗe suna musayar kalamai kafin ta tashi ta shiga cikin gida akan zata faɗawa Daddy zuwansu. Kitchen ta fara shiga ta bada umarnin akai kayan motsa baki guest sitting room ɗin Daddy sannan ta shiga ɗakin Mummy tace mata ta faɗawa Daddy ga baƙin sun zo.
Ɗakinta ta shiga tana addu'ar Allah yasa kada Daddy ya basu matsala don ita dai baza ta yarda a rabata da Baqeer ba domin kuwa shine farin cikinta dashi kaɗai zata iya rayuwa.
Tunda Mummy ta shiga ta faɗa mishi baƙin sun iso yake baƙin rai, ya daɗe bai tashi ya shirya ba don sai da ya ɓata fiye da mintuna talatin kafin ya tashi ya canja kaya ya fita. Fuska a murtke ya shiga sitting room ɗin, Salim dake zaune akan kujera yayi saurin zamowa ƙasa ya zauna yana gaishe shi. Wani irin kallo Daddy yake yi mishi don ya ɗauka shine manemin auren Zainab ɗin. Shima Baqeer ya shiga gaisheshi cikin girmamawa. Kallo ɗaya yayi mishi ya mayar da kanshi wajen Salim yace "Kai ne mai san ƴata?" Girgiza kai Salim yayi yace "A'a bani bane abokina ne Baqeer," yace yana nuna Baqeer dake zaune akan wheelchair ɗin shi.
Daddy bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba yace "What? Gurgun? Gurgun ne ke neman auren ƴata?" Yace yana nuna Baqeer da ya sandare a zaune da ɗan yatsa. Da gudu Mummy ta ƙaraso cikin parlourn don taga me yasa Daddy ihu irin haka.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*UmmAsghar Ce*
*Da*
*Ayushe Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA UKU*
{83}