← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 168

Sashe 138

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*****
Shi kuwa Badaru ganin an rufe mishi ƙofa ya juya ya kama hanyar gidanshi yana jin takaicin kai kanshi gidan Suleiman Ƙaraye da yayi, shi da yasan wata maganar Baqeer yaje ɗauko mishi me zai sa yaje wannan gidan ya jiyowa kanshi kayan takaici da baƙin ciki. Ace wai duk faɗin garin Kano Baqeer ya rasa ƴar da zai ce yana so sai ta Suleiman Ƙaraye. Tun daga soro yake ƙwala kiran Fatima har ya shiga ɗakinta, tana kwance tana jan carbi bacci ya kwasheta bata sani ba. Kamar a mafarki taji yana ƙwala mata kira, tana buɗe ido sai ta ganshi tsaye a kanta sai huci yake yi. Tashi tayi zaune tana gyara ɗaurin ɗankwalinta daya zame tana bacci. "Mallam sannu da zuwa," tace mishi duk kuwa da taga alamun zuwan nashi bana lafiya bane. Yana daga tsayen yace "Ki faɗawa nakasashen ɗanki ya kiyaye ni wallahi ya fita idona in rufe in ba haka ba sai na wulaƙanta rayuwarshi, in banda rashin mutunci ya rasa ƴar mutumin da zai so sai ta Suleiman Ƙaraye salon ya janyo mini ƙasƙanci da wulaƙanci a wajen shi."
Mamaki ne ya kamata tace "Shi Baqeer ɗin ne yake son Zainab?" Tsaki yaja yace "Na dai faɗa miki ki gaya mishi babu shi babu ƴar wannan mara mutuncin mutumin. Haba ƴaƴa sun zama kamar ƴaƴan Allah bani bau guda ɗaya na kirki a ciki kowanne da irin baƙin cikin da yake cusa maka."
Bayan fitar shi Umma na zaune tana jin mamakin wai Baqeer ne yake son Zainab, to a ina ma suka haɗu da har ya ganta yaji yana sonta? Ta yiwa kanta wannan tambayar sai kuma ta tuna ashe fa Dada tace mata Zainab ɗin tana zuwa a lokacin abun ya ɗaure mata kai sai dai bata zurfafa tunani ba ashe su soyayya suke yi ba'a sani ba. Shi kuwa Baqeer me ya kai shi bayan yasan akwai daɗaɗɗiyar rashin jituwa a tsakanin iyayensu, ture batun Badaru ma tunda ya kori Baqeer daga gidanshi amma Suleiman Ƙaraye fa ita tasan babu ta yadda za'a yi ya bashi auren ƴarshi alhalin yqna ɗan Badaru.
Nisawa tayi ta ɗaga hannayenta sama a fili tace "Allah gamu gareka, idan har akwai alkhairi a taraiyarsu Allah ka tabbatar ka kawar da fitina." Wayarta ta janyo ta kira Baqeer sai dai ta kasa samunshi, haka tayi ta gwadawa bata sameshi ba har ta haƙura ta ajiye wayar akan ta ƙara gwadawa zuwa anjima.

*****
Tunda suka bar ƙofar gidansu Zeey hankalinshi yake a tashe, daga shi har Salim an rasa me yiwa wani magana saboda kowa damuwa ce danƙare a cikin zuciyarshi. Shi Baqeer ma abubuwan ne suka taru suka yi mishi yawa ya rasa tunani ƙwaya ɗaya da zai kama. Tun lokacin da yayi accident bai ƙara tunanin wanda ya bugeshi ba don a ganinshi babu amfanin da sanin mutumin daya kaɗeshi zai yi mishi sai yanzu yake tuna yadda accident ɗin ya faru. Tabbas Kabir ne ya kaɗeshi ya janye motarshi ya tafi ya barshi a kwance a wurin, duk da bai ga fuskarshi ba amma ya gane motar tabbas ita ce motar da yake hawa yana baɗesu da ƙura idan yazo wucewa. A daidaita Salim ya tarar musu suka shiga ba tare da sun faɗa mishi inda zasu ba, sai da suka fara tafiya sannan Salim ya faɗa mishi mariri zai kai su ai kuwa ya yanka musu kuɗin da zasu biyashi, amsawa kawai Salim yayi don baya cikin yanayin da zai tsaya yin jayayya dashi.
Lokaci zuwa lokaci Baqeer yake sauke wata ajiyar zuciya, ga wata irin rawa da yaji jikinshi ya ɗauka ga alama dai zazzaɓi ne yake neman kamashi. Tashin hankalin daya tsinci a ciki ba zai faɗu ba, a yadda Zainab ta shiga ranshi bai hango ta yadda zai iya rabuwa da ita ya zauna lafiya ba. Wannan wacce irin rayuwa ce? Ace akan abinda bai taka kara ya karya ba, saboda wani saɓani daya shiga tsakanin iyayensu a shekarun baya za'a hanasu samun farin cikin su.
Kallon ƙafafuwan shi yayi sai kuma yayi wani murmushi mai ciwo cikin ranshi yace 'What do you expect? Kana tunanin kowa ne zai ganka akan wheelchair ya amince ya baka auren ƴarshi.' Shi yasan ko babu matsalar kasancewar Badaru mahaifi a gareshi to wannan nakasar kaɗai ta isa tasa a hanashi aure to bare kuma ga babban ƙalubalen Mallam Badaru daya kasance uba a wajenshi abokin adawar mahaifin Zainab kuma.
Har suka isa gida Salim ya taimaka mishi ya fita daga cikin adaidaitan ya zauna akan wheelchair ɗin shi, hannu yasa ya gara tayoyin ya shige cikin gida bai tsaya jiran Salim dake sallamar mai adaidata ba. Yana shiga ya wuce Dada dake zaune a tsakar gida tana gyaran zogale zata yi musu kwaɗo in anjima. Kan katifarshi kawai ya faɗa ya kwanta a rigingine yana kallon rufin ɗakin, wasu ƙwalla ne suka taru a idanunshi sai dai ya hanasu zubowa.
Cikin ranshi yana jin ciwo da nakasar shi ta kasance abu na farko da zai sa a hanashi aure kamar mutane sun manta ai da ba haka yake ba ƙaddara ce ta afko mishi kuma babu wanda ya wuce ta faɗa a kanshi shima. Salim ne ya shigo ya zauna a gefen katifar yana kallon Baqeer da lokaci guda duk ya zabge ya rame kamar wanda ya kwanta jinya. Tausayin shi ne yaji ya kamashi, a cikin lokaci ƙanƙani matsaltsalun rayuwa sun saka shi a gaba daga wannan sai wannan kamar baza su wuce ba sai dai yasan komai mai wucewa ne kamar yadda wancan ya wuce haka nan wannan ɗin ma zai wuce sai dai shi kanshi bai ji daɗin yadda mahaifin Zainab yayi musu ba kamar ya manta Allah ne mai tsarawa kuma shi ya ƙaddari baqeer ɗin da kasancewa haka da zai zaunar dasu yana faɗa musu maganganu na ɓatanci son ranshi. Kallon Baqeer ɗin yayi yace "Kayi haƙuri Baqeer nasan abinda mahaifin Zainab yayi mana da ciwo amma haƙuri zaka yi please kada kasa abun a ranka yayi ta damunka, a yadda nasan Zainab na sanka nasan ba zata taɓa yarda a rabaku ba."
Bai cewa Salim komai ba don shi kaɗai yasan abinda yake ji a cikin eanshi, wani irin ƙuna yake ji da bai san ta yadda zai iya fasaltaw ba. Yasan ba Zainab ba kowacce mace yace zai nema wannan nakasar ita zata zame mishi cikas don ya san babu uban da zai ɗauki ƴarshi ya bawa gurgu. Idan yayi wannan tunanin ne hankalin shi yake ƙara tashi, shi kenan shi nakasashe ba mutum bane da za'a dinga gudun shi irin haka kamar wani annoba.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*UmmAsghar Ce*
*Da*
*Ayushe Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BIYAR*

{85}
Chapter 138 · 0% Book details