← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 168

Sashe 39

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Yau Zainab ta gama sawa ranta dole taje taga Baqeer ta kuma sa a ranta wannan shine zuwa na karshe da zata yii, shima zuwan zata yi ne don kawai taga ya jikin nashi yake bayan jiya ya dawo daga ganin likita. Da wannan tunanin ta yiwa Mummy k6arya akan zata je amso saƙo a wurin wata ƙawarta. Kamar zata hanata sai kuma ta barta don bata son damuwar nan da take gani a fuskarta.
Ɗaki ta koma ta janyo riga da wando zata saka sai kuma ta maidasu runa wurin wanda zata je, kallon atamfa tayi tana tuno wasu kalamanshi na can baya shekaru masu ɗan yawa, daga ya ganta da kayan turawa zai ce ko kyau babu, tsaki tayi a fili tace “Damuwar ka ai dama ba don kai zan saka ba.” Mai makon tasa kayan turawan sai kuma tasa atamfa, doguwar riga ce tayi mata kyau sosai, kasancewar ba sawa take yi ba sai ta fito daban kamar ba ita ba. Bata ɗaura ɗan kwali ba don bata ma iya ba kawai mayafi tasa a sama ta fito, da mamaki Mummy ke kallonta sai dai ganin wajen ƙawarta tace zata yasa tayi shiru, Nabeela bata nan don tun safe taje gidansu inda mahaifiyar su take.
Sai data hau kan titi sannan ta fara tunanin wanda zata kira ta tambayi address ɗin don dama ita ba wurinshi zata je ba kawai dai jikinshi zata je gani daga nan kuma tasan ba zata ƙara ganinshi ba.
Har zata kira Maryam ta tambayeta kwatancen gidan sai ta fasa ta kira Salim, bayan sun gaisa ne tace “Salim dama naga wani kwalin magani ne a mota nake son na baka to kuma na fita nima nace ko kawai zaka faɗa mini gidan Dada sai na ajiye mata na wuce?”
Mamaki ne ya kamashi don ya tabbatar ya fita da duk magungunan sai dai zai iya yiwuwa bai kula da lokacin da wani ya faɗi ba.
Nan yayi mata kwatance ta kashe sannan ta shafi fuskarta, me yasa ta koyi ƙarya saboda Baqeer ne? Iska ta furzar sannan ta cigaba da tuƙi, bata sha wahala sosai ba don tana shiga layin ta tambaya aka nuna mata.
Tafi minti biyar a waje tana kokwanton shiga kafin ta daure ta fito, har ta kai ƙofa ta girgiza kai lallai ajinta zubewa yake nema yayi, ta ya ma zata shiga gidan tace me ya kawota? Neman juyawa tayi sai taɗan ji sautin maganar Dada da ɗan ƙarfi tana kiran Baqeer, da alama ƙofa take bugawa, sam ta manta ta fasa shiga gidan sai kawai ta tura ta shiga hankali a tashe, Dada ce ta kalleta da mamaki don bata ganeta ba.
Zee sai a lokacin tasan ta kwafsa, to meya kawota ma ne? Murmushin yaƙe tayi ta gaisheta, nan ta amsa tare da cewa “Wacece?” Yawun bakinta ta hadiya tace “ƙawar Maryam ce magani suka manta a mota nazo kawo mishi.”
Nan da nan ta saki fuska tace “Ayya Masha Allah! Mun gode kuwa.”
Zeey ta ciro paracetamol a jaka ta miƙa mata, Dada ta amsa sannan tace “Na rasa yadda zan yi da yaron nan tunda ya shiga ɗaki tun jiya har yanzu bai ko leƙo ba, ga baici abinci ba balle ya samu yasha maganinshi.”
Dada ce ta sake buga ƙofa tace “Baqeer wai din Allah wace rayuwa ce wannan?”
Zeey ce ta kalleta tace “Dada bari na wuce.”
Tayi saurin riƙeta tace “Ai kam dai ba kyazo ki tafi ba ko ruwa ban baki ba, zo ki zauna mu gaisa kici abinci.”
Baqeer da ƙamshin turaren da yaji jiya a motar nan ne ya shigo ɗakinshi yasa ya tura keken shi da hannunshi zuwa bakin ƙofa, jingina bayan keken yayi da ƙofar don son sanin wacece? Muryarta kaɗai da yaji ya gane ta. Akan me take bibiyar rayuwarshi ne wai? Shiru yayi yana tunanin turaren nan da yaji jiya ba dai jiya har motar abokin Salim ta shiga ba?
“Dada Allah babu komai, amma ya zaki yi in bai buɗe ƙofar ba?”
Kalamanta ne suka doki kunnuwanshi, “Ni kaina ban sani ba wallahi sam na kasa gane me ke damunshi, ƙaddarar nan Allah ya riga ya aiko mana ita dole ne mu amsheta.”
Tunowa tayi da yadda taga mahaifinshi na magana jiya ta tabbatar waɗannan abubuwan sune suke damunshi, murmushin da ya tsaya iya leɓe tayi kafin tace “Sai mutum ya halaka kanshi saboda ƙaddarar da Allah ya ɗaura mishi? Dada ashe mu baza mu godewa Allah ba mu san iskar kaɗai da muke shaƙa a duniya kyauta bace daga Allah zuwa garemu?”
Kallon ƙofar yayi saboda kalamanta da yaji, Dada ce tace “Abin ne duk na rasa kanshi wallahi ni kaina jiya ban yi bacci ba.”
Tayi maganar cike da jimami, fitowa tayi Zeey ta kalli ƙofar, alamun motsi taji daf da ƙofar wanda Baqeer ke neman barin bakin ƙofar.
“Haka zaka cigaba da rayuwa?”
Abinda ta faɗa kenan wanda ya sakashi tsayawa da tura keken, “Baka duba mutanen da ke tare da kai waɗanda suka damu da kai? Sai wasu ƙalilan da basu damu da kai ba?”
Yawun bakinshi ya haɗiya tare da kallon ƙofar, “In har kana son ƴan uwanka to ka cire rashin ƙafar ka a matsayin nakasa ka maidata challenges na rayuwa da Allah ya ƙaddara maka, baka san me Allah ya shiryawa rayuwarka ba da ya jarabceka da hakan. Please ka sha magani ka kuma ci abinci.”
Tana kaiwa nan ta fito waje, Baqeer ji yayi wani abu ya tokare mishi zuciya, wacece wannan? Wani abu yake ji wanda shi kanshi bai san menene ba.
Zeey a waje taga Dada da alama so take yi ta kawo mata abu, kallon yadda take juye abincin daga robobin biyu tana ƙoƙarin maidasu ɗaya take, shinkafa da wake ne, da alama ma babu yaji don gwangwanin take ta ɗan bugawa a ƙasa tana tashin wanda ya danƙare daga ƙasa, idanun Zeey ne ya nemi cicikowa, da sauri ta maidasu tace “Dada ni nama tuna ana nemana bari  nayi sauri naje zan samu lokaci nazo naci abincinki.”
Tana kaiwa nan ta fito da sauri ta faɗa motarta, janta tayi ta bar wurin tausayin Dada sai damunta yake yi, bata yi auni ba sai gata a gaban babban shagon unguwar, ajiyar zuciya tayi ta duba account dinta wanda take da kudi sama da naira duba ɗari takwas, amma gashi can abincin dubu ɗaya yana neman gagararsu. Ya zata yi ta taimaka ba tare da an san ita bace? Salim ne ya faɗo mata ai zata iya siya ta bashi ya kai a matsayin aikenshi aka yi ko? Haka ta cigaba da tafiya tana nazarin abinda ya kamata.

*****
Kamalu yana fitowa daga ɗakin Abu kawai ya daka tsalle tare da dukan bokitin robar dake tsakar gidan da kafarshi, ji yake wai yau shine zai tuka motar Baba da Baqeer, kallon kayanshi yayi babu laifi gwanjo ne amma masu kyau, comb yasa ya taje kanshi sannan ya fesa turare ya shiga mota ya ƙure kiɗa cikin ƙwambo ya fara tuki, unguwar su Zeey ya nufa, yana shiga layin yaje gidan mai gadi ya ce bata nan yana yi mishi kallon mara hankali, cike da takaici ya juyo yana tunanin ba dai wurin Salim taje ba? Kwafa yayi don wallahi yana tausayawa Salim duk ranar daya damƙeshi, kamar a mafarki ya hango motarta, ai cikin hanzari ya jaa motar yasha gabanta, wanda saura kaɗan ta buge shi, burki ta taka da sauri tana maida ajiyar zuciya, Allah ya taimaketa kan layi ne ba titi ba, da mamaki ta ɗago ta kalli motar, Kamalu ne ya sakar mata wani murmushi tare da ɗaga mata gira, bata ganeshi ba hakan yasa ta tsaya tana kallonshi har ya fito daga motar da yake yazo inda take, glass din da take ciki ya ɗan buga yana mata alama data fito tare da kashe mata ido.
Mamaki ya sake rufeta ta sauke glasses ɗin motar tace “Yaro ya haka?”
“Yaro?” Ya maimaita kalmar tare da nuna kanshi, tace “Eh, saboda halin yarinta kake yi, menene hakan?”
Yawun bakinshi ya hadiya yace “Roshni plz magana nake so muyi ina ta zuwa gidanku ba’a barina na ganki.”
Kallon mamaki kawai take yi mishi tace “Roshni?”
Dariya yayi yana haɗe leɓenshi yace “oh Zainab mantawa nayi.”
Takaici ne ya isheta kawai ta zuge glass tana neman yin reverse da sauri ya tsaya bayan motar tare da tare hanyar da zata yi reverse ɗin, mamakinta ne ya sake ƙaruwa hakan yasa ta fito don sam bata da hakuri yanzun ma damuwar Baqeer ne yasa take kokarin haƙuri da shirmen yaron.
Murmushi yayi ganin ta fito ya dawo yana tafiyar nigga ya tsaya kusa da ita yace “Roshni nine fa Sadaath ɗinki kin manta love at first sight.” Ya kanne mata ido yana shafa kuncinshi.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#Zeey
#Kamalu
#Sanyin Zuciya
#Rayuwat

*Na Umm Asghar*
   *Da*
*Ayusher Muhd*🏌🏻‍♀️

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA HUƊU*

{24}
Chapter 39 · 0% Book details